Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/07/2024.
Taƙaitattu
An sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta
IMF ta rage hasashen bunƙasar tattalin arzikin Najeriya
Turkiyya da Nijar suna tattaunawar ƙulla ƙawancen soji da tattalin arziki
Gwamnan Kano ya naɗa sabbin sarakuna uku masu daraja ta biyu
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail da Usman Minjibir
Tarayyar Turai ta ƙaƙaba wa wasu Yahudawa takunkumi
Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya wasu sabbin takunkumai a kan Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi 'yan kama wuri zauna da ke zaune a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Takunkuman za su shafi wasu Isra'ilawa biyar ne da kuma wasu kungiyoyi uku, waɗandaa Tarayyar Turai ta ce sun ƙuntata wa Falasɗinawa ta hanyar take haƙƙinsu.
Ƙungiyoyin da abin ya shafa sun hada da wata ƙungiya da ake kira Tzav-9, da ake zargi da hana manyan motocin agaji shigar da kayan zuwa Gaza.
Ɗaya daga cikin mutanen da takunkumin ya shafa kuma shi ne Ben-Zion Gopstein, wanda ya samar da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Lehava.
Ivory Coast ta karbi allurar rigakafin zazzabin maleriya
An kai kashin farko na allurar rigakafin cutar maleriya da Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da ita zuwa Ivory Coast.
Allurar rigakafin wadda wata tawaga a jami'ar Oxford ta samar da ita, ta zamo ta farko da ta samu karbuwa da kashi 75 cikin 100.
Masana kimiyyar da suka samar da rigakafin sun ce allurar za ta iya ceton rayukan mutane dubu 300 a shekara.
Wannan sabuwar allurar rigakafin ita ce ta biyu da aka samar domin magance cutar maleriya wadda ke janyo mutuwar mutane kusan dubu dari biyar a shekara yawancinsu kananan yara.
Republican ta tabbatar Trump a matsayin ɗantakarar shugaban ƙasa
Jam'iyyar Republican mai hamayya a Amurka ta tabbatar da Donald Trump a matsayin ɗantakararta na shugaban ƙasa a zaben watan Nuwamba.
Trump ya samu rinjayen goyon baya na wakilan jam'iyyar a babban taron jam'iyyar.
Trump wanda ya tsallake rijiya da baya bayan yunkurin halaka shi a wani gangamin yaƙin neman zaɓe, zai sake fafatawa ne da shugaba Joe Biden.
Trump ya zaɓi JD Vance a matsayin mataimakinsa
Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump ya sanar da sanata JD Vance a matsayin wanda zai yi masa mataimakin shugaban kasa a zaben Amurka.
Trump ya sanar da mataimakinsa ne a kafarsa ta sada zumunta a ranar Litinin.
"Bayan tattaunawa mai tsawo da dogon nazari kan wanda ya fi dacewa daga cikin mutane da dama, na yanke shawara, wanda ya fi dacewa da zama mataimakin shugaban kasar Amurka shi ne Sanata JD Vance daga jihar Ohio, kamar yadda Trump ya wallafa a kafarsa ta Truth.
Mr Vance ya taɓa caccakar Trump kuma yanzu ya zama wanda zai yi masa mataimaki a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba a Amurka
Dubban ma'aikatan Indiya sun samu ƴanci daga bautarwa a Italiya
Asalin hoton, Getty Images
'Yan sandan Italiya sun ce sun ƴantar da wasu ma'aikatan gona 'yan Indiya 33 daga yanayin aiki irin na bayi a lardin Verona da ke arewacin ƙasar.
An tsare wasu mutane biyu 'yan asalin Indiya bisa zargin shigar da wadannan ma'aikata zuwa Italiya tare da alkawuran ayyukan yi da ingantacciyar rayuwa, kawai don cin gajiyar su daga baya.
Hukumomi sun ƙwace kusan dala 545,300 daga hannun wadanda ake zargin.
Wannan lamari ya ja hankalin jama’a a yayin da ake ci gaba da bincike kan halin da ‘yan ci-rani ke ciki a Italiya, biyo bayan mummunar mutuwar wani ɗan kasar Indiya a watan da ya gabata.
Ma’aikacin ya rasa hannu a wani hatsarin da ya rutsa da shi a wurin aiki, kuma rahotanni sun ce bai samu wani taimako ba, inda a ƙarshe ya mutu sakamakon raunin da ya samu.
Wanda ya ɗau mutumin aiki a halin da ake ciki yana fuskantar tuhume-tuhume na sakaci da kuma kisa.
