Har yanzu Wiliiams na jin raɗaɗin da kasarsa ba za ta buga gasar kofin duniya ba, Gasar kofin duniya
Neco Williams ya amince cewa rashin zuwa buga gasar cin Kofin Duniya ta bana har yanzu yana ci masa rai, domin ya yi imanin Wales za ta iya yin tasiri a gasar da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Wales ta rasa damar zuwa gasar karo na biyu a jere bayan ta sha kashi a wasan neman cike gurbi a hannun Bosnia-Herzegovina.
Wannan rashin nasara ta fi taɓa zuciyar ɗan wasan baya na Nottingham Forest, Neco Williams, musamman ganin cewa shi ne ya kasa cin fenariti mai muhimmanci a karawar.
Sai dai duk da wannan ci gaba da takaici, ɗan wasan mai shekara 25 ɗin ya ce wasannin sada zumunta da Ghana da Romania a wannan mako su ne matakin farko na ci gaba da huce wannan raɗaɗi, yayin da tawagar ke mai da hankali kan gasar Euro 2028 da za a yi a gida.
Wasan da za su buga da Ghana a Cardiff ranar Talata zai zama abin tunawa da abin da suka rasa, domin Ghana na shirin shiga rukunin gasar World Cup ɗin da Ingila za ta kasance a ciki.

Asalin hoton, PA Media





