Sai da safenku
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 29/04/2025.
Usman Minjibir, Umar Mikail da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na da jan aiki a gabanta bayan rashin nasara a hannun Paris St-Germain da ci 1-0 a zagayen farko na wasan daf da karshe na gasar Zakarun Turai.
Ousmane Dembele ne ya ci wa PSG kwallo ɗaya tilo a wasan a minti huɗu da take wasa a gidan Arsenal na Emirates.
PSG ta mamayi wasan a farko, inda ta yi ta kai wa Arsenal hare-hare ba ƙaƙƙautawa - inda Davida Raya ya yi ta buge kwallaye da suke kai wa har ta kai aka tashi 1-0.
Yanzu dai Arsenal na da babban aiki a gabanta a mako mai zuwa - lokacin da za ta ziyarci gidan PSG da nufin yin bajinta na ganin ta doke ƙungiyar ta Faransa don kai wa wasan karshe na Champions League.

Firaiministan Canada Mark Carney ya ce ƙasarsa ta cancanci mutuntawa daga Amurka kuma za ta shiga tattaunawar kasuwanci da tsaro ne kawai a bisa sharuɗan da ta gindaya.
Yana magana ne da BBC kafin jam'iyyarsa ta Liberal ta lashe zaɓen Canada - duk da cewa ba lalle sune suke da gagarumin rinjaye a majalisar dokoki ba.
Batun yaƙin kasuwanci da Amurka da barazanar Trump na mayar da Canada ƙarƙashin ikon Amurka sune batutuwan da suka kankane zukatan mutane a lokacin zaɓen.
Katsalandan ɗin Trump ya yi tasiri a yadda masu zaɓe suka kaɗa ƙuri'a.
Mista Carney ya ce zai kai ziyara Washington ne kawai idan akwai wata muhimmiyar tattaunawa da ta girmama ƴancin ƙasarsa.
Babban abokin hamayyarsa, Piyer Poliyever ya rasa kujerarsa duk da cewa jam'iyyar Conservatives ta taka rawar gani a zaɓen.

Asalin hoton, EPA
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta koyi darasi daga katsewar lantarkin da ta faru bagatatan a Sifaniya da Portugal.
Mai magana da yawun hukumar Turai ta ce Brussels za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da masu kula da babban layin lantarki domin gano musabbabin ɗaukewar wutar tare da tabbatar da cewa EU ta shirya tunkarar irin haka a gaba.
Masu kula da babban layin lantarki a Sifaniya sun ce ba kutsen intanet ba ne ya janyo ɗaukewar wutar, sai dai Firaiminista Pedro Sanchez ya ƙi amincewa da duk wani abu da ka iya zama sababin matsalar.

Asalin hoton, Getty Images
PSG ta zura wa Arsenal kwallo ɗaya a raga a wasan daf da karshe na gasar Zakarun Turai.
Ɗan wasan PSG Ousmane Dembele ne ya zura kwallo a ragar Arsenal a minti na huɗu da fara wasa.
Wasan wanda ake fafatawa a gidan Arsenal na Emirates, ya cika makil da ƴan kallo.

Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin gudanarwar babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya PDP, ya ce ko a jikinsa kan ficewar da mambobinsa ke ci gaba da yi zuwa APC mai mulki.
Jam’iyyar ta kuma ce a shirye ta ke domin ganin ta samu nasara a babban zaɓen ƙasar na 2027 mai zuwa.
PDP ta bayyana haka ne a wani babban taro da ta gudanar yau Talata a Abuja - inda ta ce ƴan Najeriya sun gaji da halin da gwamnatin APC ta jefa su ciki.
Hakan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ta ke fuskantar rikicin cikin gida, wanda ya ɗauki tsawon lokaci ba tare da ta warware shi ba.
Shugaban riko na jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Iliya Damagun ya shaida wa BBC cewa sun yi Alla-wadai da waɗanda ke ficewa daga jam'iyyar.
"Sun ce abin da ya sa suka fita daga PDP shi ne suna neman shugaban ƙasa ya taimaki shiyyoyinsu. Na ga kuskure a wannan al'amari, saboda mutumin da kowa na kuka da shi yaushe za ka kai kuka gida mutuwa," in ji Damagun.
Ya ce za su bi matakin shari'a wajen karɓe kujerunsu da wadanda suka fice ɗin suka tafi da su.
kazalika, tururuwar zuwa APC da 'yan jam’iyyar ta PDP ke yi, ya sa jama’a da dama na kallon hakan zai iya ƙara jefa manyan jam'iyyun da ke da ƙarfin ƙalubalantar shugaba Tinubu a zaɓen 2027 cikin hali maras tabbas.
Sai dai Damagun ya ce hakan ba zai ba su tsoro ba, domin kuwa masu sauya sheƙar na daukar matakin ne daidai lokacin da al'umma suka gaji da irin salon mulkin gwamnatin.
A baya-bayan nan an samu gaggan ƴan jam’iyyar ta PDP da suka sauya sheka zuwa APC ciki har da gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori da duka Ƴan majalisar jihar, sai kuma Ɗan majalisar dattijai daga jihar Kano, Sanata Adulrahman Kawu Sumaila na NNPP.

Asalin hoton, PRCS
Ƙungiyar ba da agaji ta Red Crescent a Falasɗinu ta ce rundunar sojin Isra'ila ta saki wani jami'in lafiya da ke tsare tun bayan mummunan harin da Isra'ilar ta kai kan motocin ɗaukan marasa lafiya a kudancin Gaza, makonni biyar da suka gabata.
An tsare Assad Al-Nzazrah yayin wani sumame da sojoji suka kai kusa da Rafah inda dakarun IDF suka kashe ma'aikatan agaji 15.
An shafe makonni ba tare da sanin halin da yake ciki ba.
Dakarun IDF daga bisani sun ɗora alhakin hare-haren da aka kai kan gazawar aiki - iƙirarin da ƙungiyar ta Red Crescent ta yi watsi da shi.
Tun farko Isra'ila ta yi iƙirarin cewa kwambar motocin ta tunkaro sojojinta cikin duhu ba tare da kunna fitilun motocin ba.

Asalin hoton, Nigerian Army/X
Rundunar sojin Najeriya ta naɗa Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar a matsayin sabon kwamandan dakarun Operation Hadin-Kai mai yaƙi da ta'ddanci a arewa maso gabas.
Naɗin nasa na zuwa ne bayan dawowar sabbin hare-hare a yankin a watanni huɗu da suka gabata - waɗanda suka janyo mutuwar fararen hula da dama da kuma sojoji.
Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar, ta ce Janar Abdulsalam shi ne kwamanda na 15 na dakarun Haɗin-Kai da ke yaƙi da Boko Haram da kuma ISWAP a yankin arewa maso gabas.
Abubakar ya riƙe mukamin mataimakin kwamandan kwalejin tsaro da kuma kwamandan wata rundunar tsaro a arewa maso tskakiyar Najeriya.
Boko Haram da takwararta ta ISWAP sun zafafa kai hare-hare a baya-bayan nan a yankin.
Hakan ya janyo fargabar dawowar hare-haren masu iƙirarin jihadin, waɗanda a yanzu ke amfani da jirage marasa matuki da kuma abubuwan fashewa a kan hanyoyi, a cewar wani ƙwararre kan harkar tsaro.
A ranar Talata ne ISWAP ta ɗauki alhakin kisan wasu fararen hula 26 a wani hari a jihar Borno.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, EPA
Shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakin kare durƙushewar muhimman ayyukan tallafa wa al'ummar Gaza.
Volker Turk ya bayyana cewa Isra'ila, tsawon makonni tara kenan, tana toshe hanyoyin shigar da muhimman kayayyakin jin-ƙai zuwa Gaza.
Ya ce ana kashe farar hula a hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kan sansanoni da gidajen da ƴan gudun hijira ke samun mafaka.
Akwai fargabar cewa Isra'ila tana ƙara taɓarɓara yanayin da Falasɗinawa ke ciki, a cewar Mista Turk.
Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ya ce ƙasar ba farar hula take kai wa hari ba illa masu ta'addanci.

