An fara yi wa ƙananan yara allurar riga-kafin Polio a Gaza
Isra'ila ta ce an kashe 'yansandanta uku a Gaɓar Yamma
Rahoto kai-tsaye
Daga Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad
Rufewa
Jama'a masu
bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke
faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu
rufe shafin, yau Lahadi, 01 ga watan Satumba, 2024.
A madadin
kowa da kowa, Muhammad Annur Muhammad ke fatan za ku kasance da mu gobe Litinin - 02 ga watan Satumba, 2024..
Mu rufe da
wannan karin maganar da ke cewa - Raguwar tsanya ita ke fara tono.
Sojojin Najeriya sun ce sun halaka wani gawurtaccen ɗan bindiga a jihar Kaduna
Asalin hoton, NIGERIAN AIRFORCE
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar halaka wani gawurtaccen ɗan bindiga da ta jima tana nema a jihar Kaduna.
Rundunar ta ce ta halaka shi ne yayin da yake tafiya da wasu muƙarrabansa, bayan wasu bayanan sirri da ta samu, lamarin da ya sa ta tura dakarunta domin artabu da su.
Kakakin rundunar sojin saman Air Vice Mashal Edward Gabkwet, ya yi wa BBC ƙarin bayani, a yau Lahadi, inda ya ce an kashe mutumin ne, Mustapha Abdullahi, tare da wasu mutum biyar cikin yaransa, bayan da aka samu bayanan sirri kn zirga-zirgarsu a kusa d dajin Sabon Gida, da ke kan hanyar Sabon Birni a ƙarmar hukumar Igabi ta jihar ta Kaduna.
Ya ce, ''bayan da aka tura jami'an sojin saman ne su bincike yankin, suka haɗu da 'yan bindigar da ke kan babura, inda suka yi musayar wuta da su, inda sojin suka halaka su gaba daya.
AVM Gabkwet, ya ce kayan da aka samu a wajen 'yan ta'addar sun haɗa da bindigar gargajiy t maharba guda biyar, da bindiga mai sarrafa kanta kirar gida da harsasai da layu da ƙyastu (na kunna wuta) da layikan waya da kuma rigar wayoyin hannu.
An dawo da dokar hana shiga jirgin sama da abu mai ruwa a jakar hannu
Asalin hoton, Getty Images
An sake dawo da dokar hana ɗaukar wani abu mai ruwa a kayan hannu na fasinjojin jirgin sama a faɗin tarayyar Turai, zuwa wani ɗan lokaci.
Da an janye dokar ne a wasu filayen jirgin sama na ƙasashen tarayyar Turai bayan da aka samu cigaba a fasahar binciken kayayyakin fasinjoji, to amma kuma yanzu hukumar Turan ta ce an samu matsala da sabuwar na'urar binciken.
Hukuma ta ce wannan ne ya sa dole ta sake dawo da dokar.
Shekara goma sha takwas da ta gabata aka ɓullo da dokar, bayan wani yunƙuri na satar shiga jirgin sama da wani bam na ruwa, cikin jirgin transatlantic.
Dubban ƴan Isra'ila na zanga-zangar ƙyamar Firaminista Netanyahu
Asalin hoton, Reuters
Dubban ‘yan Isra’ila ne ke zanga-zanga a wajen ofishin firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu a birnin Kudus, suna bayyana shi a matsayin ‘mai kisan kai’, bayan da sojojin Isra’ila suka gano gawarwakin mutum shida da aka yi garkuwa da su a kudancin Gaza.
Sojojin sun ce Hamas ce ta kashe su.
Ana kuma gudanar da wasu manyan zanga-zangar a duk faɗin Isra'ilar, yayin da babbar ƙungiyar ƙwadago ta Histadrut, ta yi kira da a gudanar da yajin aikin gama-gari a yau Litinin, a wani yunkuri na tilasta wa gwamnatin ƙasar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Hamas.
Shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta Histadrut, Arnon Bar-David ya ce a maimakon a samu yarjejeniyar tsagaita wuta, sai ga shi Isra'ilawa na samun gawarwakin ƴan uwansu.
