Hatsarin jirgin sojan Sudan ya kashe sojoji da fararen hula

Asalin hoton, Getty Images
Wani jirgin sojan Sudan ya yi hatsari a yankin Omdurman da yammacin Talata, inda fasinjoji da sojoji da dama suka mutu, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Suna.
Ba tare da wani ƙarin bayani ba, mai magana da yawun rundunar sojin ya ce jirgin ya faɗo ne yayin da yake yunƙurin tashi daga filin jirgin sama na Wadi Seidna.
"Mun samu mutanen da suka mutu da waɗanda suka ji rauni da yawa cikin sojoji da fararen hula. An bai wa waɗanda suka ji rauni magani, masu kashe gobara kuma sun daƙile wutar a wurin da ke Al-Iskan," in ji wata sanarwa.
Jaridar Sudan Tribune da ke birnin Paris ta ruwaito cewa fararen hula aƙalla biyar ne suka mutu sannan da yawa suka ji rauni lokacin da ɓaraguzai suka rikito a kusa da gidajen jama'a.
Ta ambato wasu majiyoyin soji da suka ce lamarin ya faru ne sakamakon matsalar na'ura, kuma akwai manyan jami'ai a cikin fasinjojin.