Asalin hoton, Getty Images
Hadakar ƙasashen Sahel na AES da suka haɗa da Burkina Faso, Mali da kuma jamhuriyar Nijar na neman shiga tekun Atlantika ta hanyar Maroko.
Ƙasashen sun ce sun ɗauki matakin ne domin bambanta hanyoyin shiga tekun bayan ficewarsu daga kungiyar Ecowas a bara.
Ministocin harkokin wajen ƙasashen ne suka bayyana wannan aniya yayin wata ganawa da Sarkin Maroko Muhamma na shida.
Ministocin sun ce matakin zai ba su damar shiga kasuwanin duniya.
Wannan dai wani ɓangare ne na daɗaɗɗiyar alaƙar Masaurautar da ƙasashen uku.
Sun kuma yi na'am da shirin Sarkin na inganta hanyoyin shiga tekun Atlantika ga ƙasashen Sahel - inda suka nuna goyon bayansu na ganin an gaggauta aiwatar da matakin.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kisan mutum 26 a wani hari da ta kai jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ƙungiyar ta yi wannan iƙirari ne a shafin Telegram.
Lamarin ya faru ne ranar Litinin bayan da wata mota ta taka bam a gefen hanya kusa da iyaka da Kamaru a jihar ta Borno.
Hakan na zuwa ne kimamin mako biyu bayan da wata motar bas ta taka wani abin fashewa da aka binne a yankin, abin da ya janyo mutuwar fasinjoji takwas da kuma raunata wasu 11.
Ƙungiyar Boko Haram da ISWAP sun shafe tsawon shekara 15 suna kai hare-hare da kuma artabu da jami'an tsaron Najeriya a arewa maso gabas.
Sun sha amfani da abubuwan fashewa wajen afkawa fararen hula da kuma jami'an tsaro.

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci mahukunta a Kenya da su fitar da bayanai game da masu zanga-zangar adawa da haraji da aka kashe a Yunin bara.
Ƙungiyar ta nemi martanin hukumomin ne bayan da binciken BBC ya gano wasu jami'an tsaron ƙasar na da hannu a harbe masu zanga-zangar a Nairobi.
Shugaban ƙungiyar Amnesty a Kenya ya ce duk da alƙawuran da gwamnati ta yi, har yanzu ba a hukunta kowa ba game da kisan mutanen.
Ƙungiyar da ke sa ido kan ayyukan ƴansanda a Kenya ta saki wasu bayanai ranar Litinin ɗauke da sunayen mamatan da kuma dalilin rasuwarsu - wasu ta sanadiyyar raunukan da suka ji sakamakon harbin bindiga wasu kuma sakamakon gurɓataccen hayaƙi mai sa hawaye da suka shaƙa.
Aƙalla mutum tara aka bayar da rahoton an kashe sakamakon rikicin ƙabilanci a kusa da Damascus, babban birnin Syria.
Rikicin ya ɓarke ne tsakanin wasu ƴan ƙabilar Druze tsiraru da ke ɗauke da makamai, waɗanda galibinsu suna zaune a unguwar Jaramana da kuma wasu daga yankunan mabiya aƙidar Sunni.
Tashin hankalin ya samo asali ne bayan ɓullar wani bidiyo da a ciki wani ɗan ƙabilar Druze yake aibata addinin musulunci.
Bayanai sun nuna cewa ƴan Sunnin suna da goyon bayan jami'an tsaro sai dai gwamnatin ƙasar ta masu kishin Islama ta ce za ta hukunta duka ɓangarorin biyu.
A cewar wakilin BBC, an ci gaba da jin ƙarar musayar wuta yayin da jagororin ƙabilar ta Druze suka gana da jami'an tsaro domin kare ƙaruwar yaƙin, duka ɓangarorin sun nemi jama'a su kwantar da hankalinsu.