Ƴan sandan Italiya sun ce suna gudanar da bincike kan mutanen biyu da ake zargi da aikata laifuka.
Majalisar dokokin Gambia ta jaddada haramcin kaciyar mata
Majalisar dokokin Gambia ta yi watsi da wani yunkurin na soke haramcin kaciyar mata.
Mai magana da yawun majalisar Fabakary Tombong Jatta, ya ce yawancin mambobin majalisar sun yi watsi da kudirin.
Kimanin shekaru takwas ke nan da aka soke haramcin kaciyar a kasar tare da sanya hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru uku ga duk wanda aka kama laifin.
An dai haramta kaciyar mata a kasashe fiye da 70, abin da har yanzu ake yin ta a wasu kasashen Afirka ciki har da kasar Gambia inda aka yi wa mata fiye da kashi 1 bisa uku 'yan tsakanin shekaru 15 da 49 kaciyar..
Masu fafutika sun ce tsawon shekara tara ba a aiwatar da dokar, inda mutane biyu kawai aka hukunta tun lokacin.
Gwamnatin Tarayya ta raba wa gwamnoni tirelolin shinkafa domin talakawa
Asalin hoton, Other
Gwamnatin Najeriya ta ce ta ba kowace jiha haɗi da Abuja tirelar shinkafa 20 domin raba wa talakawa.
Ministan watsa labaran ƙasar Mohamed Idris ne ya tabbatar da haka bayan kammala taron majalisar zartarwa a ranar Litinin.
Ya ce kowace tirela tana ɗauke da buhun shinkafa 1,200 kg25 da aka ba gwamnonin jihohi a wani mataki na rage wa talakawa raɗaɗin ƙarancin abinci da tsadarsa da ake fuskanta a ƙasar.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana fatan gwamnonin jihohin za su raba kayan abincin ga mabuƙata a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Ana dai fama da tsadar kayan abinci da ake alaƙantawa da matsalolin tattalin arziki wanda janye tallafin mai da matsalar tsaro suka haddasa.
Kotu ta hana Aminu Ado Bayero bayyana kansa a matsayin sarki
Wata Babbar Kotu a Kano ta umarci Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya daina bayyana kansa a matsayin sarki.
Umurnin kotun ya kuma shafi sauran sarakuna guda hudu da gwamnatin Kano ta tube wato na Rano da Gaya da Bichi da Karaye.
Gwamnatin Kano da majalisar jihar ne suka shigar da karar, kuma a lokacin da take zartar da hukunci, Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta tabbatar da ikon majalisar jihar kan sauke sarakunan da kuma ikon gwamna na tabbatar da dokar.
Asalin hoton, AMINU ADO BAYERO/INSTAGRAM
Najeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun cimma yarjejeniyar ci gaba da zirga-zirga
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce ta cimma yarjejeniya da hukumomin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin ci gaba da zirga-zirga tsakanin ƙasashen biyu.
Hakan na nufin cewa ƴan Najeriya za su iya ci gaba da zirga-zirga zuwa birnin Dubai na ƙasar ta UAE.
A cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya fitar, ya ce "bayan nasarar da aka samu wajen tattaunawa an cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wadda za ta bai wa masu riƙe da takardar tafiya ta fasfon Najeriya samun izinin yin tafiya zuwa Haɗaɗɗiyar Daular ta Larabawa".
Sanarwar ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga yau 15 ga watan Yulin 2024.
Wannan na zuwa ne sama da shekara biyu bayan da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ta dakatar da bayar da takardar biza ga ƴan Najeriya sanadiyyar ruɗani na diflomasiyya.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabwa na daga cikin ƙasashen da al'ummar Najeriya ke yawan ziyarta, ko dai domin kasuwanci ko kuma shaƙatawa.
An samu raguwar kashe-kashe da garkuwa da mutane a Najeriya - Rahoto
Asalin hoton, Defense Headquaters
Najeriya ta samu raguwa a yawan mutanen da ake kashewa, da waɗanda ake garkuwa da su, da kuma ayyukan rashin tsaro a cikin watan Yuni, idan aka kwatanta da watan Mayu na shekarar da muke ciki ta 2024.
Hakan na ƙunshe ne cikin rahoton wata-wata na al'amuran tsaro da kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan harkokin tsaro ya fitar a yau Litinin.
Rahoton ya ce: "A watan Yunin 2024 an samu raguwar kai hare-hare, inda aka kai hari sau 618. Wannan na nuna cewa an samu raguwar kai hare-hare da kashi 19.32 cikin 100 idan aka haɗa da hare-hare 766 da aka kai a watan Mayu".
