Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 01 zuwa 06 ga watan Fabrairu 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 01 zuwa 06 ga Fabrairu 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. United ta ci wasa uku a jere a Premier League a karkashin Carrick, Premier League

    Manchester United ta yi nasara 3-2 a kan Fulham a wasan mako na 24 a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.

    United ta fara cin ƙwallo ta hannun Casemiro, haka aka je hutu tana gaba da 1-0, bayan da aka koma zagaye na biyu ne ta kara ta hannun Matheus Cunha.

    Bayan da wasa ya yi nisa ne Fulham ta zare ɗaya ta hannun Raul Rimenez a bugun fenariti, sannan Kevin ya karke ta biyu.

    To sai dai United ta kara ta uku ta hannun Sesko, hakan ya sa ta haɗa maki ukun da take bukata.

    Wasa na uku kenan da Micheal Carrick ya lashe a jere a Premier League tun bayan da ya karɓi aikin riƙon kwarya zuwa karshen kakar bana, bayan maye gurbin Ruben Amorim.

    Sai da Amorim ya yi wasa 47 da ta kai yayi nasara uku a United a cikin watan Oktoba, kafin nan ko wasa biyu a jere bai ci ba.

    Da wannan sakamakon United ta koma mataki na huɗu da maki 41 daga karawa 24.

  2. Bellingham ya ji rauni a wasan Vallecano a Barnabeu, Real Madrid

    An cire ɗan wasan Jude Bellingham a wasan da Real Madrid ta karɓi bakuncin Rayo Vallecano a gasar La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu, sakamakon raunin da ya ji.

    Anga ɗan wasa ya tsaya cak a lokacin da yake gudu zai taro ƙwallo a babbar gasar tamaula ta Sifaniya. Ɗan wasan mai shekaru 22 ya kwanta cikin fili, inda abokan wasansa suka rika rarrashinsa. Har yanzu ba a san yadda girman raunin yake ba, amma Bellingham ya fita daga filin da kansa ba tare da taimako masu duba lafiyar ƴan wasansa ba, bayan an maye gurbinsa da Brahim Diaz.

    Tawagar Ingila za ta buga wasan sada zumunta da Uruguay ranar 27 ga watan Maris da kuma Japan ranar 31 ga Maris, kafin su fara gasar cin kofin duniya da karawar farko da Croatia a ranar 17 ga Yuni.

  3. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.