Asalin hoton, PDP
Kwamatin gudanarwa na jam'iyyar adawa ta PDP ya fara taronsa na gaggawa da ya kira a babban ofishin jam'iyyar da ke Abuja.
Kafar yaɗa labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa taron da ke gudana yanzu haka, ana yin sa ne a asirce.
'Yan kwamatin sun kira taron ne domin tattauna ficewar da wasu manyan 'ya'yanta suka yi a kwanan nan da kuma rikicin shugabancin da ta daɗe tana fama da shi ƙarƙashin shugaban riƙo Umar Ilya Damagun.
A makon da ya wuce ne ɗantakarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa, ya koma APC mai mulki tare da gwamnan jiharsa ta Delta Sheriff Oborevwori.
Za mu kawo muku ƙarin bayani kan matsayar da suka ɗauka da zarar mun samu.

Asalin hoton, Reuters
Ministan harkokin cikin gida na Iran ya ce sakaci ne ya jawo gagrumar fashewa da gobara a tashar jirgin ruwa mafi girma ta ƙasar.
Mutanen da suka mutu sakamakon fashewar a ranar Asabar sun kai 70 zuwa yanzu.
Eskandar Momeni ya ce fashewar da ta lalata tashar Shahid Rajaee a yankin Bandar Abbas, ta kuma jikkata wasu 1,000, kuma ta auku ne saboda "kuskure da ya haɗa da ƙin bin tsarin kariya da kuma sakaci".
Ya ƙara da cewa "an gayyaci wasu mutane da ake zargi suna da hannu domin amsa tambayoyi".
Jami'an hjukumar kwastam sun ce wasu kwantenoni ne suka kama da wuta kuma suka fashe.
Ma'aikatar tsaro ta musanta rahotonnin wasu jaridun ƙasar waje cewa mai ne da sinadarai da ake amfani da su wajen haɗa makamai masu linzami suka fashe.
Yayin jawabinsa, Firaministan Sifaniya Pedro Sanchez ya ce fasinjojin jirgin ƙasa sama da 35,000 ne ɗaukewar lantarki ta shafa a jiya Litnin.
Ya ce wurare da ya wa na ƙsar har yanzu ba su samu dawowar lantarkin ba.
Duk da haka filayen jirgin sama, da tashoshin jiragen ruwa na ci gaba da aiki lafiya ƙalau, a cewarsa, inda ya ƙara da cewab wayoyin salula da layukan fibre optics na aiki a kashi 90 cikin 100 na ƙasar.
Gwamnatin ƙasar ta ce ta yanke shawarar fito da man fetur da ta ajiye na ko-ta-kwana tsawon kwana uku wanda za a iya buƙata.

Asalin hoton, Facebook/Mansur Ahmed
Jigo a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, Sule Lamido, ya yi gargadin cewa ƙoƙarin rusa jam’iyyar tamkar yunƙurin murƙushe dimokaradiyya ne.
Sule Lamido wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa ne a arewacin ƙasar kuma tsohon ministan harkokin waje, ya ce ficewar wasu jiga-jigan PDP zuwa APC mai mulki tuggun ne da ba zai yi wa ‘yan siyasa daɗi ba nan gaba.
"Murƙushewa da gana azaba, su ne alamun cewa mulki ya zo - haka abin yake a tarihi," in ji shi cikin wata hira da BBC.
"Ya kamata a ce Shugaba Bola Tinubu ya yi adalci, ya san cewa shi shugaban kowa da kowa ne, ya ƙyale mu mu 'yansiyasa mu yi kokawa da APC a jam'iyyance. Amma idan bai yi hankali ba dabarar za ta ci shi."
A jiya Litinin Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gada Ifeanyi Okowa suka koma jam'iyyar APC a hukumance bayan sun bar PDP.
A baya-bayan nan wasu 'yanmajalisa daga jam'iyyun adawa na Labour da NNPP sun koma APC ɗin, yayin da ake raɗe-raɗin wasu gwamnonin na kan hanyar komawa APC ɗin.