Haka nan rahoton ya nuna cewa an samu raguwar matsalar garkuwa da mutane a Najeriyar cikin watan na Yuni da kimanin kashi 58.59 cikin 100.
"An yi garkuwa da mutum 1,128 a watan Mayun 2024, yayin da a watan Yuni aka yi garkuwa da 467."
A ɓangaren kashe-kashe kuwa, shi ma rahoton ya una cewa an samu raguwa da kashi 5.96 cikin 100.
"An kashe mutum 1,090 a watan Mayun 2024, inda a Yuni abin ya ragu zuwa 1,025 a watan Yuni."
Harin ƙunar baƙin wake da ƙungiyar Boko Haram ta kai a garin Gwoza na jihar Borno, wanda ya kashe aƙalla mutum 30 a ƙarshen watan Yuni, ya ƙara fito da matsalar tsaro da ake fuskanta a sassa daban-daban na ƙasar.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha yin iƙirarin tarwatsa ƙungiyar.
Haka nan, ƴan fashin daji na cigaba da kai samame suna kashe mutane da garkuwa da su a jihohi kamar Zamfara, da Katsina, da Kaduna, a arewa maso yammacin ƙasar.
Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da bai wa ma'aikata bashin kuɗin noma
Bayani kan maƙala
Marubuci, Zahraddeen Lawan
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Daga Kano
Asalin hoton, X/Umar Namadi
Gwamnatin jihar Jigawa a raewacin Najeriya ta ƙaddamar da shirin tallafa wa ma'aikata a ɓangaren noma.
Shirin ya tanadi bai wa ma'aikatan gwamnati bashi ta yadda za su iya bayar da tasu gudunmawa wajen noma wasu zaɓaɓɓun amfanin gona.
Shirin bayar da bashin zai samar da tallafin kayan aikin gona da kuɗin aiki don noma amfanin gona kamar shinkafa, da riɗi, da gero, da kuma dawa, inda ake fatan ma’aikatan za su biya bashin bayan kammala girbi.
Hukumomin jihar sun ce sun ɓullo da shirin ne la’akari da halin matsi da kuma tsadar rayuwa, ta yadda hakan zai bai wa ma’aikata damar noma abin da za su ci da kuma samun kuɗi.
Shugaban Ma'aikata Muhammad Kandira Dagaceri, shi ne shugaban kwamitin da ke kula da shirin bayar da bashin kuma ya ce sun buɗe wani shafi a internet inda ma’aikaci zai yi rajista.
"Yanzu mun fara da ma'ikata 8,432 a kashin farko," in ji shi.
Mahamat Deby ya fasa kai ziyara Faransa kan zargin almubazzaranci
Asalin hoton, @GmahamatIdi
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby ya soke ziyarar da ya yi niyyar kaiwa Faransa a yau Litinin sakamakon binciken da hukumomin Faransar ke yi game da dukiyarsa, a cewar rahoton da kafar yaɗa labarai ta Alwihda.
Hukumomin Chadi sun soki binciken a ranar 5 ga watan Yuli, inda suka kira shi da "yunƙurin tayar da fitina" a ƙasar ta yammacin Afirka.
Masu shigar da ƙara a Faransa na zargin shugaban na Chadi da kashe dala 980,000 kan tufafi masu tsada da wani shahararren tela ya ɗinka masa a Faransa.
Sai dai shafin kafar yaɗa labaran ya ce zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban na Chadi.
Ana sa ran Mahamat Deby zai tattauna da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron game da makomar sojojin Faransan a ƙasarsa.
An kama mai kashe mutane ya jefa su a juji a Kenya
Asalin hoton, AFP
'Yan sandan Kenya sun ce sun kama wani mutum da suka yi wa laƙabi da "mai kashe mutane" da ake zargi da kisan gillar da aka yi wa mata tara, wanda aka gano gawarwakinsu a wani wuri da ake zubar da shara.
An kama Jomaisi Khalisia mai shekaru 33 a safiyar Litinin a wata mashaya yayin kallon wasan ƙarshe na gasar Euro.
‘Yan sanda sun ce ya amsa laifin kashe mata 42 tun daga shekarar 2022, ciki har da matarsa.
Gano gawarwakin dai ya haifar da kaɗuwa da bacin rai a faɗin ƙasar Kenya.
Mohamed Amin, shugaban hukumar binciken manyan laifuka (DCI), ya bayyana cewa, "Jomaisi Khalisai ya amsa laifinsa, ya ce ya kashe tare da kuma zubar da gawarwakin mata 42 a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024."
