Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Haruna Ibrahim Kakangi da Muhammad Annur Muhammad

  1. Amnesty ta buƙaci kotun ICC ta daina jinkiri wajen binciken laifuka a yaƙi da Boko Haram

    Amnesty

    Asalin hoton, UNIAN

    Ƙungiyar Amnesty International ta kai kokenta ga alƙalan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC a madadin waɗanda aka yi zalinta domin daƙile yadda masu shigar da ƙara na kotun ke jan ƙafa wajen neman haƙƙin waɗanda aka yi wa laifi a Najeriya.

    A watan Disamban 2020 ne masu gabatar da ƙara na International Criminal Court (ICC) suka ce dukkan sharuɗa sun cika domin fara binciken laifukan da aka aikata a lokacin yaƙin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya tun daga 2010.

    Cikin laifukan har da waɗanda mayaƙan masu iƙirarin jihadi suka aikata, da kuma wanda ake zargin dakarun sojin Najeriya da aikatawa.

    Amnesty ta ce ya kamata ne a ce an kai buƙatar hakan ga alƙalai masu sauraren korafe-ƙorafe, idan sun amince sai a fara bincike.

    "Amma shekara huɗu ke nan har yanzu ofishin mai gabatar da ƙara a ICC bai gabatar da buƙatar ba," in ji Amnesty.

    A cewar shugaban Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi: "Waɗanda aka zalinta a Najeriya sun cancanci adalci kamar sauran waɗanda aka zalinta a wasu wuraren. Sun daɗe suna jira a yi musu adalci, bai kamata kotun ICC ta manta da Najeriya ba."

  2. Yadda aka ƙaddamar da allurar riga-kafin malaria a Najeriya

    Malaria

    Najeriya ce ƙasar da ke da kashi 27 na masu ɗauke da cutar malaria, da kuma kashi 31 na waɗanda cutar ta kashe a duniya, kamar yadda rahoton malaria na duniya na 2023 ya nuna.

    Kusan mutum 200,000 ne suka rasu a sanadiyar cutar malaria a bara, kuma yara ƴan ƙasa da shekara biyar da mata masu ciki suka fi saurin kamuwa.

    Ƙasar ta karɓi allurar riga-kafin malaria kawo na farko a watan Oktoba, sannan an fara allurar a yau Litinin a jihohi biyu - Bayelsa da Kebbi - kafin a faɗaɗa zuwa wasu jihohin nan da wasu watanni masu zuwa.

    Happiness Idia-Wilson, wadda ɗanta mai kimanin wata 11 a duniya ne farkon wanda aka fara yi wa allurar riga-kafin a Bayelsa, ta bayyana farin cikinta, tare da cewa ita ce ta nemi a yi wa ɗanta riga-kafin, "domin ya samu kariya," in ji ta, sannan ta ƙara da cewa, "zan wayar da kan iyaye mata don su kawo yaransu domin hakan ne zai sa a rage yawan cutar malaria."

    Malaria
    Maalria
  3. EFCC ta ƙwace unguwa guda daga wani tsohon jami'in gwamnati a Abuja

    EFCC

    Asalin hoton, EFCC/X

    Hukumar EFCC ta samu nasarar ƙwace kadara mafi girma a tarihinta, inda a ranar Litinin, 2 ga watan Disamban 2024, mai shari'a Jude Onwuegbuzie ya mallaka wa gwamnati wani rukunin gidaje, wanda aka gina a fili mai mai faɗin murabba'in ƙasa 150,500, mai ɗauke da rukunin gidaje 753 da wasu gine-ginen a Abuja.

    Wannan shi ne ƙwace kadara mafi girma tun bayan kafa hukumar EFCC a shekarar 2003.

    Kotu ta ƙwace rukunin gidajen ne mai lamba 109 a yankin Zone C09 da ke unguwar Lokogoma a Abuja, wanda kotun ta ce ta mallakin wani tsohon jami'in gwamnati ne, kamar yadda wata sanarwa da EFCC ta fitar ta nuna.

    Da yake hukunci kan ƙwace rukunin gidajen, mai sharii'a Onwuegbuzie ya ce wanda ake ƙara ya kasa gamsar da kotun abin da zai hana a ƙwace masa kadarar, "wadda ake zargin ya mallaka da kuɗaɗen da ya samu ta wasu hanyoyi zamba. Don haka an ƙwace kadarar, an kuma miƙa ga gwamnatin tarayya."

    Tun da farko, a ranar 1 ga watan Nuwamban 2024 ne kotun ta fara ƙwace rukunin gidajen na wucin-gadi, kafin yanzu ta ƙwace baki ɗaya.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ana cigaba da binciken jami'in gwamnatin

    Shugaban hukumar, Mr Ola Olukoyede, ya sha nanata cewa ƙwace kadarorin da aka mallaka ta hanyoyi marasa kyau na da matuƙar muhimmanci a yaƙi da cin hanci da rashawa.

