Labarin wasanni daga 01 zuwa 06 ga watan Fabrairu 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 01 zuwa 06 ga Fabrairu 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Daga Jaridu

    Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Everton za ta yi wa ɗanwasan gaba na Ingila Dwight McNeil tayin sabuwar yarjejeniya bayan ya gaza komawa Crystal Palace kafin rufe kasuwar ƴanwasa. (Football Insider)

    Newcastle za ta farfaɗo da buƙatarta kan ɗanwasan tsakiya na Ivory Coast Patrick Zabi, mai shekara 19. (The i - subscription required)

    Golan Leeds United da Faransa Illan Meslier, mai shekara 25, ga alama zai koma Turkiya a ƙungiyar Besiktas. (Teamtalk)

    Ɗanwasan tsakiya na Jamus Leon Goretzka, mai shekara 30, wanda yarjejeniyarsa ta kawo ƙarshe a Bayern Munich zai iya komawa Arsenal. (Bayern Insider)

    West Ham na iya rasa kocinta Nuno Espirito Santo ba tare da biyan diya ba idan har ƙungiyar ta koma buga Championship. (Athletic - subscription required)

  2. Manchester City za ta kara da Newcastle a Carabao Cup, Carabao Cup

    Haaland

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a kammala wasa na biyu zagayen daf da karshe a Carabao Cup ranar Laraba, tsakanin Manchester City da Newcastle United mai rike da kofin da za su ɓarje gumi a Etihad.

    Ranar 13 ga watan Janairu, City ta yi nasarar cin Newcastle 2-0, kuma ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama na fatan lashe League Cup a bana na tara jimilla rabonsu da shi tun 2021.

    Ita kuwa Newcastle ɗaya ne da ita, mai fatan lashe Carabao Cup karo na biyu jimilla.

    Arsenal – za ta buga wasan karshe a Wembley da duk wadda ta yi nasara tsakanin City ko Newcastle United.

    A jiya Gunners ta ci Chelsea 1-0 a Emirates, kenan da cin kwallo 4-2 gida da waje.

    Arsenal na bukatar kofin nan, wanda rabonta da shi tun 1993.

  3. Fenerbahce ta ɗauki Kante daga Al-Ittihad, Babbar gasar tamaula ta Saudiyya

    Kante

    Asalin hoton, Getty Images

    Fenerbahce ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan tawagar Faransa, N'Golo Kante, daga Al-Ittihad mai buga babbar gasar tamaula ta Saudiyya.

    A ranar Talata, shirin ɗan wasan Faransan na komawa Turkiyya ya kusan rushewa, bayan Fenerbahce ta fitar da sanarwa tana zargin Al-Ittihad da haddasa kawo cikas a cinikin.

    Fenerbahce ta ce Al-Ittihad ta kasa cika takardun da ake bukata don kammala kulla yarjejeniya daga ciki ɗan wasan tawagar Morocco, Youssef En-Nesyri ya koma Al-Ittihad.

    Sai dai a ranar Laraba, Fenerbahce ta tabbatar da cewa an warware matsalar da ke tsakaninsu, kuma Kante tsohon ɗan wasan Chelsea ya koma Turkiya, bayan shafe shekara biyu da rabi a Saudiyya.

    Kante, mai shekaru 34, ya koma Al-Ittihad daga Chelsea a shekarar 2023, bayan lashe Gasar Zakarun Turai (Champions League) da Premier League da Europa League da FA Cup.

    Ya koma Chelsea ne daga Leicester City a shekarar 2016, bayan da ya bayar da gudunmuwar da Leicester ta lashe kofin Premier League.

    En-Nesyri, mai shekaru 28, zai maye gurbin tsohon ɗan wasan Real Madrid, Karim Benzema, wanda ya koma Al-Hilal a makon nan.

  4. Arsenal ta kai wasan ƙarshe a gasar Carabao

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan kusan shekara shida da kuma rashin nasara sau huɗu a wasan kusa da na ƙarshe, a wannan karon Arsenal ta doke Chelsea da ci 4-2 a gasar Carabao domin zuwa wasan ƙarshe.