Bayan kama shi, an bayar da rahoton cewa, Khalisia ya jagoranci jami’an tsaro zuwa gidansa, wanda ke da tazarar mita 100 daga wurin da lamarin ya faru domin bincike.
A gidan nasa ne ƴan sandan suka ƙwato kayayyakin da yake amfani da su da suka hada da wayoyi 10, da kwamfutar tafi-da-gidanka, da katunan shaida, da tufafin mata da adduna da ake kyautata zaton da shi yayi amfani wajen kashe matan da buhu 9 da ake zargin da su aka yi amfani wajen kwashe gawarwakin.
Tun a ranar Juma'a, 'yan sanda suka tsare wurin zubar da sharar yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Ba ni da gida a ƙasar waje kuma haya nake biya a Abuja - Ɗangote
Asalin hoton, X/DANGOTE
Mutumin da ya fi kowa kuɗi a nahiayr Afirka, Aliko Ɗangote ya bai wa jama'a da dama mamaki tun bayan da ya sanar da cewa ba shi da gida a ƙasashen waje.
Ɗangoto ya kuma sanar da cewa gidajensa biyu ne rak sannan kuma gidan haya yake sauka a duk lokacin da ya je Abuja, babban birnin Najeriya.
Aliko Ɗangote ne dai attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a karo na 13 a jere duk da irin ƙalubalen tattalin arziƙin da Najeriya ke fuskanta.
Dukiyar Ɗangote ta ƙaru da dala miliyan 400 a shekarar da ta gabata, inda yawan arziƙinsa ya kai dala biliyan 13.9 kamar yadda mujallar Forbes a lokacin.
Hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru zuwa 34.19 a watan Yuni - NBS
Asalin hoton, EPA
Hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru zuwa kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin da ya gabata, a cewar sababbin alƙaluma daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa.
Hakan na nufin an samu ƙaruwar kashi 2.31 cikin 100 idan aka kwatanta da 2.14 da aka samu a watan Mayun da ya biyo baya.
Cikin rahoton da ta fitar a yau Litinin, National Bureau of State Statistics (NBS) ta ce yawan ƙaruwar farashi a watan na Yuni ya zama maki 0.24 idan aka kwatanta da yawan adadin hauhawar da aka samu a watan Mayun 2024.
"A watan Yunin 2024, jimillar hauhawar farashin ta ƙaru zuwa kashi 34.19 saɓanin ta watan Mayun 2024 da aka samu 33.95," in ji rahoton. " Idan aka kwatanta sauyin, za a ga yawan hauhawar na Yuni ya ƙaru da kashi 0.24 idan aka kwatanta da na Mayun 2024.
"Idan aka kwatanta da irin wannan lokacin na shekarar da gabata kuma, an samu ƙarin kashi 11.40 a Yunin 2024 saɓanin wanda aka samu a watan Yunin 2023, inda jimillar hauhawar ta kai 22.79."
A ɓangaren kayan abinci kuma, farashi ya hauhawa da kashi 2.55 cikin 100 a watan Yuni, inda kuma a watan Mayu aka samu ƙarin 2.28.
NBS ta ce tashin farashin gyaɗa, da mai, da doya, da rogo, da dankali (na Turawa da na Hausa), da kifi, da sauransu su ne suka haifar da hauhawar farashin.
PDP ta yi wuf da komai a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Adamawa
Asalin hoton, Adamawa State Government
Bayanan hoto, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri kenan lokacin da ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen na ranar Asabar
Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta yi nasara a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar, inda ta lashe baki ɗaya kujerun yankuna 21 na jihar, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
A cewar sakamakon da hukumar zaɓen jihar ta Adamawa State Independent Electoral Commission (ADSIEC) ta fitar, PDP ce kuma ta cinye duka kujerun kansiloli, ban da Mazaɓar Demsa ta ƙaramar hukumar Demsa da NNPP ta ci kansila ɗaya.
Da yake sanar da sakamakon a jiya Lahadi a birnin Yola, shugaban hukumar zaɓen jihar, Mohammed Umar, ya ce jam'iyya 12 ne suka shiga zaɓen daga cikin 19 da ke da rajista.
A hukuncin nata na ranar Alhamis, kotun ta kuma bai wa ƙananan hukumomin 'yancin kashe kuɗinsu da kansu a matsayinsu na mataki na uku a tsarin gwamnati - bayan tarayya da jiha - sannan ta umarci gwamnatin tarayya ta dinga tura musu kasonsu kai-tsaye, ba ta hannun gwamnoni ba.
