Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/08/2025
Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya tura jam'ian rundunar tsaro ta ƙasa zuwa birnin Washington don yaƙi da laifukan da ake ganin sun gagari ƴan sanda birnin.
Yawan aikata laifuka a babban birnin Amurkan na raguwa, sai dai shugaban ƙasar ya bayyana cewa ana zubar da jini da samun tashe tashen hankula da laifuka masu muni a birnin.
Mista Trump ya kuma nuna yiwuwar tura sojoji nan gaba. Ya kuma ƙara da cewa a shirye yake ya ɗauki irin wannan mataki a wasu biranen ƙasar.
Ya ce lamarin na kokarin zama na rashin bin doka, kuma za su kawar da unguwannin talakawa inda masu aikata laifin suke.
Sai dai kamar birnin na Washington, jihohin da Trump ya ambato na ƙarƙashin jam'iyyar Democrat ne.

Asalin hoton, Kashim Shettima/X
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya nuna kaɗuwarsa kan rasuwar tsohon ministan noma, Cif Audu Ogbeh.
Shettima ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa ta'aziyya ga iyalan marigayin ranar Litinin, inda ya ce Nijeriya ta rasa ɗaya daga cikin jagorori na gari.
Ya kwatanta mutuwar Ogbeh da cewa rashi ne ga ɓangaren noma da kuma cigaban Najeriya.
"Ba za a manta irin gudummawar da Audu ya bayar wajen bunƙasa noman abinci ba a Najeriya," in ji Shettima.
Tsohon ministan noman ya rasu ne ranar Asabar yana da shekara 78.
Ogbeh ya fara siyasa a shekarar 1979, inda ya zama ɗanmajisar jihar Benue, har ya zama mataimakin shugaban majalisar.
Haka kuma ya taɓa zama shugaban jam'iyyar PDP a zamanin Olusegun Obasanjo.

Asalin hoton, Kashim Shettima/X

Asalin hoton, Kashim Shettima/X

Asalin hoton, Getty Images
Sama da mutum 3,000 ne suka tsere daga muhallinsu a ƙauyuka 15 na jihar Kwara da ke arewacin Najeriya bayan harin ƴanbindiga a jihar.
Harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗansanda da wasu mutum huɗu, ya faru ne ne a garin Babanla da ke ƙaramar hukumar Ifelodun na jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jaridar ta ruwaito cewa wasu ƴan ƙungiyar Mahmuda ne ake zargi suka kai harin a ƙauyukan a tsakanin ranakun 8 zuwa 10 ga watan Agusta.
Haka kuma rahoton ya bayyana cewa ƴanbindigar sun kai farmaki ofishin ƴansanda na Babanla, inda suka ƙwace makamai, sannan suka yi garkuwa da wasu mutane da ba a tantance ba.
"Garin da muka fi tunanin ya fi aminci shi ne Babanla, kuma shi ma ɗin an kai hari a yanzu. Dole za mu bar garin domin babu wanda yake so ya mutu. Ya kamata gwamnati ta kawo mana ɗauki," in ji wani mazaunin garin mai suna AbdulRahman.
Jihar Kwara dai na cikin jihohin da a baya ake tunanin ba su cika fuskantar matsalar tsaro ba, amma yanzu ake fargabar matsalar ta fara shiga.

Asalin hoton, Getty Images
Iraq ta shiga cikin duhu bayan ɗaukewar lantarki a faɗin ƙasar sakamakon durkushewar wata tashar samar da makamashi, a yayin da buƙatar lantarkin ya ƙaru saboda tsananin zafi.
Gwamnatin ƙasar ta buƙaci al'ummar ta da su rage amfani da wutar, a yayin da injiniyoyi ke kokarin dawo da lantarkin.
Ɗaukewar wutar ta sanya akasarin ƴan ƙasar zama ba tare da fankoki ko na'urorin sanyaya wuri ba a cikin yanayin zafin da ya kusa kai wa maki 50 a ma’aunin celcius.
Iraq ƙasa ce da ke cikin manyan ƙasashen da ke samar da mai a duniya, sai dai ta dogara ne da iskar gas daga Iran domin samar da makamashi.

