Tsagaita wuta a Gaza na ci gaba da aiki duk da sabbin hare-haren Isra'ila - Trump

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce har yanzu yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Gaza na ci gaba da aiki, sa'o'i bayan da jami'an kiwon lafiya a yankin suka tabbatar da cewa hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama, sun halaka sama da mutum 40.
Isra'ila ta zargi Hamas da kashe sojojinta biyu a kusa da Rafah da ke kudancin Gaza.
Hamas dai ta musanta cewa tana da masaniya kan lamarin, tana mai zargin Isra'ilar da ƙirƙirar wani yanayi don samun damar ci gaba da kai hari da gangan.
Kafofin watsa labaran Isra'ila sun rawaito cewa wani matsin lambar Amurka ya tursasawa Isra'ilar soke matakin da ta ɗauka da farko na rufe hanyoyin shigar da kayan jin ƙai zuwa Zirin Gaza.
Hamas ta kuma zargi Isra'ila da bai wa wasu gungun 'yan daba a Zirin makamai, inda ta ce suna cin karensu ba babbaka a yankunan da har yanzu ke karkashin ikonta.