  4. Mataimakin firaiministan Rasha ya ziyarci Nijar

    Nijar

    Asalin hoton, ORTN

    A jamhuriyar Nijar, mataimakin Firaministan Rasha ne ya ziyarci shugaban mulkin sojan ƙasar wanda ya tabbatar masa cewa Shugaba Vladmir Putin "ya ba da umarni na ƙarfafa dangantaka tsakanin Rasha da ƙasashen Afirka, musamman na ƙawancen ƙasashen Sahel da suka haɗa da Nijar, Mali da kuma Burkina Faso".

    A yayin da tawagar mataimakin firaministan Rasha ta kammala rangadin ƙasashen Sahel da jamhuriyar Nijar wasu ƴan ƙasar na fatan ganin talaka ya amfana da wannan hulɗa.

    Hakan dai na faruwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar koma bayan dangantaka da ƙasashen yamma waɗanda a baya aka fi dogaro kan tallafin da suke bayarwa.

  5. Mafi ƙarancin albashi: Gwamnan Ebonyi ya yi barazanar sallamar duk ma'aikacin da ya shiga yajin aiki

    Ebonyi

    Asalin hoton, Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru/Facebook

    Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi barazanar sallamar duk wani ma'aikacin da ya shiga yajin aiki nan da awa 72 idan bai koma aiki ba.

    Gwamna Nwifuru ya bayyana haka ne a ranar Litinin a ofishinsa da ke Abakaliki a lokacin da yake jawabi a game da yajin aikin da shugaban ƙungiyar ƙwadago na jihar, Kwamrade Comrade Oguguo Egwu ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    A ranar Lahadi ne Oguguo ya bayyana cewa yajin aikin biyayya ce ga umarnin shugaban ƙungiyar na ƙasa na ranar 8 ga Nuwamban 2024, inda ta yi kira ga ma'aikata a duk jihar da ba a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba su shiga yajin aiki.

    Nwifuru, ya ce majalisar tarayya ba ta ƙayyyade sabon albashi ba, inda a cewarsa dokar ta yi magana ne kan mafi ƙarancin albashi.

    "Na fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi tun a watan Oktoba, shi ya sa na yi mamaki da na ga sun fara yajin aiki. Kuma babu wani ma'aikaci da yake binmu bashin albashi, haka ma ƴan fansho.

    "Don haka duk wanda bai koma aiki ba nan da awa 72, zan sallame shi, in ɗauki wasu.

    Gwamnan ya ƙara da cewa ya bayar da umarnin a fara ɗaukar sunayen waɗanda suke zuwa aiki, sannan ya ce babu maganar zaman sulhu, "saboda kwamrade Egwu ba ma'aikacinmu ba ne."

  6. Iran za ta fara ayyana waɗanda ba su sa hijabi a matsayin masu 'babban laifi'

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar Iran ta amince da wani ƙuduri da ya sanya hukunci mai tsauri kan mata waɗanda ba su sanya hijabi - ko kallabi.

    Sabuwar dokar na nufin duk waɗanda aka ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, za a ci tarar ua daga dala 11 zuwa dala 100, wanda kwatankwacin albashin wata biyar ne - sannan a ayyana su a matsayin masu babban laifi.

    Dokar ta kuma ba ƴan ƙasar damar tilasta amfani da hijabi idan akwai buƙatar hakan.

    Sai dai ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Human Rights Watch ta ce dokar ta kama-karya ce.

  7. Jihohin Najeriya da 'yan ƙwadago suka shiga yajin aiki

    Takardar naira

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyoyin ƙwadago a wasu jihohin Najeriya sun tsunduma yajin aiki saboda rashin fara biyan naira 70,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi da gwamnonin jihohin suka yi.

    Matakin ƙungiyoyin biyayya ce ga wa'adin da gamayyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa wato Nigeria Labour Congress (NLC) ta saka na ranar 1 ga watan Disamba ga jihohi kusan 14 da ba su fara biyan sabon albashin ba ga ma’aikatansu.

    A ranar 29 ga watan Yulin 2024 ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tabbatar da sabon albashin bayan ya saka hannu kan dokar da aka yi wa kwaskwarima tare da alƙawarin za a dinga sake duba ta duk bayan shekara uku.

  8. Ƴan Sudan na ƙara fuskantar bala'o'i - MDD

  9. Joe Biden ya isa Cape Verde a ziyararsa ta farko Afirka

  10. Ƴansandan Najeriya sun gurfanar da ƴan ƙasashen waje kan zargin aikata laifi ta intanet

  11. Firaministan Georgia ya yi watsi da batun gudanar da sabon zaɓe

  12. Mutum 56 sun mutu a turmutsitsin filin ƙwallo a Guinea

  13. Joe Biden zai ziyarci Afirka a karon farko

  14. Jihohi biyu ne kaɗai za su amfana da sabuwar dokar harajin Najeriya - Zulum

  15. Yau za a a fara rigakafin cutar Maleriya a Najeria