Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 29/04/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail da Ahmad Bawage

  1. Bam ya kashe mutum 26 a jihar Borno

    Fashewar

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa aƙalla mutum 26 ne suka rasu ranar Litinin sakamakon tashin wani bam da motar da suke ciki ta taka a kan hanyar da ke tsakanin garin Rann zuwa Gmaboru Ngala.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa mutanen da abin ya rutsa da su sun haɗa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.

    Bam ɗin da ake zaton ƙungiyar Boko Haram ce ta dasa binne shi, ya kuma jikkata aƙalla mutum da dama waɗanda suke asibiti domin samun kulawa.

    Duk da cewa al'ummar yankin sun ɗora laifin kan ƙungiyar Boko Haram amma har kawo yanzu hukumomin tsaro ba su ce uffan ba.

  2. Kotu ta yi watsi da buƙatar Emefiele kan dawo masa da gidajen da EFCC ta ƙwace

    Rukunin gidajen Emefiele

    Asalin hoton, EFCC

    Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ta neman a dawo masa da rukunin gidajen da gwamnati ta ƙwace.

    A ranar 2 ga watan Disamba ne hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta samu amincewar kotu domin ƙwace unguwa guda mallakar Mista Emefiele da ke Abuja babban birnin ƙasar.

    Unguwar da ke yankin Lokogoma ta ƙunshi gidaje 753.

    Tsohon gwamnan ya nemi kotun ta ƙara masa lokaci domin gabatar da buƙatar neman jingine umarnin da ta bayar na ƙwace rukunin gidajen a watan Disamban 2024.

    Ya yi iƙirarin cewa bai san lokacin da kotun ta yanke hukuncin ƙwace gidajen ba, sannan ya zargi EFCC da wallafa sanarwar neman mamallakin gidajen a wani "ɓoyayyen sashe na shafin jarida ta yadda zai yi wahala ya iya rubuta martani a kan lokaci".

    Sai dai Mai Shari'a Jude Onwuegbuzie ya yi watsi da iƙirarin nasa, yana mai cewa sanarwar da aka wallafa a rabin shafin jarida ta ƙasa ya wadatar.

  3. Har yanzu mutane na cikin duhu a Sifaniya da Portugal

    Sifaniya

    Asalin hoton, Reuters

    Injiniyoyi sun duƙufa cikin dare domin dawo da wutar lantarki a cibiyoyin sadarwa a Sifaniya da Portugal bayan da aka samu katsewarta a a kasashen biyu ranar Litinin.

    Babban jami'in ma'aikatar lantarki a Sifaniya ya ce zuwa yanzu an mayar da wutar a kashi 90 cikin 100 na biranen ƙasar, amma da maraice mutane da yawa sun ci gaba da yin amfani da kyandira da fitulu domin samun haske a gidajensu.

    Wakilin BBC ya ce tituna da dama sun fada cikin duhu, inda za ka ga jami'ai na nuna wa mutane inda za su bi saboda fitulun kan hanya sun dauke.

    Sannan hatta wuraren cin abinci, da na shan barasa sun rufe da wuri.

    A Pourtugal kuwa, kamfanin rarraba hasken lantarki na kasar ya ce ana dawo da wutar sannu a hankali.

  4. Assalamu Alaikum

    Yau Talata ma za mu kawo muku rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Shafin zai fi mayar da hankali kan Najeriya da Nijar da maƙwabtansu tare da ni Umar Mikail bisa sa'idon Usman Minjibir.

    Ku biyo mu.