Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta amince ta fitar da tsantsagwaron kuɗi fam milian 125 daga lalitarta domin sayen ɗan wasa Alexander Isak daga Newcastle.
Majiyoyi da ke da masaniya kan cinikin sun shaida wa BBC cewa yanzu an kammala yarjejeniyar komawar ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Sweeden zuwa Anfield.
Majiyoyi daga ɓangaren Newcastle sun ce kuɗin zai iya kaiwa fam miliyan 130, tare da wasu ƴan canji a sama.
Ana sa ran yi wa Isak gwaje-gwajen lafiya a yau Litinin gabanin sanya hannu da zai yi kan kwantaragin taka leda a Liverpool ta tsawon shekara shidda.
A watan Agustan da ya gabata Liverpool ta miƙa wa Newcastle tayin sayen Isak kan kuɗi fam miliyan 110, sai dai an yi watsi da tayin nata, amma a yanzu da alama ta shirya ɗaukar ɗan wasan da ta nace mawa.
Da alama doguwar tirka-tirka da aka kwashe tsawon lokaci ana yi kan sayen matashin mai shekara 25 a duniya za ta zo ƙarshe ne a ranar ƙarshe ta kasuwar musayar ƴan wasa ta wannan bazara.
Hakan na zuwa ne bayan Newcastle ta samu nasarar sayen ɗan wasa Nick Woltermade daga ƙungiyar Stuttgart a makon da ya gabata.
Tuni Liverpool ta karya tarihin da take da shi na kashe kuɗi wajen sayen yan wasa bayan ta sayi Bajamushen ɗan wasan tsakiya Florian Wirtz kan kuɗi kimanin fam miliyan 100 tare da ƙarin fam miliyan 16 a sama.
Bayan sayen ƴan wasa Hugo Eketike, Milos Kerkez, Jeremie Frimpong, Giorgi Mamardashvili, Armin Pecsi da kuma Giovanni Leoni, sayen ɗan wasa Isak zai sanya kuɗin da Liverpool ta kashe a wannan bazara ya kai fam miliyan 416 da ɗoriya.