Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/10/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Rufewa

    A nan muka kawo muku karshen wannan shafin na labaran kai-tsaye.

    Da fata kun ji dadin kasancewa tare da mu.

    Sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Isra'ila ta karɓa gawar mutum ɗaya daga hannun Hamas

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta ce ta karbi karin gawar mutum daya cikin wadanda aka yi garkuwa da su ta hannun kungiyar bayar da agaji ta Red Cross.

    Hamas na ta ci gaba da dawo da gawarwakin wadanda aka yi garkuwa da su daga Gaza a wani gefe na yarjejeniyar tsagaita wuta, sai dai ta ce ta na fuskantar kalubale wajen ganin wasu gawarwakin cikin baraguzai.

    Tun da farko sojojin Isra'ila sun hallaka wasu mutum uku kusa da birnin Gaza wandanda su ka zarga da tsallaka iyakar da aka amince da ita.

    wakiliyar BBC ta ce a yanzu haka sojojin Isra'ila sun fitar da wani bidiyo da ke nuna wasu manyan motoci na sake zana layin da aka shata.

  3. Hukumar Alhazan Najeriya ta kafa kwamitin kula da jiragen jigilar maniyyata

    Hajj

    Asalin hoton, Ahmad Muazu

    Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya kafa kwamitin kula da jiragen jigilar maniyyata na hajjin shekarar 2026.

    Da yake kafa kwamitin a ɗakin taro a hedkwatar hukumar da ke Abuja, ya buƙaci mambobin da su yi aiki da gaskiya da amana domin tabbatar da samun nasarar bin da ake buƙata daga jiragen da za su yi jigilar maniyyatan.

    "A gwamnatin Najeriya ƙarƙashin Bola Tinubu, samun nasarar Hajj ba aiki ba ne kawai kamar sauran, aiki ne na ibada. Don haka aikinmu ne mu tabbatar dukkan maniyyatan Najeriya sun gudanar da ibadarsu cikin natsuwa da tsaro mai inganci."

    Shugaban ya nanata cewa duk da nasarorin da aka samu a ɓangaren jigila, kula da sa ido kan jiragen jigilar na da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da aikin Hajji.

    "Wannan kwamiti ne mai muhimmanci da yake da aiki babba wajen jin daɗi da walwalar alhazai. Don haka alhakin sa ido kan harkokin jiragen da za su yi jigilar maniyyatanmu na kanku," in ji shi, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Ahmad Muazu ya bayyana.

  4. NLC ta ba gwamnatin Najeriya mako huɗu ta daidaita da ASUU

    NLC

    Asalin hoton, NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta ce ta ba gwamnatin Najeriya mako huɗu ta kawo ƙarshen matsalar da ke tsakaninta da ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya wato ASUU da sauran ƙungiyoyin manyan makarantun ƙasar.

    Ta yi barazanar cewa idan har gwamnatin ba ta ɗauki wani mataki ba har wa'adin ya ƙare, za ta iya ɗaukar mataki babba.

    Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    "Muna so gwamnati ta gama tattaunawa da dukkan ƙungiyoyin manyan makarantun Najeriya nan da mako huɗu. Mun ga sun fara magana da ASUU, amma matsalar ba ta ASUU ba ce kaɗai," in ji shi.

    Ya ce da zarar mako huɗu ya yi, kuma ba su ga wani mataki da aka ɗauka ba, "za mu zauna mu ɗauki matakin da duk wani ma'aikaci da duk wata ƙungiya da ke ƙasar nan za ta shiga maganar har sai an samar da mafita. Yanzu an wuce lokacin da za a riƙa yi wa ƙungiyoyi barazana."

  5. Sojojin Myanmar sun kama dubban masu damfarar intanet

    Hukumomin soji a Myanmar sun ce dakarunsu sun yi nasarar kama daya daga cikin sanannun wuraren damfara da ke kusa da kan iyaka da Thailand.

    Shagunan damfarar intanet inda ma'aikata ke damfarar yan kasashen waje da kasuwanci na karya ko kuma yaudarar soyayya, sun yi ta bunkasa a yankunan da ke kan iyaka a Myanmar.