Kagame na neman wa'adi na huɗu a matsayin shugaban Rwanda
Asalin hoton, AFP
Shugaban Rwanda Paul Kagame - wanda ake tsoro da kuma sha'awa - na neman tsawaita wa'adinsa na shekaru 24 a zaɓe mai zuwa, wanda manazarta ke hasashen zai yi nasara da gagarumin rinjaye.
Kagame, wanda ya mamaye kowane zaɓe tun lokacin da ya zama shugaban ƙasa a shekara ta 2000 da sama da kashi 90 cikin 100 na kuri'un da aka kada, ya samu gagarumar nasara da kashi 99 cikin 100 a zaɓen 2017.
Yanzu dai yana da shekara 66, kuma yana fuskantar ‘yan takara biyu ne kacal saboda hukumar zaɓe ta ƙasar ta hana sauran ‘yan takara tsayawa.
Kagame ya kasance jigo a fagen siyasar Rwanda tun bayan da dakarunsa na tawaye suka kawo karshen kisan kiyashin da aka yi a shekarar 1994, wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan ƙabilar Tutsi da Hutu masu matsakaicin ra'ayi kimanin 800,000.
Dr. Felix Ndahinda ya yaba wa shugabancin Kagame kan zaman lafiyar ƙasar cikin shekaru 30 da suka gabata.
Sai dai masu suka na zargin Kagame da murkushe 'yan'adawa da kuma kitsa kisan gillar da ake yi musu, yayin da yake kare haƙƙin ɗan'Adam na Rwanda.
Kimanin masu kaɗa ƙuri'a miliyan tara ne suka yi rajista a zaɓe mai zuwa.
Masu kada ƙuri'a za su zabi shugaban kasa da 'yan majalisar wakilai 53, inda za a zaɓi ƙarin 'yan majalisa 27 a washegari.
Ga mafi yawan matasan Ruwanda, Kagame ne kawai shugaban da suka sani.
Dakarun RSF sun kashe fararen hula 23 a Sudan - Rahoto
Asalin hoton, Reuters
Dakarun rundunar ƙawance ta RSF a Sudan sun kashe aƙalla fararen hula 23 a wani ƙauye da ke tsakiyar jihar Arewacin Kordofan, inda aka zargi mayaƙanta da buɗe wa wani jerin gwanon motocin haya wuta, a cewar rahoton jaridar Sudan Tribune.
"RSF ta aikata kisan kiyashi a Arewacin Kordofan ranar Asabar, inda suka buɗe wuta kan wasu jerin motocin haya tare da kashe fararen hula 23," in ji rahoton.
Ta ambato ƙungiyar Sudanese Doctors Network ta likitocin Sudan na cewa RSF "ta aikata sabon kisan kiyashi a kan wasu mutanen ƙauyen Fanquqa sakamakon buɗe musu wuta suna kan hanyar zuwa kasuwa".
An sha zargin ƙungiyar RSF da ke iko da wurare da yawa a Arewacin Kordofan da aikata kashe--kashe a jihar, ciki har da sace-sace, da tsare mutane, da kuma ɓatar da su.
Yaƙi tsakanin RSF da dakarun sojin gwamnatin Sudan ya shiga wata 15, yayin da kamfanin labarai na Rakoba ya ruwaito a jiya cewa wasu dakarun RSF sun koma ɓangaren sojoji a yankin Al-Nuhud na Kordofan ɗin tare da miƙa ababen hawa na soji 15.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama riƙaƙƙun 'yanbindiga a jihar Taraba
Asalin hoton, NG Army
Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama wasu ƙasurguman 'yanbindiga biyu a jihar Taraba da ke tsakiyar ƙasar tare da ƙwace babura daga hannunsu.
Wata sanarwa da mataimakin kakakin runudunar, Kanal Oni Olubodunde, ya fitar ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Stroke ne suka yi nasarar kama mutanen da ba ta bayyana sunansu ba a ranar Alhamis.
"Samamen da dakaru suka kai bayan tattara bayanan sirri a ƙauyen Geshi na ƙaramar hukumar Donga a jihar Taraba ya yi sanadiyyar ƙwato babur biyu da 'yanta'addan ke amfani da su," in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa an samu bayanan sirrin ne bayan wasu mahara sun kai hari, inda dakaru suka ɗunguma zuwa Geshi kuma suka fara musayar wuta da su "abin da ya sa suka tsere zuwa cikin daji".
"Yanzu haka 'yanta'addan na hannunmu domin gudanar da bincike."