Asalin hoton, EFCC
Hukumar EFFC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta fara bincike kan wasu dubun dubatar kuɗaɗen ƙasar waje da aka kama a filin jirgin sama na Kano.
EFCC ta ce an ga dala 86,500,305 da kuma riyal 305,150 ne cikin wata jaka lokacin da aka ga wani ma'aikacin filin jirgin mai suna Sale Bala ya yi yunƙurin ɗaukar ta ranar Lahadi.
"Bayan bincike, jami'an kwastam sun gano kuɗaɗen ne da aka ɓoye cikin zannunwan gado," in ji EFCC cikin wata sanarwa.
"An kama Sale Bala da wani Abdullahi Tahir da ake zargin shi ne aka tsara zai karɓi jakar bayan kammala tantance ta."
Ta ƙara da cewa kuɗin da kuma waɗanda ake zargi na tsare a hannunta, kuma za ta kai su kotu da zarar an kammala bincike.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da ƙoƙarin yaudarar duniya ta hanyar ayyana tsagaita bude wuta ta kwanaki uku a mako mai zuwa.
Fadar Kremlin ta ce za a dakatar da yakin ne daga ranar 8 zuwa 11 ga watan Mayu, wanda ya zo daidai da bukukuwan samun nasara kan sojojin yan Nazi na Jamus yayin yaƙin duniya na biyu.
Sai dai Mista Zelensky ya ce an yi sanarwar ne da nufin tabbatar da lumana yayin faretin sojojin Rasha.
Wakilin BBC ya ce su ma masu sukar Rasha ba za su ga wannan tsagaita wuta a matsayin an yi ta da zuciya daya ba, face ma wata toshiyar baki ga fadar White House da nufin nuna wa Shugaba Trump cewa Rasha ce mai son zaman lafiya.
Shugaba Zelensky na Ukraine ya yi kiran a tsagaita wuta cikin gaggawa tsawon kwana 30, wadda za ta samar da tushe ga abin da ya bayyana a matsayin diflomasiyya ta gaske.

Asalin hoton, NG Police
Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce ta kama mutum 15 da take zargi da aikata fashi da kuma garkuwa da mutane a faɗin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Olumiyiwa Adejobi ya ce dakarunsu sun yi nasarar ƙwace makamai da dama.
Sanarwar ta ce rundunarta ta Special Tactical Squad (STS) ce da taimakaon mafararuta da 'yan sa-kai ta yi nasarar kama 'yanfashi huɗu a jihar Taraba ranar 25 ga watan Afrilu, sannan ta ƙwace bindigogi uku.
A jihar Kaduna kuma, wani samame da dakaru suka kai ya yi sanadiyyar kama mutum biyar da zargin aikata fashi. An kama ɗauke da bindigogi ƙirar AK-49 da AK-47 huɗu.
"A ranar 17 ga watan Afrilun kuma, dakarun sun kama wani mai suna Isa Ibrahim, wanda ya amsa cewa ya koma Kaduna ne domin kafa wata sabuwar dabar 'yanfashi bayan kama abokan aikinsa a jihar Kwara," in ji sanarwar.
"Ranar dai, samamen da jami'ai suka kai a ƙauyen Lamido ya yi nasarar kama 'yanfashi biyu, waɗanda suka amsa laifukan fashi.
"A ranar 18 ga watan, 'yansandan jihar [Kaduna] sun kama wasu masu safarar bindigogi ɗauke da binidigogin AK-47 biyu, daga baya kuma suka kama wani ɗauke da bindigogi biyu ƙirar gida da wata doguwar sarƙa a cikin buhu."