    Ana zargin wurin da ake kira KK Park, na safarar dubban 'yan kasashen waje tare da tilasta musu gudanar da wasu ayuika na zamba ta intanet.

    Sojojin sun ce sun kama mutane sama da dubu biyu da ke aiki a wurin, da kuma wasu na'urorin sadarwa na kamafanin Starlink na Elon Musk.

  6. EFCC ta ƙwato dukiyar da ta haura naira biliyan 500 a shekara biyu - Shetima

    Kashim

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci alƙalai da sauran ma'aikatan ɓangaren shari'ar ƙasar da su ƙara ƙaimi tare da yin aiki na sani ba sabo wajen tabbatar da adalci, inda ya yi gargaɗin cewa ana fara samun matsala ne a ƙasa da zarar waɗanda aka ba amanar tabbatar da hukunci sun fara cin amana da tauye haƙƙin mai haƙƙi.

    Tinubu ya bayyana haka ne a taron ƙara wa juna sani ga alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar hukumar shari'a ta Najeriya suka shirya a Abuja.

    Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu, ya ce gwamnatinsu ba ta sa baki a harkokin shari'a, "mun ba ɓangaren shari'a da hukumomin yaƙi da cin hanci damar gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba," in ji shi.

    Da yake bayyana irin nasarar da suka samu wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, Shettima ya ce EFCC ta ƙwato samu nasarar ƙwato dukiya da ta haura naira biliyan 500 a cikin shekara biyu.

    "A cikin shekara biyu na wannan gwamnatin, EFCC ta samu nasarar gabatar da sama da mutum 7000 a kotu, sannan ta ƙwato dukiyar da ta haura naira biliyan 500."

    Ya ƙara da cewa kuɗaɗen da aka ƙwato ana karkatar da su ne wajen amfanar da al'umma, musamman wajen aiwatar da shirye-shiryen walwalar al'umma kamar bashin ɗalibai da sauransu.

  7. Jarumin barkwanci finafinan Indiya Asrani ya rasu

    Asrani

    Asalin hoton, Filmfare.com

    Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu.

    Asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350.

    Asrani ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor. Daga cikin fina-finansa da suka yi fice akwai Sholay, inda ya fito a matsayin ɗansand da Bawarchi da Chupke-Chupke da Hera Pheri da Muqabla da Dhamaal da Yamla Pagla Deewana da Dillagi da Welcome da Bhool Bhulaiya da Garam Masala da Baghban da The Burning Train da Ajnabee da Seeta aur Geeta da Sargam da dai sauransu.

    Ya karbi lambobin yabo da dama da suka hada da jarumin da yafi kowa iya barkwanci wanda kamfanin Film Fare ya ba shi.

    Ya mutu ya bar matarsa wadda ita ma jaruma ce wato Manju Asrani da kuma ɗansa Naveen Asrani.

    Ya yi fina-finai da jarumai da dama da suka hada Amita Bachchan da Dharamendra da Jeetandra da Shatugan Sinha da Rajesh Khanna da Rishi Kapoor da Vinod Khanna da Akshay Kumar, Shahrukh Khan da Aamir Khan da Salman Khan da Ajay Devgan da Sanjay Dutt da dai sauransu.

  8. A shirye nake in halarci ganawar Trump da Putin idan an gayyace ni - Zelensky

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa a shirye yake ya halarci taron tattaunawa da ake shirin gudanarwa a Hungary tsakanin Donald Trump da Vladimir Putin, idan aka gayyace shi.

    Shugabannin Amurka da Rasha sun sanar a ranar Alhamis cewa suna shirin yin taron tattaunawa kan yaƙin Ukraine a Budapest cikin makonni masu zuwa.

    Sai dai rahotanni sun ce ganawar da Zelensky ya yi da Trump a Fadar White House ta rikiɗe zuwa hayaniya, inda bangaren Amurka ya matsa masa lamba da ya karɓi sharuddan Rasha don kawo ƙarshen yaƙin.

    Zelensky, wanda ya yi taron manema labarai karo na farko tun bayan ganawar, ya ce tattaunawar ta kasance mai gaskiya amma cike da saɓani.

    Ya bayyana wa Trump cewa burinsa shi ne samun zaman lafiya mai adalci, ba zaman lafiya na gaggawa ba.