Jam'iyyar masu tsattsauran kishin farar fata ta kama hanyar cin zaɓe a Jamus
Asalin hoton, Getty Images
Sakamakon farko-farko na zaɓen Jamus, na nuna cewa jam'iyyar masu tsatstsauran ra'ayin riƙau da kishin farar fata, ta Alternative For Germany, na kan hanyar cin zaɓen jiha a karon farko.
Ana hasashen jam'iyyar za ta yi nasara a kusan kashi talatin da uku cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a jihar Thuringia.
A sauran zaɓukan na yau, Lahadi, kamar a jihar Saxony, sakamakon farko na nuna jam'iyyar ta AfD a matsayi ta biyu, bayan jam'iyyar Christian Democrats.
Jam'iyyar BSW ta masu sassaucin ra'ayi da aka kafa a kwana-kwanan nan na shirin zama ta uku a zaɓen.
Da alama jam'iyyar Social Democrats ta shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz ta share kashi biyar cikin ɗari na abun da ake buƙata don ci gaba da kasancewa a majalisun dokokin jihohin biyu.
Yanzu dai za a fara wani yunƙurin ƙawance mai cike da sarƙaƙiya bayan wallafa sakamakon a hukumance.
Da wuya jam'iyyar ta AfD ta iya kafa gwamnati, kasancewa jam'iyyu da dama sun nuna ba za su shiga ƙawance da ita ba.
Masu suka ku yi ta yi ko a jikina - El-Rufai
Asalin hoton, Kaduna Gov FB
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya mayar da martani ga waɗanda ke caccakarsa a shafukan sada zumunta da muhawara, yana mai cewa suka da zagin da suke yi masa ba su da makama.
Tsohon gwamnan ya ce ko lama bai damu da jirkita saƙonninsa da yi msu wata fassara ta daban da ake yi ba, da cewa masu yin hakan suna yi ne cikin jahilci da son-rai.
A jiya Asabar ne El-Rufai ya bayyana hakan a wani saƙo da ya sanya a shafinsa na X, yana mai cewa,''... abin da Allah Ya ƙaddara zai kasance, in sha Allah.”
Netizens sun yi ta caccakar tsohon gwamnan a kan wani saƙo da ya wallaf rnar Asabar da ta wuce, inda yake magana a kan ƙyashi da tsana a kan 'yan Najeriya.
Ya yi amfani da kasancewar matimkiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, a matsayin ƴar takarar jam'iyyar Democrat a matsayin misali na abin da yake nuni da ƙaddarar Ubangiji
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum arba'in a India
Asalin hoton, Gujarat Information/X
Mamakon ruwan sama ya yi sanadin mutuwar mutum goma a jihohin Andhra Pradesh da Telengana na kudancin India.
Mutum biyar daga cikinsu sun rasu ne sakamakon zaftarewar ƙasa a garuriuwa da dama.
Sufurin jirgin ƙasa da na motoci sun taƙaita kasancewar yankunan da ba a kan tudu suke ba, har yanzu ambaliya ta mamaye su.
A garin Vijayawada an yi ruwan sama mai yawan da ba a taɓa yi a cikin shekara ashirin.
Mutane d dama na garin sun ce sun rasa komai da suka mallaka, kuma ba su da abinci da ruwa mai tsafta.
An rufe makarantu a Hyderabad kuma jihohin da ke gaɓar ruwa na shirin tunkarar ƙarin ruwan sama a kwanakin da ke tafe.
Can a gaɓar yamma ta tekun ƙasar kuwa a Gujarat, sama d mutum 30 ne suka mutu, dubbai suk rasa muhalllinsu a sanadiyyar ambaliyar da mamakon ruwan sama na tsawon mako ɗaya ya haddasa.
An fara shigar da kayan agaji Sudan - MDD
Asalin hoton, Reuters
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da manyan motoci hamsin ɗauke da kayn agaji sun shiga Sudan ta wata muhimmiyar mashiga da ke kan iyaka da Chadi, wadda aka sake buɗewa kwananan.