Asalin hoton, EPA
An samu ƙarin mutum 11 da suka rasu a sanadiyar rashin abinci mai gina a Gaza, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Gaza ta bayyana.
Wannan ke nufin jimillar waɗanda suka rasu a sanadiyar rashin abinci mai gina jiki sun kai 212, ciki har da ƙananan yara 98.
Haka kuma aƙalla 38 aka kashe, sannan wasu 491 suka jikkata a sanadiyar hare-haren Isra'ila a cikin awa 24 da suka gabata, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.
Ana dai cigaba da samun rahotannin mace-mace a zirin a daidai lokacin da wa'adin da aka ba mutanen yankin su kwashe kayansu, su bar Gaza a yunƙurin da Isra'ile ke yi na ƙwace zirin.
Rahotanni daga Isra'ila na nuna cewa Isra'ila na so ne ta ƙwace birnin Gaza, sannan ta mayar da mutanen garin zuwa can kudancin birnin, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a duniya.

Asalin hoton, @officialEFCC
Jam'iyyar haɗaka ta ADC ta zargi hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da cewa ta zama ƴar koren jam'iyya mai mulki ta APC, inda suke zaɓar waɗanda suke yin bincike a kansu.
Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta hannun sakataren yaɗa labaranta, Malam Bolaji Abdullahi, ta ce abin da EFCC ke yi a yanzu na sake buɗe shari'o'i da aka kammala da fito da fayil-fayil na shekaru da suka wuce har ma da matsa wa mambobin jam'iyyar, ba irin aikin da aka san hukumar ba ce da shi, illa wadda ke yi wa wani aiki.
A baya-bayan nan dai mambobin jam'iyyar haɗakar sun ce sun samu sakonnin gayyata daga EFCC waɗanda suka ce suna alaƙa da siyasa.
"Hukumar na yin haka ne domin matsa wa manyan jiga-jigan adawa lamba duk da cewa ba su aikata wani laifi ba," in ji sanarwar.
Jam'iyyar ta ce ta lura cewa an daina yin bincike kan waɗanda ke cikin jam'iyya mai mulki, inda aka mayar da hankali kan ƴan adawa waɗanda ba su aikata komai ba ko ma shari'o'in a aka riga aka kammala tuntuni.
"An kafa EFCC ne domin yaƙi da rashawa ta kuma gudanar da aiki ba tare da jin tsoro ba. Aikinta shi ne kama duk wani mai laifi ko a ina yake, kama daga jam'iyya mai mulki zuwa ta adawa da sauransu. Amma a yau hukumar ta sauka daga turbar da aka kirkiro ta, inda ta koma aiki kamar wani sashe na jam'iyyar APC," in ji Bolaji Abdullahi.
Don haka ne ADC ta yi kira ga dukkan ƴan Najeriya, ƙungiyoyin farar hula da kuma kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu da su yi watsi da irin abin da hukumar ke yi na kama ƙarya don cimma manufofinta.

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da yin Alla-wadai daga sassan duniya kan kisan ƴan jaridar Al Jazeera biyar.
Sun mutu ne bayan hari da Isra'ila ta kai Gaza:

Asalin hoton, Getty Images
Mutum biyar da ake zargi da shirya harin bam a Coci Katolika ta Saint Francis da ke Owo, Jihar Ondo, a shekarar 2022, sun musanta tuhume-tuhume tara na ta’addanci da gwamnatin Tarayya ta shigar a kansu.
An gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya a ranar Litinin, inda ake zargin su da kasancewa mambobin ƙungiyar ta’addanci ta Al-Shabab a sashenta na jihar Kogi, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Mai Shari’a Nwite ya sanya ranar 19 ga Agusta, 2025 a matsayin ranar fara sauraron shari’ar, sannan ya yi umarni da a ci gaba da tsare su a hannun hukumar tsaro ta DSS.
Gurfanar na zuwa ne bayan shekara uku da tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya sanar da cewa an kama waɗanda ake zargi da kitsa harin.
Majalisar tsaro ta ƙasa ta danganta harin da miyagun ayyukan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP.
Fiye da mutum 40 ne suka rasu a harin, sannan da da dama suka jikkata, lokacin da ƴanbindigar suka kai farmaki a cocin a wata ranar Lahadi a daidai lokacin da suka gudanar da ibada.
Tsohon gwamnan Jihar, marigayi Rotimi Akeredolu, ya bayyana harin a matsayin “cin zarafin ɗan'adam."