    A yayin da aka tambayi Trump ko Zelensky zai shiga taron Budapest, ya ce yana son ya sanya lamarin ya zama “mai dacewa ga kowa.” Ya kara da cewa shugabannin ukun “dole ne su hadu,” kodayake hakan na iya kasancewa a matakai daban-daban.

  9. DR Congo ta sallami mara lafiya na ƙarshe da ke ɗauke da cutar Ebola

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An sallami mara lafiya na karshe da ke ɗauke da cutar Ebola daga asibit da ke Bulape a lardin Kasai na kudu-tsakiya na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo jiya, a wani mataki na yaƙi da ɓarkewar cutar, kamar yadda gidan jaridar Actualite.cd ya ruwaito.

    Wannan zai saka Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana a hukumance cewa cutar ta ƙare a ƙasar muddin babu sabon lamari da aka tabbatar a wannan lokaci.

    “Warkarwar marar lafiya na karshe, bayan makonni shida da bayyana barkewar cutar da aƙalla mutum 64 ne suk kamu da cutar babban abin alfahari ne,” in ji Dr Mohamed Janabi, daraktan WHO na yankin Afirka.

    An kafa cibiyar jinya ta Ebola da ke ɗauke da gado 32 da ƙwararrun masu kula ta musamman, sannan sama da mutane 35,000 sun samu rigakafin cutar bisa tsarin WHO.

    Akalla marasa lafiya 19 sun warke, kuma babu sabon lamari da aka samu tun ranar 25 ga Satumba.

  10. Sojojin Najeriya sun mutu wajen ƙoƙarin daƙile harin Boko Haram a Borno

    ...

    Asalin hoton, Defence HQ/X

    Rundunar sojojin Najeriya ta ce wasu dakarunta sun rasa rayukansu wajen ƙoƙarin daƙile wani mummunan harin da mayaƙan Boko Haram suka shirya kai wa a yankin Kashimri, cikin ƙaramar hukumar Bama, jihar Borno.

    Harin, wanda aka yi ƙoƙarin kai wa a ranar 17 ga Oktoba 2025, rundunar ta ce sojojinta karkashin Operation Hadin Kai su samu nasarar daƙile shi bayan da suka gano kuma suka lalata sansanonin ’yan bindigan da ke yankin.

    A cikin sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X, kakakin rundunar, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ta bayyana cewa sojojin sun fafata da ƴan bingidar inda suka kashe da dama daga cikinsu, wasu kuma suka jikkata.

    "Duk da nasarar da aka samu, kwamandan rundunar 202, Laftanar Kanal Aliyu Saidu Paiko, da wasu dakarun sojin sun rasa rayukansu a yayin fafatawar." in ji sanarwar.

    Sanarwar ta kuma ce "Waɗannan sojojin sun sadaukar da rayukansu ne don tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasar, kuma rundunar za ta ci gaba da girmama tarihin jarumtar su."

    Rundunar ta bayyana cewa "Mutuwar waɗannan jami'an ta sake tunatar da ita muhimmancin ci gaba da yaki da ta’addanci har sai an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya baki ɗaya."

    Babban hafsan sojan ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu.

    Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen murkushe duk wani abu da ya shafi ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da ƙasar baki ɗaya.

  11. Hare-haren sojojin Sudan sun kashe fararen hula bakwai a Darfur

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Sudan ta kai hare-hare da jiragen yaƙi marasa matuƙa a yankunan da dakarun RSF ke iko da su a Darfur ta Arewa da ta Yamma, inda fararen hula aƙalla bakwai suka rasa rayukansu kamar yadda gidan jaridar Sudan Tribune da ke Faransa ta ruwaito.

    Wasu majiya da ke Saraf Omra a Darfur ta Arewa sun ce harin ya afkawa babban kasuwar garin, inda ya kuma taɓa tashar mai da yankin masana’antu tare da lalata motocin yaƙin RSF da dama.

    Rahotannin cikin gida sun nuna cewa RSF na tattara dakaru a Saraf Omra domin kai hare-hare kan yankunan da sojojin gwamnatin ƙasar ke iko da su a Darfur ta Arewa.