    Wannan ne karon farko da Arsenal ta kai wannan matakin a ƙarƙashin horarwar Mikel Arteta bayan jan ragamar ƙungiyar ta lashe kofin FA a shekarar 2020.

    Ɗan wasan Arsenal, Havertz ne ya zura ƙwallo a ragar Chelsea a minti 90+7 a wasan na biyu, bayan samun nasara a wasan farko da 3-2, inda jimilla ya zama Arsenal ta doke Chelsea da ci huɗu da biyu.

    Yanzu Arsenal za ta jira sakamakon wasan Manchester City da Newcastle domin sanin ƙungiyar da za ta fafata da ita a wasan ƙarshe na gasar a ranar Lahadi 22 ga watan Maris.

    A shekarar 2018 ne aka buga wasan ƙarshe na gasar tsakanin Arsenal da Man City, a lokacin kocin Arsenal na yanzu, Mikel Arteta yana mataimakin Pep Guardiola a City, inda City ta samu nasara a wasan.

  5. , Daga Jaridu

    Sterling

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Marcus Rashford, mai shekara 28, ba ya son komawa Manchester United idan wa'adin zamansa ya kawo ƙarshe a matsayin aro a Barcelona kuma ɗanwasan na Ingila zai amince a rage masa albashi don ya ci gaba da taka leda a Spain. (Mirror)

    Tsohon ɗanwasan tsakiya na Liverpool Xabi Alonso ana tunanin yana cikin mutum uku da ake sa ran za su gaji Pep Guardiola yayin da ake ganin wannan ce kakarsa ta ƙarshe a matsayin kocin Manchester City. (Telegraph - subscription required)

    Ɗanwasan gaba Dayot Upamecano, mai shekara 27, na shirin sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Bayern Munich. (Fabrizio Romano)

    Ɗanwasan baya na Manchester United Tyrell Malacia, mai shekara 26 na fushi da daraktan wasanni Jason Wilcox kan toshe damarsa ta barin Old Trafford. (Mirror)

  6. Morocco za ta ɗaukaka kara kan hukuncin da aka yi wa Senegal, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Morocco ta sanar a ranar Talata cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin ladabtarwa da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta yanke game da wasan ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi cikin ruɗani a watan da ya gabata da Senegal, inda mai masaukin baki ta sha kashi da ci 1-0 bayan ƙarin lokaci.

    Morocco ta soki hukuncin tana mai cewa ba su tsanani ba kan laifukan da aka aikata a wasan ranar 18 ga Janairu ba.

    An ci karo da tsaikon minti 14 a karawar, bayan da wasu ƴan wasan Senegal suka fice daga fili, an kuma samu yamutsi tsakanin magoya bayansu da jami'an kasar.

    Kwamitin ladabtarwa na CAF ya dakatar da kocin Senegal, Pape Thiaw tsawon wasa biyar da cin tarar dalar Amurka 100,000, saboda shi ne ya umurci ƴan wasan su bar filin, sakamakon hukuncin VAR da ta bai wa Morocco bugun fenariti.

    Haka kuma, an ci tarat hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal dalar Amurka 615,000, saboda halayyar ƴan wasa da magoya bayanta.

    An kuma dakatar da Iliman Ndiaye da Ismaila Sarr wasa biyu kowanne, saboda rashin ɗa'a da suka nuna ga alkalin wasa.

    Morocco, wadda CAF ta ƙi amincewa da ƙarar da ta shigar na neman sauya sakamakon wasan, itama an ci tararta dalar Amurka 315,000.

    Hukuncin ya shafi abin da CAF ta bayyana a matsayin rashin ɗa’a daga ƴan wasan Morocco da jami’an tawagar da magoya baya, ciki har da amfani da hasken laser da kuma shiga tsakani ba bisa ƙa’ida ba a yankin da VAR take.

    An dakatar da ƙyaftin ɗin Morocco, Achraf Hakimi wasa biyu, yayin da Ismael Saibari aka dakatar da shi wasa uku. An hukunta ƴan wasan ne saboda yunƙurin cire tawul ɗin mai tsaron ragar Senegal, Edouard Mendy.