Asalin hoton, @GoitaAssimi
Rasha ta yi kira ga ƙasashen duniya su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen taimakon haɗakar ƙasashen Alliance of Sahel States wato AES domin ba su taimakon da suke buƙata a yaƙin da suke yi da matsalar tsaro.
Ƙasashen AES ɗin su ne Mali da Burkina Faso da kuma Nijar waɗanda suke ƙarƙashin mulkin soja bayan shugabannin mulkin ƙasashen sun hamɓarar da gwamnatin fararen hula.
Kafar Actualite.bf mai zaman kanta ne ta ruwaito cewa Rasha ta gabatar da wannan ƙoƙon baran ne a jawabinta ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda wakilinta na dindindin, Dmitry Chumakov ya ce ƙasashen na buƙatar agajin tsaro.
"Domin samun dawwamammen zaman lafiya, ya kamata ƙasashen duniya su ba ƙasashen Mali da Burkina Fasp da Nijar gudunmuwa," in ji Chumakov.
Ya ƙara da cewa, "ƙasashen Afirka ɗin ne da kansu suka fi sanin yadda za su magance matsalolin da suke fuskanta, kuma su ne suka fi sanin yadda za su yi yaƙi da matsalar tsaro da kuma hanyoyin inganta dimokuraɗiyya da tattalin arzikinsu."
Rasha dai ta zama babbar ƙawar ƙasashen na AES, waɗanda ke jan jikinsu daga wasu ƙasashen na yamma, inda Moscow ta ƙuduri aniyar taimakon ƙasashen wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.

Asalin hoton, Nwadike Precious
Ƙungiyar ƴan fansho na arewacin Najeriya, NUP ta ce jihohi huɗu cikin 19 na arewacin Najeriya ne kaɗai suke biyan mafi ƙarancin fanshon naira 32,000 da gwamnatin tarayya ta tsara.
Da yake bayani a taron shiyya na ƙungiyar a Kaduna, shugaban ƙungiyar, Kwamrade Mohammed Sali ya bayyana lamarin da "rashin adalci" da ya ce ake yi wa tsofaffin ma'aikatan bayan sadaukar da rayuwarsu da suka yi wajen aikin al'umma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
"Jihohi huɗu ne kacal ke biyan mafi ƙarancin fansho na naira 32,000 a arewacin Najeriya mai jihohi 19. Akwai jihohin da suke biyan fanshon naira dubu 3,000 da 4,000 da 5,000," in ji shi, inda ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta fi mayar da hankali kan neman hanyoyin sasanci maimakon fito na fito da gwamnatocin jihohin.
"Ba za mu yi fito na fito da gwamnonin jihohin ba domin mu iyaye ne. Kuna so ku ga iyayenku a tituna suna gudanar da zanga-zanga? za mu zagaya jihohin mu tattauna da hukumomi domin samun sasanci cikin lumana," in ji Sali.

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto da tashar Channels ta ruwaito daga cibiyar Zamfara Circle Community Initiative ya bayyana cewa a mako ɗaya, an kai hari a ƙauyuka 15 a tsakanin 4 zuwa 10 ga watan Agusta.
Rahoton cibiyar ya ce hare-haren sun yi sanadiyar garkuwa da kusan mutum 144, sannan an kashe kusan mutum 24 tare da jikkata wasu mutum 16.
Rahoton ya ƙara da cewa garuruwan da aka kai wa harin su ne: Sabe da Tungar Yamma da Sauru da Lambasu da Dogon Madacci da Dankalgo da Kwanar Kalgo a ƙaramar hukumar Bakura.
A ƙaramar hukumar Tsafe, rahoton ya nuna cewa an kai harin a garuruwan Chediya da Kucheri da Yankuzo da Katangar Gabas Bilbils.
A ƙaramar hukumar Mafara kuma, ƙungiyar ta ce an kai harin a Tabkin Rama da Matsafa da Ruwan Gizo, sai kuma Rafin Jema da ke Gummi da Adabka da Masu a ƙaramar hukumar Bukkuyum.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a ƙasar Gambia sun ƙaddamar da bincike kan mutuwar wata jaririya ƴar wata ɗaya da ake zargi ta mutu ne a sanadiyar kaciyar da aka mata a ƙauyen Wellingara.
Binciken asibiti na farko-farko ya tabbatar da jaririyar ta ji rauni, wanda hakan ya sa hukumomi suka ce za a gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan gawa domin tabbatar ko an mata kaciyar, sannan ko kaciyar ce silar mutuwarta.
Lamarin dai ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasar.
A wata sanarwa da ƴansanda suka fitar, sun ce kaciya aka yi wa jaririyar, lamarin da ya sa jini ya ɓarke mata, har ta ce ga garinku.
Tuni aka kama mata mata biyu da ake zargi da hannu a lamarin.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam da dama sun soki lamarin, sannan suka yi kira da a yi bincike, sannan a tabbatar an yi adalci.

