Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/07/2024.

Taƙaitattu

  • An sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta
  • IMF ta rage hasashen bunƙasar tattalin arzikin Najeriya
  • Turkiyya da Nijar suna tattaunawar ƙulla ƙawancen soji da tattalin arziki
  • Gwamnan Kano ya naɗa sabbin sarakuna uku masu daraja ta biyu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Usman Minjibir

  1. Matashin da ya harbi Trump shi kaɗai yake aiki - FBI

    Donald Trump

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar tsaro ta FBI a Amurka ta ce ɗanbindigar da ya so kashe tsohon shugaban ƙasar Trump ya yi gaban kansa ne wajen kai harin, ba wai yana aiki ne da wasu ba.

    Ta ce ya sayi irin zungureriyar bindigar nan ce mai sarrafa kanta da ake kira AR 15 domin aiwatar da shirin nasa.

    FBI ta ƙara da cewa an sayi bindigar ne bisa doka kuma an gan shi rataye da ita lokacin da aka harbo shi daga saman rufin benen da ya yi harbin.

    Matashi ne mai shekara 20 da ake kira Thomas Matthew Crooks.

    Hukumar ta kuma ce an gano wasu bama-bamai a cikin motar wanda ake zargin, kodayake har yanzu ba a fayyace dalilinsa ba, ko wata akida, ko ma taɓin hankali da suka ingiza shi aiwatar da shirin nasa ba.

  2. Bam ya kashe mutum biyar a Somalia suna kallon wasan Ingila da Sifaniya

    Mogadishu

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata fashewa da auku a wurin shan shayi da ke tsakiyar birnin Mogadishu ta kashe aƙalla mutum biyar yayin da suke tsaka da kallon wasan ƙarshe na gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasashen Turai.

    Haka nan, bam ɗin da aka ɗana a jikin mota ya jikkata aƙalla mutum 20, in ji rundunar 'yansandan Somalia, yayin kallon wasan da Sifaniya da doke Ingila 2-1 kuma ta ɗauki kofin gasar ta Euro 2024 ranar Lahadi da dare.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, rundunar ta ce motar da aka ajiye a kusa da shagon mai suna Top cafe ce ta tarwatse.

    Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:28 na dare, a cewar 'yansandan.

    Ɗaya daga cikin mutanen da suka tsira daga harin ya faɗa wa wata kafar yaɗa labaran yankin cewa yana cikin shagon da ake kallon wasan lokacin da bam ɗin ya tashi.

  3. 'Yan Rwanda na kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa

    Zaɓen Rwanda

    Asalin hoton, Reuters

    A yau ne al'ummar ƙasar Rwanda ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa da 'yan majalisar dokokin kasar, inda ake kyautata zaton Shugaba Paul Kagame zai sake samun nasara a karo na huɗu.

    Ya mamaye kowane sakamakon zabe tun lokacin da ya zama shugaban kasa a shekarar 2000, inda yake samun sama da kashi 90 na ƙuri'un da ake kaɗawa.

    Wakiliyar BBC ta ce a zaben baya na 2017 ya samu kashi 99 cikin 100 na ƙuri'un da aka kada, wanda kashi 96 cikin 100 na wadanda suka yi rijista sun yi zabe, abin da ya sa manazarta ke ganin akwai lauje cikin naɗi.

    ‘Yan takara biyu ne kawai aka tabbatar da cewa za su fafata da shi; Frank Habineza na jam’iyyar Democratic Green Party, da Payimana Philippe ɗan takara mai zaman kansa.

    Dukkansu sun tsaya takara a zaɓen 2017.

  4. Barka

    Maraba da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na Litinin.

    Umar Mikail da Usman Minjibir ne za su kasance da ku a wannan hantsi.

    Ku biyo mu.