    Morocco za ta ɗaukaka ƙara kan waɗannan hukuncin domin kare dukkan haƙƙoƙin da doka ta tanada,” in ji wata sanarwa daga hukumar, wadda ta jaddada “ficewar ‘yan wasan Senegal daga fili da kuma halayen magoya bayansu” a matsayin hujjar ƙalubalantar hukuncin.

    Sai dai CAF ta bayyana gasar a matsayin wacce ta yi nasara gaba ɗaya, ta kuma ce ta samu kuɗi masu yawa a tarihi duk da rikicin da ya biyo bayan wasan ƙarshen.

    CAF ta kuma tabbatar da cewa hukuncin da ta yanke zai shafi dukkan gasar da take shiryawa.

  7. Arsenal za ta kara da Chelsea a daf da karshe a Carabao Cup ranar Talata, Carabao Cup

    Arsenal za ta karɓi bakuncin Chelsea a wasa na biyu na daf da karshe a Carabao Cup da za su fafata a Emirates ranar Talata.

    A cikin watan Janairu Arsenal ta je ta doke Chelsea 3-2 a Stamford Bridge.

    Gunners na fatan ɗaukar Carabao Cup na uku jimilla rabonta da shi tun 1993, ita kuwa Chelsea na fatan cin na shida tun bayan 2015.

    Liverpool ce kan gaba a yawan lashe League Cup a tarihi mai 10 jimilla.

  8. , Daga Jaridu

    Aubameyang

    Asalin hoton, Getty Images

    Malacia na shirin hawa jirgi zuwa Turkiya a Besiktas kafin Wilcox ya fada masa cewa dole ya ci gaba da zama a Manchester United. (Talksport)

    Tsohon ɗanwasan Chelsea da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 31, an yi masa tayin zuwa Union Berlin a kwanakin baya amma ya ki amincewa. (Florian Plettenberg)

    Ɗanwasan gaba na Faransa Karim Benzema, mai shekara 38, zai bar Al-Ittihad zuwa Al-Hilal ta Saudiyya. Benzema ya ƙulla yarjejeniya da Al-Ittihad ta shekara uku bayan ya baro Real Madrid a 2023. (The Athletic)

    Tottenham ta kasa cimma yarjejeniya da Monaco kan Maghnes Akliouche, mai shekara 23, amma tana fatan sake taya ɗanwasan na Faransa a bazara. (Teamtalk)

  9. Da alama Ronaldo ya shiga damuwa a Saudiyya, Babbar gasar tamaula ta Saudiyya

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    An fara tababa kan makomar Cristiano Ronaldo a ƙungiyarsa ta Al-Nassr bayan rashin ganinsa a wasan da ƙungiyar ta buga ranar Litinin da ƙungiyar Al-Riyadh a babbar gasar ƙasar ta Saudi Pro League.

    Jaridar Bola ta ƙasar Portugal ta ce Ronaldo, mai shekara 40 a duniya ya ƙi buga wasan ne bayan nuna ɓacin ransa kan yadda ake tafiyar da lamurran ƙungiyar.

    Al-Nassr da Al-Hilal su ne ƙungiyoyi biyu mafiya nasara a Saudiyya, wadanda kuma Asusun Zuba Jari na Gwamnatin Saudiyya (PIF) ke gudanarwa, wanda kuma ke da hannu a tafiyar da ƙungiyae Newscastle da ke Ingila.

  10. Verona ta kori kociyanta, Zanetti, Serie A

    Hellas Verona da ke matakin ƙarshe a teburin gasar Serie A ta kori kocinta, Paolo Zanetti bayan shekara daya da rabi a kan mukamin, sakamakon rashin nasara takwas a jere.

    Verona, wadda ta sha kashi da ci 4–0 a hannun Cagliari a ranar Asabar, wasa biyu kacal ta ci a bana da canjaras takwas mai maki 14 bayan karawar mako na 23.