Asalin hoton, Abdulaziz Usman Kwari
A Najeirya, Rahotannin na nunar da cewa, wasu tankokin biyu ɗaya maƙare da man fetur da wata mai ɗauke da gas, sun gogi juna tare da haifar mummunar fashewa a garin Ɗa Magaji da ke yankin Zariya na jihar Kaduna.
Lamarin dai ya faru ne bayan tayar tankar mai ɗin mai ɗauke da mai ta fashe ta fara tangal-tangal, inda ta gogi tankar ɗayan tankar mai ɗauke da gas ɗin.
Lamarin ne ya yi sanadiyar faɗuwarsu ƙasa tare da yin bindiga.

Asalin hoton, Abdulaziz Usman Kwari

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kashe ƴanjarida da Isra'ila ta yi a Gaza babban laifi ne, lamarin da ta ce ya saɓa da dokokin duniya.
A wani rubutu da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta yi Allah-wadai da harin da Isra'ila ta kai kai-tsaye zuwa tantin da ƴanjaridar suke zaune, inda ta ƙara da cewa, "dole Isra'ila ta riƙa kula da dukkan fararen hula, ciki har da ƴanjarida da suke gudanar da aikinsu."
"Muna kira da a tabbatar da cewa ƴanjarida suna samun damar bayar da rahoton abubuwan da ke faruwa a Gaza ba tare da fuskantar ƙalubale ba," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Asalin hoton, AFP
Sojojin Jamhuriyar Nijar sun samu nasarar ceto ƴancirani guda 50 da suke maƙala a sahara a hanyarsu ta tafiya ƙasar Libya.
RFI ta ruwaito cewa mutanen sun maƙale ne a kusa da bakin iyakar shiga ƙasar ta Libya bayan motarsu ta lalace a ranar 10 ga watan Agusta.
"Motarsu ta lalace ne a hanyarsu ta tafiya Libya, ƙasar da ake ratsawa domin tafiya ƙasashen turai. A ciki akwai fasinjoji 44 kuma motar tana tafiya ne a hanyar Madama-Dao da ke arewacin Nijar a lokacin da ta lalace, ta tsaya cak," in ji rahoton na RFI.
Daga baya ne aka shiga neman motar, inda sojojin suka samu nasarar ceto su, sannan aka kai su garin Madama, inda ake cigaba da kula da su.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da asalin ƙasashen da mutanen suka fito ba, da kuma asalin ƙasar da suke shirin zuwa.

Asalin hoton, PRESIDENCY NG
Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta musanta rahotannin da ke nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da lafiya kuma ana shirin fitar da shi zuwa asibiti a ƙasar waje.
A makon da ya gabata ne dai cibiyar aikin jarida mai binciken ƙwaƙwaf ta Najeriya, ICIR ta rawaito cewa wasu majiyoyinta sun tabbatar mata da cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na ta shirye-shiryen fitar da shugaba Tinubu zuwa ƙasar wajen domin neman magani.
Cibiyar kamar dai yadda ta wallafa a shafinta na intanet ta ce "rahotanni na nuna cewa shugaba (Tinubu) na kwance a gado ba ya iya zuwa ko'ina abin da ya janyo rashin gudanar da al'amuran shugabanci. Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilci shugaban a wasu ayyukan gwamnati."