Ofishin da ke tsara ayyukan jinƙai na majalisar ya ce akwi ƙarin wasu motocin 128 da za su shiga ƙasar ta wannan mashiga ta Adre a cikin makonnin da ke tafe
Motocin suna ɗauke da kayan agaji na kusan mutum dubu ɗari uku
Gwamnatin Sudan t rufe wnnan mashiga ne ta Adre a watan fabarairu bia zargin cewa ana kai wa mayaƙan RSF makamai.
Hotunan zanga-zangar Isra'ilawa a Birnin Ƙudus
An fara gudanar da zanga-zanga a biranen Ƙudus ta Tel Aviv a yau, yayin da mutanen a faɗin Isra'ila ke kiran gwamnatin ƙasar ta cimma yarjejeniya da ƙungiyar Hamas don gaggauta saki tare da maido da Isra'ilawan da ƙungiyar ke garkuwa da su a Gaza.
Nan hotunan wasu gungun jama'a ne da suka fara taruwa a wajen ofishin firaminista a Birinin Ƙudus.
Tun da farko Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatinsa ba za ta ''saurara'' ba har sai ta kama waɗanda suka kashe Isra'ilawa shidan da aka gano gawawakinsu ranar Asabar a Gaza.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Getty Images
Jagoran adawar Isra'ila ya yi kiran gudanar da ''yajin aikin gama-gari''
Asalin hoton, Reuters
Jagoran adawar Isra'ila, Yair Lapid ya yi kira ga mutanen ƙasar su fara ''babban yajin aiki'' da maraicen yau, domin matsa wa gwamnati lamba to amince da yarjejeniyar tsagaita wuta don sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
Tun da farko ƙungiyar iyalai da dangin mutanen da ake garkuwa da su, sun yi kiran gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar don neman firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu ya gaggauta ɗaukar mataki.
Mista Lapid ya yi kira ga kowane ɗan ƙasar da ya ce ''zuciyarsa ta sosu kan abin da ya faru'' ya fito zanga-zangar, inda ya yi kira na musamman ga ma'aikata da hukumomi da manyan ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar da su ''dakatar da tattalin arzikin ƙasar''.
Kiran na zuwa ne bayan da a ranar Asabar, sojojin ƙasar suka gano gawar mutum shida daga cikin mutanen da ake garkuwa bayan sun mutu.
'Za mu tsayar da Isra'ila cak ta hanyar yajin aiki da zanga-zanga'
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ko a ranar 15 ga watan Agusta ma sai da masu zanga-zangar suka fito a birnin Tel Aviv don neman sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su
Iyalan Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza sun yi kiran gudanar da yajin aiki a faɗin ƙasar, a wani mataki na tilasta wa gwamnatin Isra'ila cimma yarjejeniyar da za ta kai ga sakin mutanen.
Ƙungiyar iyalai da dangin mutanen da ake garkuwar da su, sun yi kira ga 'yan ƙasar su ''shiga gagarumar zanga-zangar da za su shirya, domin tsayar da komai a Isra'ila da tilasta wa gwamnati aiwatar da yarjejeniyar da za ta kai ga sakin 'yan'uwan nasu''.
Matakin na zuwa ne bayan da ranar Asabar sojojin ƙasar suka gano gawarwakin mutum shida cikin waɗanda aka yi garkuwar da su a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Ƙungiyar ta yi kiran gudanar da zanga-zanga a Tel Aviv, babban birnin ƙasar ranar Lahadi, sannan ta yi kira ga manyan ƙungiyoyi masu faɗa-a-ji na ƙasar su shiga zanga-zangar, kamar yadda kamfanin diallancin labarai na AFP ya ruwaito.
Tuni dai wasu ƙungiyoyin 'yan kasuwa suka bayyana aniyar shiga yajin aiki, ciki har da ƙungiyoyin masu gidajen sinima da gidajen cin abinci, waɗanda suka ce za su rufe ayyukansu a ranar Lahadi da maraice domin nuna goyon bayansu.