    Zanetti ya jagoranci Verona zuwa matsayi na 14 a Serie A a kakar da ta gabata - kungiyar za ta karɓi baƙuncin Pisa da ke matsayi na 19 ta biyun karshen teburi da maki 14 iri daya da na Verona.

  11. Ƴan wasa bakwai aka saya a Premier League ranar rufe kasuwa, Premier League

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasuwar saye da sayar da ƴan wasa a Premier League a watan Janairun 2026 ta kasance mafi ƙarancin hada-hada a tarihinta a ranar da aka rufe ta, inda ƴan wasa bakwai aka saya ranar Litinin.

    Cikin cefanen da aka yi ranar karshe har da Jorgen Strand Larsen da Crystal Palace ta saya daga Wolverhampton kan fam miliyan 48.

    An kuma tabbabar da kammala cinikayya biyar, bayan da aka rufe kasuwar da karfhe takwas na dare daidai da agogon Najeriya da Niger daga cikinsu Sunderland ta sayi ɗan wasan Ecuador, Nilson Angulo daga Anderlecht kan fam miliyan 17.5. Haka kuma Wolverhampton ta ɗauki aron Angel Gomes daga Marseille, sannan ta maye gurbin Strand Larsen da Adam Armstrong daga Southampton kan fam miliyan bakwai.

    Wannan ya kai jimillar kuɗin da aka kashe a Premier League a kasuwar hunturu zuwa sama da fam miliyan 390.

    Liverpool ma ta cimma yarjejeniya a ranar ƙarshe, wadda ta sayi mai tsaron baya, Jeremy Jacquet daga Rennes kan fam miliyan 60, amma zai ci gaba da taka leda a Faransa har sai kan fara kakar baɗi zai koma Anfield.

    A dokance an bayar da awa biyu tsakani da wa'adin rufe kasuwa da zarar ƙungiyoyi biyu sun gabatar da takardar ciniki a tsakaninsu.

  12. Lookman ya koma Atletico Madrid daga Serie A, La Liga

    Lookman

    Asalin hoton, Getty Images

    Atletico Madrid ta ɗauki ɗan wasan tawagar Najeriya, Ademola Lookman kan fam miliyan 30.3 daga Atalanta.

    Lookman zai zama wanda aka haifa a Ingila da ya taka leda a Premier League da Bundesliga da Serie A da kuma La Liga.

    Ƴan wasa 21 ne suka buga manyan gasar Turai hudu a tarihi, yayin da uku ne suka kara a gasa biyar har da ta Ligue 1 ta Faransa da ya hada da Christian Poulsen da Justin Kluivert da kuma Stevan Jovetic.

    Mai shekara 28 ya fara taka leda a Serie A tun daga 2022 da cin kwallo 55 da bayar da 27 aka zura a raga tun bayan da ya koma can daga RB Leipzig mai buga Bundesliga.

  13. Cinikayyar da ake kafin a rufe kasuwa ranar Litinin

    2 ga watan Fabrairu

    14:00: Fally Mayulu [Bristol City - FC Arouca]

    13:31: Juan Larios [Southampton - Real Zaragoza] aro

    09:55: Moussa Sissoko [Watford - Panathinaikos]

    09:00: Brajan Gruda [Brighton - RB Leipzig] aro

    English Football League

    15:00: Ryan Doherty [Stevenage - Ipswich]

    15:00: Elliot Lee [Wrexham - Doncaster] aro

    15:00: Patrick Roberts [Sunderland - Birmingham]

    15:00: Nik Tzanev [Newport - Huddersfield]

    15:00: Ethan Wheatley [Man Utd - Bradford] aro

    14:30: Jack Hunt [Stockport - Wigan] ƙwantiragi ya kare

    14:00: Omar Beckles [Leyton Orient - Gillingham] ƙwantiragi ya kare

    13:30: Tyler Roberts [Birmingham - Mansfield] ƙwantiragi ya kare

    13:12: James Morris [Watford - Leyton Orient]

    13:00: Leo Hjelde [Sunderland - Sheffield United] aro

    13:00: Jamaldeen Jimoh-Aloba [Aston Villa - West Brom] aro

    1 ga watan Fabrairu

    English Football League

    Tayo Adaramola [Crystal Palace - Sheffield Wednesday] aro

    Oladapo Afolayan [St. Pauli - Blackburn]