Asalin hoton, Umar Dikko Radda
Gwamnatin jihar Katsina a Najeriya ta yi martani kan sanarwar da ƙungiyar agaji ta Medicins Sans Frontiers, MSF, ta fitar wanda ke cewa aƙalla kananan yara 652 suka mutu cikin watanni 6 a jihar, sakamakon matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.
A ƙarshen makon da ya gabata ne dai kungiyar MSF ta sanar da cewa zabtare kuɗaɗen tallafi da take samu daga ƙasashen duniya na janyo tsaiko a ƙoƙarin da take yi na tallafawa harkar kula da lafiya musamman a ƙasashe masu tasowa.
Barista Bulama Bukarti ya yi sharhi kan matsalar, inda ya ce "MSF ta ce a wata shida farko kawai na wannan shekarar an kawo yara aƙalla dubu 70 a asibitocinta, a ciki kuma kimanin dubu 10 sai da aka kwantar da su sannan daga cikinsu kuma yara 650 suka mutu a jihar Katsina."
Da take martani kan batun, gwamnatin Katsina da bakin shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko, Dr Shamsuddeen Yahaya, ya ce duk da cewa akwai cutar yunwar, akwai wasu matsalolin da suke ta'azzara matsalar.
"Mun san akwai matsalar tamowa a Katsina, kamar yadda take a sauran jihohin arewa maso yamma, hakan ya sa gwamnatin Katsina ta ware ƙarin naira miliyan 500 ɗoriya a kan naira miliyan 500 da aka fara warewa domin fuskantar matsalar."
Sai dai ya ce duk da sun san akwai yunwa, "amma akwai wasu cututtuka da ma rashin sani da suke ta'azzara matsalar saboda misali bincike ya nuna shayar da yaro nonon uwa zalla a wata shidan farko na kare yaro daga cututtuka. Sannan matsalar tsaro na taka rawa."

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar ƴantawaye ta M23 a Congo ta musanta zarginta da ake yi da kashe gomman fararen hula a Kudancin Kivu na ƙasar, sannan kuma ta nanata cewa zarginta da ake yi da amfani da ƙananan yara a yaƙi ƙanzon kurege ne.
Kakakin M23, Willy Ngoma ne ya bayyana wa BBC haka, inda ya ce ko kaɗan ba ya cikin tsarinsu kai farmaki kan fararen hula.
"Ba ma kashe fararen hula. Ta yaya za mu kashe ƴanƙasa, waɗanda muke fafutikar karewa? ko kajin fararen hula ba za mu kashe ba, saboda muna girmama mutane," in ji Ngoma.
Rundunar sojin Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo ce ta zargi ƙungiyar ta M23 da kashe fararen hula bayan hukumomin kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya sun bayyana cewa an kashe aƙalla fararen hula 300 a ƙasar, wanda ake alaƙantawa da ƴantawayen masu samun goyon baya daga Rwanda.
Ngoma ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta da ido a yankunan da M23 ke da iko, kuma ta fi samun bayanai daga gwamnatin ƙasar.
Masana dai suna ganin duk da yunƙurin Amurka da Qatar na shiga tsakani domin samar da maslaha a ƙasar, alamu na nuna cewa akwai sauran rina a kaba.

Asalin hoton, Getty Images
An gudanar da sallar gawa ta ƴanjaridar Al Jazeera guda biyar da hare-haren Isra'ila suka rutsa da su a Gaza, waɗanda suka yi sanadiyar mutuwarsu a daren jiya Lahadi.
Al Jazeera ta ruwaito cewa an kwashi gawarwakin ƴanjaridar ne daga asibitin al-Shifa, inda aka kashe su, sannan aka tafi da su gidajensu domin a musu sutura.
Hotuna sun nuna yadda ɗimbin mutane suka halarci sallar gawarwakin a Gaza cikin jimami da alhini.
A daren jiya ne dai hare-haren Isra'ila suka kashe fitaccen ɗanjarida Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa huɗu a wani hari da ta kai Gaza.
Isra'ila ta ce tana zargi yana da alaƙa da Hamas sannan ta ce ta hallaka shi ne saboda irin rahotannin da yake bayarwa masu tsanani daga arewacin Gaza.
Sauran ƴanjaridar da aka kashe su ne: Ibrahim Zaher da Mohammed Noufal da Moamen Aliwa waɗanda dukkanin su suna aiki ne da kafar ta Al Jazeera.