Gasar kofin duniya 2026: Brazil ta kai zagayen ƴan 16 bayan cin Japan

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagayen ƙasashe 32
Brazil 2 , Japan 1 at Full time
Brazil
Japan
Full time
Hutun rabin lokaci Brazil 0 , Japan 1

Key Events

Brazil

  • Casemiro Goal 56 minutes
  • Gabriel Martinelli Goal 90 minutes plus 5

Japan

  • K. Sano Goal 29 minutes
Ba da ƙwallo a ci
Brazil,Gabriel Magalhães (56 minutes), Bruno Guimarães (90 minutes plus 5)

Taƙaitattu

  • Brazil za ta fafata da Japan a zagayen ƴan 32 a gasar kofin duniya 2026
  • Duk wadda ta yi nasara za ta kara da ko dai Norway ko Ivory Coast a zagayen ƴan 16
  • Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
  • Zagaye na biyu a gasar kofin duniya 2026: Jamus za ta fafata da Paraguay
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
  • An fitar da Afirka ta Kudu a gasar kofin duniya a hannun Kanada a zagayen ƴan 32
  • Messi ne kan gaba a takarar ƙyautar takalmin zinare a gasar kofin duniya mai ƙwallo shida a raga a wasa uku
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan kun ji dadin kasancewa da mu, za kuma ku kasance a shirinmu na gaba da muke kawo muku sharhi da bayanan gasar cin kofin duniya kai tsaye.

    Sunana Mohammed Abdu da na gabatar da shirin da kuma taimakon AI.

    Mu hadu a shirinmu na gaba.

  2. Wasannin da za a buga ranar Talata, Brazil 2-1 Japan

    Liv

    Asalin hoton, BBC Sport

  3. Yadda aka taka leda a fafatawar, Brazil 2-1 Japan

    Liv

    Asalin hoton, BBC Sport

  4. An tashi wasan, Brazil 2-1 Japan

    Shi kenan Brazil ta kai zagayen yan 16 a gasar cin kofin duniya ta 2026.

    Ƴan wasan tawagar Japan sai kuke suke a filin wasa na Houston, domin sunga ta leko ta koma, sune suka fara cin kwallo daga baya aka farke aka kara musu na biyu daf a tashi.

    Gabriel Martinelli #22 na Brazil yana murna tare da abokan aiki bayan ya zira kwallo ta biyu a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 Round Of 32 tsakanin Brazil da Japan.

    Asalin hoton, Getty Images

  5. GOAL - Brazil 2-1 Japan, Gabriel Martinelli

    Daf da za a tashi dan wasan Arsenal, Martinelli ya samu kwallo ya kuma yi gaba da gaba da mai tsaron bayan Japan ya kuma buga da fadi, domin sai ta bugi turke sannan ta fada raga.

    Gabriel Martinelli #22 na Brazil yana murnar zura kwallo ta biyu ta kungiyarsa yayin wasan gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 Round Of 32 tsakanin Brazil da Japan.

    Asalin hoton, Getty Images

  6. , Brazil 1-1 Japan

    Endrick yana taka rawa ya samu dama daga kusurwa, amma ya buga ta yi kwana.

  7. , Brazil 1-1 Japan

    Casemiro ya fita an kuma sa Fabinho ya canje shi.

  8. Minti 90 ya cika an kuma yi karin lokaci, Brazil 1-1 Japan

    An kara minti shida, bayan da minti 90 ya cika.

    Shin za a ci kwallo a wannan karin lokacin ko kuwa?.

  9. , Brazil 1-1 Japan

    Brazil na sa matsi ta yi bugun tazara kuma mai tsaron ragar Japan ya sa mata hannu ta je wajen Vinicius ya daga kafa ya kuma ja ya buga amma ta je kwana.

    Yana daga hannu magoya baya su ci gaba da kuwa.

  10. , Brazil 1-1 Japan

    Kwallo mai kyau aka sakawa Endrick nan da nan golan Japan ya fito da gudu ya doka ta wajen jiya.

    Brazil na sa kuzari ko za ta samu damar kara na biyu.

  11. , Brazil 1-1 Japan

    Martinelli yana kasa a kwance a gidan Japan, ya yi kokarin sakawa kwallo kai, amma aka riga shi.

    Brazil's forward #22 Gabriel Martinelli (L) reacts next to Italian referee Maurizio Mariani during the 2026 World Cup round of 32 football match between Brazil and Japan.

    Asalin hoton, Getty Images

  12. , Brazil 1-1 Japan

    Suzuki ya karbi katin gargadi sakamakon wata keta da ya yi a gefen fili daf da za a shiga gidan Japan.

  13. Mun shiga saura minti 10 da suka rage a wasan, Brazil 1-1 Japan

    Shin za a kara kwallo na biyu ko kuma haka za su tashi?

  14. Japan ta kara yin canjin ƴan wasa, Brazil 1-1 Japan

    Ao Tanaka da Shuto Machina sun shiga fili su maye gurbin Daichi Kamada da kuma Junya Ito.

    Kawo yanzu Japan ta yi canji hudu, saura daya ya rage mata.

  15. , Brazil 1-1 Japan

    Brazil ta samu damar kara kwallo, kuma iri daya da yadda ta ci ta farko.

    Sai dai kwallon da Rayan ya sakawa kai ta doki keyar mai tsaron bayan Japan ta kuma je kwana.

  16. , Brazil 1-1 Japan

    Gabriel Magalhaes shi ne na biyu da ya raba kwallo 100 ko fiye da aka a gasar kofin duniya dan kasar Brazil tun bayan Dunga da ya yi bajintar linki uku a 1994.

    Gabriel Magalhaes #3 na Brazil yana kallo yayin wasan gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 Round Of 32 tsakanin Brazil da Japan.

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Brazil da Japan kowa ya yi canji, Brazil 1-1 Japan

    Matheus Cunha ya fita, an maye gurbinsa da Gabriel Martinelli.

    Ita kuwa Japan ta fitar da Keito Nakamura da Ritsu Doan ta maye gurbinsu da Yukinari Sugawara da kuma Junnosuke Suzuki.

  18. An je hutun shan ruwa, Brazil 1-1 Japan

  19. , Brazil 1-1 Japan

    Kadan ya rage Brazil ta kara kwallo, inda Vinicius ya buga ta je ta bugi turke da ya ci ta biyar a gasar nan.

    Tun da aka koma zagaye na biyu Brazil take ta saka matsi a kan Japan.

  20. GOAL - Brazil 1-1 Japan, Casemiro

    Tsohon dan wasan Manchester United, Casemiro aka bugowa kwallo, wanda ya yi tsalle ya saka kai ta fada raga, wasan ya koma 1-1.

    Casemiro #5 na Brazil yana murna tare da Bruno Guimaraes # 8 bayan ya zira kwallo ta farko a lokacin gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 Round Of 32 tsakanin Brazil da Japan.

    Asalin hoton, Getty Images