    Waɗannan hare-hare sun biyo bayan artabun da ya ɓarke tsakanin RSF da dakarun da ke goyon bayan gwamnati a garin Abu Gamra, inda harin RSF ya tilastawa mazauna garin tserewa zuwa ƙasar Chadi.

  12. Yaƙi da rashin tsaro nauyi ne na kowa da kowa - Gwamnan Zamfara

    ...

    Asalin hoton, Dauda Lawal/Instagram

    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa yaƙi da matsalar tsaro a jihar haƙƙi ne na kowa da kowa ma'ana haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da kuma mutanen jihar.

    Wannan furucin ya biyo bayan taron majalisar zartarwa na 18 da gwamnan ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Litinin.

    A taron, an tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da tsaro da ilimi da lafiya da ci gaban ababen more rayuwa

    Gwamna a jawabinsa na buɗe taron ya ce: “Ina so in tunatar da mu duka game da hakkinmu na haɗin gwiwa a wannan gwamnatin wajen yaki da rashin tsaro.”

    Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta samu ci gaba wajen dawo da zaman lafiya a mafi yawan sassan jihar.

    Ya ce, “Hare-haren ƴan fashi da makami ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.”

    Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin kwamitin da su kasance masu himma sannan su rika gabatar da rahotannin aiki ga kwamishinan saro a kai a kai. Ya kuma roƙi a yi addu’a ga rayukan duka jaruman da suka rasu.

  13. Mutum biyu sun mutu bayan jirgin kaya ya faɗa cikin teku a Hong Kong

    ...

    Mutane biyu daga ma’aikatan tsaro na filin jirgin saman Hong Kong sun mutu bayan jirgin dakon kaya ya fita daga hanyar saukar jirgi, ya buge motar sintirinsu, sannan ya fada cikin teku.

    Jirgin Emirates EK9788, daga Dubai ya kauce daga hanyar saukar jirgi inda ya karya shinge, sannan ya buge motar sintiri yana tura ta cikin ruwa.

    Mutanen biyu da ke cikin motar sun mutu, yayin da jirgin Boeing 747 ya tsaya rabi cikin ruwa, amma ma’aikatan jirgin guda hudu sun tsira da ransu.

    Hukumomi sun fara bincike kan musabbabin hatsarin da ya auku a hanyar saukar jirgi ta arewacin ƙasar.

    Sauran hanyoyin saukar jirgi guda biyu suna ci gaba da aiki.

    Wannan na ɗaya daga cikin mummunan haɗuran jirgin sama a cikin ‘yan shekarun nan a filin jirgin saman Hong Kong.

    Hukumomin filin jirgin sun ce sun ba jirgin umarnin da ya dace, kuma akwai alamomi a kan hanyar saukar jirgin don jagorantar jiragen sama.

  14. China na gudanar da taron manyan shugabannin ƙasar a Beijing

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan shugabannin China, sun fara wani taro na yini huɗu a birnin Beijing, domin yanke shawara kan muhimman manufofi da burukan da za a sanya a gaba na ƙarashen shekaru goma masu zuwa.

    Ana sa ran babbar jam'iyar kwaminisanci da ke mulkin ƙasar za ta tunkari batutuwa da dama, kamar tabarbarewar tattalin arziki da rikicin kasuwanci da Amurka.

    Abin da taron zai yanke shawara a kai ne zai zamo daftarin ciyar da kasar gaba da za a yi amfani da shi har nan da shekarar dubu biyu da talatin.

  15. An tarwatsa masu zanga-zangar neman sakin Nnamdi Kanu a Abuja

    ...

    Jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar neman sakin shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, a Abuja a ranar Litinin ta hanyar amfani da hayaƙi mai sa hawaye lamarin da ya sa masu zanga-zangar suka gudu.

    Ɗan gwagwarmayan kare hakkin dan'adam, Omoyole Sowore ne ya jagoranci zanga-zangar duk da umarnin kotu da gargadin ‘yan sanda.

    An dai girke jami'an tsaro a wasu manyan hanyoyi da muhimman wurare a Abuja, babban birnin Najeriya saboda zanga-zangar.

