Ƴansandan ƙasa da ƙasa ne mana tsohon ministan kuɗin Ghana
Hukumar Ƴansandan ƙasa da ƙasa ta ayyana tsohon ministan kuɗin Ghana, Ken Ofori-Atta a matsayin wanda take nema ruwa a jallo saboda zarge-zargen cin hanci.
A farkon wannan wata ne masu shigar da ƙara a Ghana suka ayyana nemansa ruwa a jallo saboda yunƙurin tsere wa sharia'
Zarge-zargen sun haɗa da almundahar sayen kayyaki da za a gina babbar kocin ƙasa a birnin Accra, da ta janye ce-ce-ku-ce.
Har yanzu dai ginin ba inda ya je, duk kuwa da laƙume fiye da dala miliyan 50 daga asusun gwamnati.
Mista Ofori-Atta, wanda rahotonni suka ce ya fice daga ƙasar domin neman lafiya, bai ce komai ba game da batun.
A baya dai ya yi ƙorafin rashin y masa shari'a bisa adalci
Gwamnan jihar Akwa Ibom ya fice daga PDP zuwa APC
Asalin hoton, Umo Eno/X
Bayanan hoto, Umo Eno ya kasance gwamnan PDP na biyu da ya koma APC cikin ƙasa da wata biyu
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya bayayna ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da komawa APC, mai mulkin Najeriya.
Cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a, Mista Eno ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar abokan shawararsa.
“Kan haka ne na ɗauki matakin fita daga PDP tare da komawa jam'iyyar APC'', kamar yadda gwamnan ya bayyana.
Gwamnan ya ce ya koma APC ne domin ƙarfafa jam'iyyar.
“Ba mu shiga jam'iyyar daga ɓangaren masu gazawa ba, mun shiga ne domin ƙarfafa jam'iyyar,” in ji shi.
Mista Eno ya ce ya koma APC ne domin taimaka wa sauye-sauyen tattalin arziki na shugaban Najeriya Bola Tinubu.
Ficewar Eno daga PDP na zuwa ne ƙasa da wata biyu bayan gwamnan Delta Sheriff Oborevwori, ya fice daga jam'iyyar adawar ta PDP zuwa APC
'Dakarun Wagner za su fice daga Mali'
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar sojojin hayar Rasha ta Wagner ta ce za ta fice daga Mali bayan shafe shekara uku da rabi tana yaƙi da masu iƙirarin jihadi.
Cikin wani saƙo da kungiyar ta wallafa a shafinta na Telegram ta ce ta samu nasarar kammala ayyukanta a ƙasar.
Hare-haren masu iƙirarin jihadi sun ƙaru a wannan watan, yayin da rahotonni hare-haren mayaƙan sun kashe gomman sojojin Mali da mayaƙan Wagner.
Bayan juyin mulkin da aka samu a 2020 da 2021 hukumomin mulkin sojin ƙasar sun kori dakarun Faransa daga ƙasar tare da gayyato mayaƙan Wagner.
To sai dai wata ƙungiyar jami'an tsaron mai samun goyon bayan gwamnatin Rasha, mai suna ''Dakarun Afirka'', za ta bar wasu sojojinta a Malin, waɗanda tuni suke ƙasashen Nijar da Burkina Faso.
'Gobara ta laƙume shaguna kusan 300 a kasuwar waya da ke Kano'
Asalin hoton, TWITTER/@GBOYEGAKOSILE
Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar sayar da wayoyi da ke birnin Kano ta haifar da ɗimbin asarar dukiya.
Shugaban kasuwar Amb. Jamilu Bala Gama ya shaida wa BBC cewa gobarar ta kwashe sa'o'i shida zuwa bakwai tana ci.
Ya ƙara da cewa gobarar ta shafi shaguna fiye da 300 a kasuwar, inda ta fi ƙamari a ɓangare masu sayar da wayoyin da kayan gyaran wayoyin.
''An yi ƙazamar asara ta dukiya da kadara, a shago guda za ka iya samun naira miliyan 500, wani ma har biliyan guda , kuma duka sun ƙone'', in ji shi.
Shugaban kasuwar ya ƙiyarta asarar da aka yi a gobarar da cewa ta kusa naira biliyan 100.
Kawo yanzu dai ba a san musababbanin tashin gobarar ba, kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Gobara ta jima tana haifar da mummunar asara ga ƴan kasuwa a Najeriya, wani abu da masana ke alaƙanta shi da rashin bin tsari a wasu lokutan.
Isra'ila ta kai wa Hezbollah hari a jajiberin Sallah
Isra'ila ta ƙaddamar da wasu hare-hare a kudancin Beirut da ke Lebanon bisa cewar tana neman wurin da Hezbollah ke ƙera jirage maras matuƙa.
Harin da aka kai shi ranar Alhamis ana jajiberin ranar Sallah ya biyo bayan gargaɗin da Isra'ilar ta yi na jama'a su bar yankin da Hezbollah take da ƙarfi a birnin ƙasar.
