'Aƙalla ƴanjarida 186 aka kashe a Gaza'

Asalin hoton, Abdalhkem Abu Riash/Anadolu via Getty Images
Ƙungiyar kare ƴanjarida ta Committee to Protect Journalists (CPJ) ta ce aƙalla ƴanjarida 186 ne aka tabbatar da kashewa tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙinta a Gaza a watan Oktoban 2023.
Ƙungiyar CPJ ta ce tsakankanin yaƙin ne lokaci mafi muni ga ƴanjarida tun daga shekarar 1992 da ta fara bibiyar halin da ƴanjarida suke shiga.
"Ƴanjarida na fuskantar babbar barazana, wasu lokutan barazanar rayuwarsu a wajen ɗauko rahoton yaƙin, ciki har da luguden wuta ta sama da Isra'ila ke yi," kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata.
A watan jiya, BBC da wasu kafofin sadarwa - Reuters da AP da AFP - sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa, inda a ciki suka bayyana takaikinsu kan halin da ƴanjarida ke shiga a zirin, waɗanda suka ce suna kwanaki ba tare da samun abinci ba.
Wakilan BBC na wucin-gadi guda uku daga zirin sun ce sukan yi kwanaki ba su ci komai, har ma akwai wani wanda ya yanke jiki ya faɗa a daidai lokacin da yake ɗauko rahoto.
Sama da ƙungiyoyin agaji na duniya guda 100 ne suka yi gargaɗin cewa Gaza za ta faɗa matsananciyar yunwa, lamarin da Isra'ila ta zargi ƙungiyoyin da yarda da farfagandar ƙungiyar Hamas.