    Elijah Campbell [Everton - Port Vale] Loan

    Laminne Fanne [Luton - Venezia]

    Andre Garcia [Reading - Club Brugge]

    Calum Kavanagh [Bradford - Oldham]

    Anthony Patterson [Sunderland - Millwall] aro

    Calum Scanlon [Liverpool - Cardiff]

    Martin Sherif [Everton - Port Vale]

    Mohamed Toure [Randers - Norwich]

    Zak Vyner [Bristol City - Wrexham]

    Lewis Warrington [Walsall - Tranmere]

    Tommy Watson [Brighton - Millwall] aro

    Willum Willumsson [Birmingham - NC Nijmegen]

  14. Liverpool na shirin auna koshin lafiyar Jacquet daga Rennes, Liverpool

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool na daf da auna koshin lafiyar ɗDan bayan Rennes, Jeremy Jacquet, kafin a kammala rufe kasuwar saye da sayar da ƴan wasa ta Turai ranar Ltinin kan fam miliyan 60.

    Sai dai zai ci gaba da wasa a Rennes zuwa karshen kakar nan, daga nan ya koma Anfield kan fara kakar baɗi da zarar an kammala cimma komai.

  15. , Daga Jaridu

    Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Celtic ta yi watsi da tayin fam miliyan 14 daga Nottingham Forest kan ɗanwasan tsakiya na Belgium Arne Engels. (Mail)

    Liverpool na son ɗauko ɗanwasan Inter Milan da Netherlands mai shekara 29 Denzel Dumfries. (Fabrizio Romano)

    Chelsea na sa ido kan ɗanwasan baya na Nantes da Faransa mai shekara 18 Tylel Tati. (L'Equipe)

    Leicester City da Birmingham City na ciki ƙungiyoyin da ke buga Championship da suka tuntuɓi Newcastle United kan ɗanwasan baya Jamaal Lascelles. (Sky Sports)

    Brighton na tattaunawa da Marseille kan dawo da ɗanwasan tsakiya da ta bayar aro Matt O'Riley. (Athletic - subscription)

  16. Ba za a matsa wa Estevao sai ya koma Chelsea daga hutun da yake aBrazil ba, Chelsea

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Chelsea, Liam Rosenior, ya ce ba zai tilasta wa Estevao komawa ƙungiyar da wuri ba, bayan da aka bashi izinin zuwa Brazil ranar Asabar.

    Matashin mai shekaru 18 ya koma gida ne bayan samun tutu, domin magance wani lamari na kashin kansa, kuma ba a sa ran zai buga wasa na biyu a zagayen daf da karshe a Carabao Cup da Arsenal ranar Talata a Emirates.

    Wannan ce kakarsa ta farko a Ingila bayan da ya koma Chelsea daga São Paulo.

    Da aka tambaye shi game da yiwuwar ranar dawowarsa, Rosenior ya ce: “Ban sani ba tukunna. Yaro ne matashi da yake sa ƙwazo matuƙa.

    Yana fuskantar wani lokaci mai matuƙar wahala, shi ya sa muka bashi hutu, domin ya samu natsuwa.''

    Tun bayan zuwansa, Stamford Bridge ya zura ƙwallo shida a wasa 29 da ya buga.

  17. , Daga Jaridu

    Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Juventus ta tuntuɓi Everton kan Beto, amma ƙungiyar ba ta son rabuwa da ɗanwasan gaban na Guinea-Bissau mai shekara, 28, domin yana cikin manyan ƴanwasanta maciya raga. (Talksport)

    Juventus na dab da cimma yarjejeniya da Manchester City kan ɗanwasan gaba Justin Oboavwoduo. (Sky Sports Italia - in Italian)

    Tottenham da Leeds United da Sunderland na sa ido kan matashin ɗanwasan gaba na Real Madrid da Brazil Endrick, wanda ke taka rawar gani a Lyon a matsayin aro. (Fichajes)

