Hukumar ƙwallon ƙafa ta Morocco ta sanar a ranar Talata cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin ladabtarwa da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta yanke game da wasan ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi cikin ruɗani a watan da ya gabata da Senegal, inda mai masaukin baki ta sha kashi da ci 1-0 bayan ƙarin lokaci.
Morocco ta soki hukuncin tana mai cewa ba su tsanani ba kan laifukan da aka aikata a wasan ranar 18 ga Janairu ba.
An ci karo da tsaikon minti 14 a karawar, bayan da wasu ƴan wasan Senegal suka fice daga fili, an kuma samu yamutsi tsakanin magoya bayansu da jami'an kasar.
Kwamitin ladabtarwa na CAF ya dakatar da kocin Senegal, Pape Thiaw tsawon wasa biyar da cin tarar dalar Amurka 100,000, saboda shi ne ya umurci ƴan wasan su bar filin, sakamakon hukuncin VAR da ta bai wa Morocco bugun fenariti.
Haka kuma, an ci tarat hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal dalar Amurka 615,000, saboda halayyar ƴan wasa da magoya bayanta.
An kuma dakatar da Iliman Ndiaye da Ismaila Sarr wasa biyu kowanne, saboda rashin ɗa'a da suka nuna ga alkalin wasa.
Morocco, wadda CAF ta ƙi amincewa da ƙarar da ta shigar na neman sauya sakamakon wasan, itama an ci tararta dalar Amurka 315,000.
Hukuncin ya shafi abin da CAF ta bayyana a matsayin rashin ɗa’a daga ƴan wasan Morocco da jami’an tawagar da magoya baya, ciki har da amfani da hasken laser da kuma shiga tsakani ba bisa ƙa’ida ba a yankin da VAR take.
An dakatar da ƙyaftin ɗin Morocco, Achraf Hakimi wasa biyu, yayin da Ismael Saibari aka dakatar da shi wasa uku. An hukunta ƴan wasan ne saboda yunƙurin cire tawul ɗin mai tsaron ragar Senegal, Edouard Mendy.
Morocco za ta ɗaukaka ƙara kan waɗannan hukuncin domin kare dukkan haƙƙoƙin da doka ta tanada,” in ji wata sanarwa daga hukumar, wadda ta jaddada “ficewar ‘yan wasan Senegal daga fili da kuma halayen magoya bayansu” a matsayin hujjar ƙalubalantar hukuncin.
Sai dai CAF ta bayyana gasar a matsayin wacce ta yi nasara gaba ɗaya, ta kuma ce ta samu kuɗi masu yawa a tarihi duk da rikicin da ya biyo bayan wasan ƙarshen.
CAF ta kuma tabbatar da cewa hukuncin da ta yanke zai shafi dukkan gasar da take shiryawa.