Dakarun Isra'ila sun ce sun gano wani wuri da hezbollah ke ƙera jirage maras matuƙa masu yawa a ƙarƙashin ƙasa da Iran ke marawa baya.
Harin dai na ci gaba duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Isra'ilar da Hezbollah watanni shida da suka gabata.
Tuni rundunar sojin ƙasar Lebanon ta ce za ta zare hannunta daga yarjejeniyar aikin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra'ilar da Hezbollah.
WHO ta yi kira a kare asibitoci a Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kira da a gaggauta samar da tsaro ga asibitoci biyu da suka rage a Gaza.
WHO ta ce a halin da ake ciki, babu asibitin da ke aiki a arewacin Gaza sannan asibitocin Nasser da Al-Amal da ke kudancin zirin suna cikin haɗari saboda takunkumin da aka sa kan shigar da kayan jin ƙai.
Asibitocin biyu sun kasance a wajen wani yanki da Isra'ila ta ayyana a matsayin tudun mun tsira a yankin Khan Younis - inda galibin Falasɗinawa a yanzu suke zaune.
WHO dai na fargabar nan ba da daɗewa ba za a hana agaji isa inda suke.
Tinubu ya yi Sallah a Legas, Shettima a Abuja
Asalin hoton, Bayo/Facebook
Bayanan hoto, Shugaba Tinubu da muƙarrabansa a masallaci Idi da ke Legas.
Asalin hoton, Bayo/Facebook
Bayanan hoto, Shugaba Tinubu na sallah tare da muƙarraban gwamnatinsa a masallacin Idi a Legas.
Asalin hoton, Bayo/Facebook
Bayanan hoto, Kashim Shettima da muƙarrabansa a lokacin da suke sauraron huɗuba a masallacin Idin Abuja
Bukuwan Sallah a Najeriya - Kano da Legas
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wata yarinya tasha gilashi ɗauke da darduma da carbi bayan sakkowa daga sallar Idi a birnin Kano.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ƴanmata da ke murnar bikin sallah babba bayan sakkowa daga sallar Idi a birnin Kano.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu ƴan mata ke murnar bikin sallah bayan sakkowa daga Idi a birnin Kano
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sahun ɗaruruwan Musulmi da ke sallar Idi a filin Idi da ke unguwar Ikeja a birnin Legas.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu yara da ke murnar sallar bayan kammala huɗuba a masallacin da ake Ikeja Legas.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani ɓangaren masallata a Ikeja birnin Legas ke ɗaga hannaye a lokacin yin addu'o'i
Mene ne hukuncin yin sallar Juma'a ranar Idi?
Asalin hoton, BBC/GRAB
Sallar Idin babbar salla ta bana ta dace da ranar Juma'a ta 10 ga watan Zhul Hajji, wani abu da ke janyo kace-nace dangane da yin ɗaya a bar ɗaya ko kuma haɗa su duka biyun.
BBC ta tattauna da wasu malaman addinin Musulunci guda biyu, Sheikh Ahmad Gumi da Sheikh Halliru Maraya a kwanakin baya domin jin fatawoyin malamai a kan haka.
Kuma malaman sun ce addinin Musulunci tuni ya yi tanadi game da haɗa waɗannan ibadun biyu.
Hajj 2025: Mahajjata na ci gaba da gudanar da aikin Hajji
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Tuni mahajjata suka fara yin ɗawafi bayan kammala jifan Shaiɗan na ranar farko.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu mahajjata na aski da saisaye bayan kammala jifan ranar farko da Ɗawafi da Sa'ayi.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu alhazai na addu'a bayan kammala Ɗawafi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Dandazon mahajjata da ke Sa'ayi bayan yin Ɗawafi.
Hajj 2025: Yadda mahajjata ke gudanar da aikin hajjin bana
Tun bayan barin filin Arfa da yammacin ranar Alhamis inda zuka kwana a filin Muzɗalifa sannan kuma tun safiyar yau suka nufi Jamra domin gudanar da jifan Shaiɗan a ranar farko.
Daga nan kuma wasu ke koma wa tantunansu a Mina, inda wasu kuma ke wucewa zuwa Makka domin yin ɗawafi da Sa'ayi daga nan kuma sai su yi yanka da aski su kuma tuɓe harami.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Nan ma mahajjata ne ke jifan Shaiɗan a ranar farko daga cikin kwanaki uku da mahajjatan za su yi a jerin ayyukan aikin hajji.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Nan wani mahajjaci ne ke tsintar ƙananan duwatsu domin jifan Shaiɗan.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yadda mahajjata suke zuwa Jamra ta farko domin jifan Shaiɗan a ranar farko.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Nan wani Alhaji ne yake jifan Jamra da ake kira jifan Shaiɗan a ci gaba da gudanar da ayyukan Hajjin bana.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Dandazon Mahajjata maza da mata ke jifan Shaiɗan bayan baro Muzɗalifa.