    Masu zanga-zangar dai sun ce niyyarsu ita ce su yi tattaki zuwa fadar Shugaba Tinubu da sauran muhimman cibiyoyin mulki.

    Jami'an tsaro ciki har da 'yan sanda da sojoji da sauransu suka kafa shingayen bincike a kan tituna musamman wadanda suka nufi fadar Aso Rock.

    ...
  16. Kano, Katsina da Jigawa sun shiga yarjejeniyar bunƙasa lantarki

    ...

    Asalin hoton, Facebook/Gaddafi Sani Shehu

    Gwamnonin Kano da Katsina da kuma Jigawa sun shiga yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa kasuwar wutar lantarkin jihohin uku tare da zuba hannun jari a kamfanin Future Energies Africa (FEA), babban mai zuba jari a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano wato KEDCO.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan Wutar Lantarki da Makamashi na jihar Kano, Dr. Gaddafi Sani Shehu ya fitar.

    Sanarwar ta ce an cimma wannan yarjejeniyar ne yayin wani taro kan bunƙasa lantarki da aka gudanar a birnin Marrakech, Morocco, daga ranar 16 zuwa 19 ga Oktoba, 2025.

    Dr. Gaddafi ya ce jihohin uku za su yi aiki tare wajen gano hanyoyin da za su amfanar da kasuwannin wutar lantarkinsu, tare da kafa tsare-tsaren doka da hadin gwiwa domin inganta aiki.

    Ya kara da cewa "samun hannun jari a kamfanin FEA zai taimaka wajen karfafa dabarun KEDCO da kuma haɓaka rarraba wutar lantarki a yankin Arewacin Yamma."

    Kwamishinan ya bayyana cewa "za su kashe naira biliyan 50 wajen bunƙasa lantarkin da hanzarta samar da wuta ga al’umma ta hanyoyi da dama kamar samar da wuta a gida da tsarin hasken rana da sauransu."

    "Haka zalika, za a yi aiki tare da KEDCO domin rage asarar wutar lantarki daga masu amfani da lantarkin a gida, wanda zai tabbatar da ingantaccen samar da wuta ga al’umma."

    An tsara cewa wakilan jihohin za su gudanar da taron kasa da kasa a kowace shekara, sannan su gana sau huɗu a shekara domin duba ci gaban ayyuka da tsara manufofi da karfafa dangantaka a kasuwar wutar lantarki ta jihohi uku.

  17. Rodrigo Paz ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Bolivia

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Kotun zaɓe a Bolivia, ta sanar da dan takara mai ra'ayin ciyar da harkokin kasuwanci gaba Rodrigo Paz, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

    Ya doke mutumin da ke mara masa baya Jorge Quiroga na jama'iyyar masu ra'ayin rikau a zaben kasar na farko da ya kai ga zuwa zagaye na biyu.

    Yayin wani jawabi da ya gabatar, Mista Paz wanda dan majalisar dattawa ne, ya godewa magoya bayansa.

    Ya ce "Sakamakon wannan nasara tamu ta yau, muna mika gayyatarmu ga dukkan al'ummar wannan kasa da ke son ciyar da ita gaba, don mu yi aiki tare."

    A yanzu dole ne Paz ya tashi tsaye wajen magance matsalar tattalin arziki da ƙasar ke fama da shi.

    Bolivia na cikin matsanancin hauhawar farashin kayan masarufi ga kuma dumbin bashin da ke kanta.

  18. Tchiroma Bakary ya fara wallafa sakamakon zaɓe a Kamaru

    ...

    Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty Images

    Dan takarar jam'iyyar adawar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya fara fitar da sakamakon zaɓe daga wasu yankuna na ƙasar domin kare iƙirarin da yake yi na cewa ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 12 ga Oktoba.

    Tchiroma, mai shekaru 76, ya wallafa takardun sakamakon a shafukan sada zumunta a ranar Lahadi, inda ya yi iƙirarin cewa ya yi nasara a manyan yankuna 18 daga cikin yankuna 58 na ƙasar, waɗanda a cewarsa suna wakiltar kusan kashi 80 cikin 100 na masu zaɓe.

