Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Rasha ta ce ta kakkaɓo jiragen Ukraine marasa matuƙa kusan 40

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ukraine ta ƙaddamar da wasu sabbin hare-haren jirage marasa matuƙa a wasu sassan ƙasar Rasha ciki har da Moscow babban birnin kasar.

    To sai dai magajin garin Moscow, Sergei Sobyanin ya ce Rasha ta kakkaɓo jiragen marasa matuƙa biyar a kusa da wata matatar mai a Moscow.

    Gwamnonin yankin sun ce kusan jirage marasa matuƙa 40 ne aka tarwatsa a Bryansk, da Voronezh (Vuh-ROH-nezh) da sauran yankunan.

    Sun ce ɓarnar da hare-haren suka yi ba ta da yawa, inda aka lalata cibiyoyin adana mai da kuma wasu muhimman gine-gine a wurare daban-daban.

    Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce ba kasafai Rasha ke bayyana irin girman ɓarnar hare-haren Ukraine ba.

  2. An gano gawarwakin mutum shida da Hamas ke garkuwa da su

    Hostages Families Forum

    Asalin hoton, Hostages Families Forum

    Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa gawarwakin mutum shida da aka gano a wani rami da ke birnin Rafah na Gaza na mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su ne a harin ranar 7 ga watan Oktoba.

    Ta bayyana sunayensu tare da cewa cikinsu akwai Ba'amurke wanda ya fito a wani bidiyon Hamas a watannin baya an yanke hannunsa.

    Shugaba Biden ya bayyana mutuwarsa a matayin abin takaici, yana mai cewa shugabannin Hamas za su ɗanɗana kuɗarsu kan abin da suka aikata.

    Kungiyar 'yan'uwan mutanen da ake garkuwa da su sun sake yin kira ga firaminista Benjamin Netanyahu ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

  3. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kada ku manta da tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.