Hajj 2025: Yadda ake yin aikin Hajji
Asalin hoton, Getty Images
Aikin Hajji, daya ne daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da ake wajabta wa Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.
Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga Zul Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan.
A wannan shekarar kimanin mutum miliyan biyu ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya, wanda shi ne taro mafi girma a duniya.
BBC ta yi bincike tare da tattauna da malaman addinin Musulunci a shekarun baya dangane da yadda ya kamata mahajjata su gudanar da aikin Hajji kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Karanta cikakken labarin da muka rubuta bisa fatawar malamai dangane da aikin hajji a nan
Amurka ta ƙara sanya wa alƙalan kotun duniya takunkumi
Asalin hoton, Getty Images
Amurka na ci gaba da sanya takunkumi a kan ma'aikatan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC- saboda abin da ta kira ayyukan kotun da suka saba doka a kan Amurka da Isra'ila.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, shi ne ya sanar da sanya takunkumin a kan masu shari'a na kotun su hudu a ranar Alhamis.
Biyu daga cikin wadannan masu shari'a na kotun hukunta manyan laifukan ta duniya da ke birnin Hague sun bayar da sammacvin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da tsohon babban hafsansa na tsaro Yoav Gallant, haka kuma masu shari'ar biyu sun bayar da umarnin kotun ta gudanar da bincike kan zargin keta haddi da sojojin Amurka suka yi a Afghanistan.
A sanarwar ta Amurka Sakataren harkokin wajen kasar - Marco Rubio ya ce, ''wadannan mutane hudu sun kasance kai da fata a haramtattun ayyukan ICC da kuma matakai marassa tushe a kan Amurka da shakikiyar kawarta Isra'ila.''
Babban attajirin nan na duniya wanda kuma a baya-bayan ya ɓaɓe da Shugaba Trump, bayan ya kasance kusa a gwamnatin - Elon Musk, ya tsaya kan matsayinsa na neman a tsige shugaban daga mulki.
Sai dai ya janye barazanar da ya yi ta ficewa daga wani muhimmin shirin Amurka na sararin samaniya.
Hamshakin attajirin ya sauya shawara ne 'yan sa'o'i bayan ya ce zai soke aikin kumbon zuwa sararin samaniya da ya yi wa lakabi da SpaceX Dragon.
Wannan rigima ta barke ne har ta kai aka ga tsofaffin shakikan biyu a rana – bayan hamshakin attajirin wanda mako daya baya yake zaman lamba daya da kusan ba kamarshi a gwamnatin ta Trump, bayan ya soki shugaban kasar kan sababbin dokokinsa kan haraji, da kuma kudurin dokar gwamnatin na kashe kudade.
Cikin wani saƙo da hamshaƙin attajirin ya wallafa a shafinsa na X, ya yi wa Trump gori da cewa ba don taimakonsa ba da Trump din ya fadi zaɓen shugaban ƙasar.
Ina kira ga ƴan Najeriya da ku ƙara haƙuri - Tinubu
Asalin hoton, Onanuga/X
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ja hankalin ƴan Najeriya da ka da su yanke ƙauna da gwamnatinsa, inda ya ƙara da cewa abubuwan kyautata rayuwarsu na nan tafe ba da jimawa ba.
Tinubu wanda ya yi wannan kiran a saƙonsa na taya Musulmi murnar babbar sallah, ya ce duk da dai tafiyar ba ta rasa kun-kunji amma ya kamata jama'ar Najeriya su ƙara haƙuri.
"Ba lallai mun samu abin da muka so ba amma ina kira ga ƴan Najeriya da ka da su yanke ƙauna. Mu ci gaba da fata mai kyau sannan kuma mu jure. Sauye-sauyenmu da muke son yi na samun haɓaka musamman bisa dogaro da alƙaluman tattalin arziƙi da ke nuna ci gaba. Nan ba da jimawa ba kowa zai kurɓi romon."
Daga ƙarshe shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan ƙasar su yi wa al'ummar garin Mokwa addu'a sakamakon ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita al'ummar garin bayan kashe mutum kimanin 700.
Yadda aka gudanar da Sallar Idi a masallacin Katampe da ke Abuja
Bayanan hoto, Limami yayin da yake huɗuba bayan kammala sallar Iid
Bayanan hoto, Masallata na sauraron huɗuba
Bayanan hoto, Wasu Masallata na sauraron huɗuba
Bayanan hoto, Masallata na sauraron huɗuba
Budewa
Masu bibyarmu barkan ku da Sallah. Da fatan an sallata lafiya. Allah ya maimaita mana ta baɗin baɗaɗa.
Kamar kullum yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye daga Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Ka da ku manta za ku samu bayanan da kuke neman dangane da halin da mahajjata ke ciki a ƙasar Saudiyya. Mun gode