    Ga alama Manchester United ba za ta iya hana ɗanwasan gaba na Ingila Marcus Rashford mai shekaru 28 ci gaba da taka leda a Barcelona ba idan har Barca ta biya fam miliyan 26 ƙarƙashin yarjejeniyar karɓar aronsa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

    Nottingham Forest za ta sauya ra'ayi bayan rashin nasarar samun ɗanwasan tsakiya na Inter Milan da Italiya Davide Frattesi, mai shekara 26. (Sky Sports)

  18. Afirka ta Kudu ta nisanta kanta da shirya Wafcon 2026, Gasar kofin Afirka ta mata ta 2026

    Wafcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan wasanni na Afirka ta Kudu, Gayton McKenzie, ya ce “ba a yanke hukunci ba” kan sauya wurin da za a gudanar da gasar Kofin Afirka ta Mata (Wafcon) 2026 daga Morocco, bayan da mataimakiyarsa ta sanar da cewa Afirka ta Kudu za ta karɓi bakuncin gasar.

    McKenzie ya fitar da wata sanarwa domin fayyace batun, bayan Peace Mabe ta bayyana cewa ƙasar “za ta karɓi bakuncin” gasar, wadda aka shirya fara ta daga ranar 17 ga Maris.

    Sai dai daga baya, McKenzie ya ce Morocco “har yanzu ita ce ƙasar da aka ayyana a hukumance a matsayin mai masaukin baƙin gasar” Wafcon 2026.

    Hukumar ƙwallon kafa ta Afirca CAF ba ta ce za ta ɗauke wasannin ba daga Morocco, sai dai Afirka ta Kudu ta yi tayin maye gurbin Morocco da zarar an bukaci hakan.

    An tuntuɓi Caf domin jin ta bakin su.

  19. Watakila Bellingham zai yi jinyar mako huɗu, Real Madrid

    Real Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Watakila ɗan wasan Real Madrid, Jude Bellingham ya yi jinyar mako huɗu sakamkon raunin da ya ji ranar Lahadi a wasan La Liga.

    Ɗan ƙwallon tawagar Ingila ya ji rauni ne a lokacin da yake gudu zai taro ƙwallo sai aka ga ya tsaya cak daga baya ya kwanta a cikin fili yana kuka a karawar da Real ta ci Rayo Vallecano 2-1.

    Real Madrid ta fitar da sanarwar cewar matashin ya ji rauni a tsokar cinyan hagu, amma ba ta fayyace kawanakin da zai yi jinya ba.

    To sai dai wasu na cewa irin raunin da ya ji, watakila ya yi jinyar mako huɗu ko fiye da haka.

    Kenan ba zai samu buga karawar cike gurbi a Champions League ba da Benfica gida da waje da aka tsara yi ranar 17 da kuma 25 ga watan Fabrairu.

    Ana kuma cewa watakila sai a wasan hamayya da Real Madrid za ta yi da Atletico Madrid ranar 22 ga watan Maris ake sa ran Bellingham zai koma taka leda leda.

  20. Mbappe ne ya ci ƙwallon da Real Madrid ta doke Vallecano, Gasar La Liga

    Real Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Kylian Mbappe ne ya ci wa Real Madrid ƙwallo na biyu a bugun fenariti da ta kai ta samu nasara 2-0 a kan Rayo Vallecano a gasar La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

    Sai dai kuma Jude Bellingham ya ji raunin a wasan mako na 22 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

    Real ta samu fenariti ne, sakamakon ƙetar da Nobel Mendy ya yi wa Brahim Diaz a minti na 100, hakan ya sa Real Madrid ta rage tazarar maki tsakaninta da Barcelona zuwa ɗaya a gasar La Liga.

    Vinicius Junior ne ya fara zura ƙwallo, daga baya Vallecano ta farke ta hannun Jorge de Frutos.

    Mbappe da Eduardo Camavinga sun buga ƙwallo ta bugi raga, yayin da Rayo Vallecano ta karasa karawar da yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Pathe Cisse jan kati kai tsaye, sakamakon mummunar keta da ya yi wa Dani Ceballos.