    Ya ce, “Da nasarar da muka samu a waɗannan yankuna 18, tabbas mun yi nasara a ƙasa baki ɗaya, domin nauyin zaɓe na yankunan nan shi ke ƙayyade sakamakon ƙarshe.”

    Sai dai jam’iyyar mai mulki ta CPDM ƙarƙashin shugaba Paul Biya ta yi watsi da iƙirarin, tana mai cewa ba gaskiya ba ne cewa kaso 80 na masu zaɓe suna cikin waɗannan yankuna 18.

    Jam'iyyar CPDM ta ce “Ya kamata a bi ytadda doka ta tanada kafin a bayyana sakamakon ƙarshe.”

    Tchiroma ya kuma kira al’ummar Kamaru da su “kare nasarar su”, yana mai tabbatar musu da cewa zai ci gaba da tsaya musu.

    A makon da ya gabata ne wasu masu zanga-zanga suka fito kan tituna suna nuna ɓacin rai kan abin da suka kira maguɗin zaɓe, inda suka ƙone gine-gine da lalata hotunan yaƙin neman zaɓen shugaba Biya.

  19. 'Har yanzu wajibi ne ɗalibai su haɗa da lissafi a jarrabawarsu ta sakandire'

    ...

    Asalin hoton, KANO STATE GOCT/FACEBOOK

    Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa har yanzu wajibi ne ɗalibai su haɗa da darasin Lissafi a jarabawarsu ta kammala makarantar Sakandire (SSCE), duk da sauye-sauyen da aka yi a tsarin karɓar ɗalibai jami’a.

    A makon da ya gabata ne ma'aikatar Ilimin ƙasar ta bayyana sabon tsari da ta janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin malamai da ɗalibai a faɗin ƙasar, inda ta sanar da cewa ba za a sake wajabta wa ɗaliban sakandire da ke neman karatu a fannin da ba na kimmiya ba cin darasin lissafi kafin samun gurbin karatu a jami'a ko kwalejin fasaha ba.

    Sai dai mai magana da yawun ma’aikatar, Boriowo Folasade, ta bayyana cewa wannan ba yana nufin ɗalibai ba za su yi darasin Lissafi a jarabawarsu ta kammala sakandire ba wato WAEC.

    A cewarta, duk ɗalibai dole ne su yi rajista da rubuta jarabawar Turanci da Lissafi, domin waɗannan darussa su ne muhimman ginshiƙin ilimi da sadarwa, da tunani mai zurfi.

    Ta ce "Sabon tsarin karɓar ɗalibai ya fi mai da hankali ne wajen sassauta sharuɗɗan shiga jami’a, amma hakan bai shafi wajabcin yin waɗannan darussa ba."

    'Wannan sabon tsari yana bin ka’idojin ilimi na ƙasashen duniya, kuma manufarsa ita ce tabbatar da cewa ba za a hana ɗalibai masu ƙwazo da cancanta samun ilimi ba saboda ƙarancin maki a darussa da ba su da alaƙa kai tsaye da fannin da suka zaɓa." in ji Folasade.

    Ta kuma jaddada cewa Turanci da Lissafi za su ci gaba da kasancewa muhimman darrusa a sassan tsarin ilimi a Najeriya, domin su ne ginshiƙi wajen fahimta sadarwa, da koyon rayuwa.

  20. Ana jayayya kan zanga-zangar neman a sako Nnamdi Kanu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Waɗanda suka shirya zanga-zangar neman a sako jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu da ake zargi da cin amanar kasa sun sha alwashin ci gaba da shirin su duk da gargaɗin da hukumomi suka yi.

    Masu shirin zanga-zangar sun sha alwashin gudanar da ita duk da umarnin da wata babbar kotun tarayya ta bayar, wanda ya haramta masu yin zanga-zangar a sassan babban birnin Najeriya, Abuja.

    Sun tsara gudanar da zanga-zangar ta su ne a ranar Litinin 20 ga watan Oktoban 2025, domin neman gwamnati ta sako jagoran ƙungiyar IPOB mai fafutukar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, wanda ake tsare da shi tun a 2021, lokacin da jami'an tsaro suka kama shi a Kenya suka kuma mayar da shi Najeriya domin fuskantar tuhuma a kan ayyukan ta'addanci.