Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar kofin duniya 2026: Brazil ta kai zagayen ƴan 16 bayan cin Japan

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagayen ƙasashe 32
Brazil 2 , Japan 1 at Full time
Brazil
Japan
Full time
Hutun rabin lokaci Brazil 0 , Japan 1

Key Events

Brazil

  • Casemiro Goal 56 minutes
  • Gabriel Martinelli Goal 90 minutes plus 5

Japan

  • K. Sano Goal 29 minutes
Ba da ƙwallo a ci
Brazil,Gabriel Magalhães (56 minutes), Bruno Guimarães (90 minutes plus 5)

Taƙaitattu

  • Brazil za ta fafata da Japan a zagayen ƴan 32 a gasar kofin duniya 2026
  • Duk wadda ta yi nasara za ta kara da ko dai Norway ko Ivory Coast a zagayen ƴan 16
  • Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
  • Zagaye na biyu a gasar kofin duniya 2026: Jamus za ta fafata da Paraguay
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
  • An fitar da Afirka ta Kudu a gasar kofin duniya a hannun Kanada a zagayen ƴan 32
  • Messi ne kan gaba a takarar ƙyautar takalmin zinare a gasar kofin duniya mai ƙwallo shida a raga a wasa uku
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Brazil ta raba kwallo sau 359 a zagayen farko, wannan ya nuna yadda Brazil ke son farke kwalon nan.

  2. Mun koma zagaye na biyu, Brazil 0-1 Japan

    Za kuma yi a minti 45 da kuma yin hutun shan ruwa.

    Abin tambaya ko Brazil za ta farke kwallon nan kuwa?

    Komai zai iya faruwa a lokacin tamaula.

  3. , Brazil 0-1 Japan

    Carlo Ancelotti ya saka dan wasa mai shekara 19, Endrick bayan da aka koma hutu.

    Ya maye gurbib Lucas Paqueta, wanda yake ta dingishi.

  4. Yadda aka taka zagayen farko, Brazil 0-1 Japan

  5. , Brazil 0-1 Japan

    An je hutun rabin lokaci za su yi minti 15, sannan su dawo a ci gaba da zagaye na biyu minti 45 za kuma a yi hutun shan ruwa.

    Shin me zai faru a zagaye na biyun?

  6. , Brazil 0-1 Japan

    Kafin na an bai wa Daichi Kamada katin gargadi.

  7. Minti 45 ya cika, Brazil 0-1 Japan

    Minti 45 ya cika an kuma yi karin minti hutu.

    Ko Brazil za ta farke kafin lokacin nan ya cika?

  8. , Brazil 0-1 Japan

    Yanzu dai Japan ce ke gara kwallo daf da gidan Brazil tana raba kwallo hagu da dama da tsakiya tana yin bani in baka, amma dai ba ta samu shiga cikin gidan Brazil ba.

  9. , Brazil 0-1 Japan

    Wasan bayan nan da suka fafata, Japan ce ta doke Brazil 3-2.

    Ko Brazil za ta yi wani abu a karawar nan kuwa.

    Sai dai kuma Brazil ba ta samun damar ratsa bayan Japan, sai dai ta buga kwallo daga waje, abinda take yi kenan kuma babu kuzari.

    Cin golan Japan daga nesa ai sai an yi da gaske kam.

  10. Matsala ga Brazil idan aka yi la'akari da wannan lissafi, Brazil 0-1 Japan

    Brazil ta kasa cin wasa daga biyar baya da aka fara zura mata kwallo a raga, tun daga lokacin da ta yi nasara a kan Croatia ranar 12 ga watan Yunin 2014.

  11. , Brazil 0-1 Japan

    Brazil sai kai kora take gidan Japan tana ta kokarin yadda za ta fasa bayan abokiyar hamayya, amma abin bai yiwuwa.

    Kuma Brazil ta kula da bayanta domin Japan da zarar ta tsinke da kwallo ta komai zai iya faruwa.

  12. GOAL - Brazil 0-1 Japan, Kaishu Sano

    Houston ta rude da kuwwa.

    Brazil ta yi kokarin bayar da kwallo sai Sanu ya sa kafa ya kuma ja zuwa gidan Brazil yana ta gudu yana tangal-tangal har ta kai ga ya buga kwallon da karfi ta kuma je ta farda ragar Brazil.

    Tun daga wajen layi ya buga kwallon ta yi fadi sosai da golan Brazil ya kasa taba kwallon.

  13. An ci gaba da wasan, Brazil 0-0 Japan

    Har yanzu ba wasu mugayen hare-hare da aka kai da fatan wasan nan za a kammala shi a cikin mintin 90 ba tare da bugun fenariti ba.

  14. An je hutun shan ruwa, Brazil 0-0 Japan

  15. , Brazil 0-0 Japan

    Dan wasan Crystal Palace, Daichi Kamada ya yi bugun tazarar amma dai ba ta wuce masu tsaron bayan Brazil ba.

  16. Katin gargadi, Brazil 0-0 Japan

    An bai wa dan wasan Brazil, Casemiro katin gargadi sakamakon ketar da ya yiwa Junya Ito, an kuma bai wa Japan bugun tazara.

    Kenan Casemiro ba zai buga zagayen yan 16 ba da zarar Brazil ta kai zagayen gaba.

  17. , Brazil 0-0 Japan

    Matheus Cunha ya gwasa sa'a zuwa gidan Japan ko kwallon zai fada raga.

    Amma dai mai tsaron ragar Japan, Zion Suzuki bai da wata matsala da kwallon.

  18. Katin gargadi ga Japan, Brazil 0-0 Japan

    Kaishu Sano ya yiwa Vinicius Junior keta, kuma alkalin wasa ya busa ya kuma bashi kati mai ruwan dorawa.

  19. , Brazil 0-0 Japan

    Kwallon da da aka buga ta je wajen Danilo ya ja a guje daf da bakin lafi ya kuma shiga gidan Japan.

    Dama ce mai kyau da Brazil ta samu amma ba wani hadari sosai.

  20. , Brazil 0-0 Japan

    Brazil tana jin dadin yadda take da gagarumin rinjaye a taka leda a kan Japan a wannan karawar.