Ambaliya ruwa: Gwamnan Zamfara ya bai wa mutanen Gummi tallafin naira miliyan 100
Asalin hoton, Zamfara State Government
Bayanan hoto, Gwamnan Zamafara da sarkin Gummi
Gwamnan jihar Zamafar Dauda Lawal Dare ya bai wa al'ummar yankin Gummi da suka fuskanci bala'in ambaliya tallafin naira miliyan 100.
Cikin wata sanarwa da sakatare yaɗa labaran gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce gwamnan ziyarci garin Gummi ranar Asabar, domin jajanta wa mutanen da bala'in ambaliyar ta shafa.
Garin Gummi ya fuskanci mummunar ambaliya a 'yan kwanakin baya-bayan nan , lamarin da ya haddasa asarar dukiya mai dimbin yawa.
Dauda Lawal ya ce ya je garin ne domin jajanta wa mutanen garin kan abin da ya faru.
Gwamnan ya kuma kai musu kayayyakin tallafi domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi a lokacin ambaliyar.
“Ina so na yi amfani da wannan damar don sanar da ku cewa na ba ku tallafin buhu 10,000 na abinci da ya haɗa da shinkafa da masara da gero domin raba wa mutane da bala'in ya shafa. Haka kuma a madadin gwamnatin jihar Zamfara na bayar da tallafin naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ta shafa'', in ji shi.
Gwamnan ya kuma ƙara da cewa gwamnati za ta bai wa mutanen da ambaliyar ta shafa filaye a wuraren da ba su da hatsarin ambaliya domin sake gina gidajensu.
Gwamnatin Bauchi ta naɗa Haruna Ɗanyaya sabon sarkin Ningi
Asalin hoton, Galaje_Lenses
Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da naɗin Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin sabon sarkin Ningi.
Sanarwar naɗin na ƙunshe cikin wata wasiƙa da sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Mohammed Kashim ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan jihar, Bala Mohammed ne ya amince da naɗin sabon sarkin.
Alhaji Haruna Yunusa Ɗanyaya shi ne babban ɗa ga marigayi sarkin Bauchi na 16, Alhaji Yunusa Ɗanyaya.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar Bauchi na da ƙwarin gwiwa kan sabon sarkin zai ci gaba da wanzar da zaman lafiya da haɗin kai da ci gaban masarautar da ma jihar baki ɗaya, kamar yadda mahaifinsa yake yi a baya.
Mawaƙin siyasa Garba Gashua ya rasu
Asalin hoton, Family
Fitaccen marubucin waƙoƙin Hausa da na siyasa, Garba Gashua ya rasu.
Babban ɗan marigarin, Musa Garba Gashua ne ya tabbatar wa BBC rasuwar tsohon mawaƙin, wanda ya rasu a ranar Lahadi da asuba, yana da shekara 73 a duniya.
Garba Gashua ya yi fice a waƙoƙin siyasa musamman a lokacin jamhuriya ta uku a Najeriya, daga zamanin mulkin Babangida zuwa lokacin siyasar SDP da NRC.
Tuni aka yi jana'izar marigayin - wanda ya mutu ya bar 'ya'ya 11 da jikokki da dama.
Hotunan yadda ake yi wa yaran Gaza riga-kafin Polio
Asalin hoton, EPA
Wata ma'aikaciyar jinya a Gaza da ke taimakawa wajen gudanar da allurar Polio a tsakiyar Gaza ta ce tun da safe ake samun fitowar ƙananan yara masu yawan gaske domin karɓar allurar.
An ƙiyasta yi wa yara 1,000 allurar yau a cibiyar riga-kafin a asibitin Rewaa Mohsen da ke Deir al-Balah.
Asalin hoton, Reuters
Ta shaida wa BBC cewa ƙananan yara sun cika cibiyar da take aikin allurar.
Asalin hoton, Reuters
Ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara 10 ne za a yi wa riga-kafin, har karo biyu cikin mako huɗu, kamar yadda jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke jagorantar allurar suka bayyana.
Asalin hoton, EPA
An tanadi aƙalla allurar riga-kafin miliyan 1.26 a Gaza, yayin da ake sa ran samun ƙarin allura 400,000.
Hukumar Lafiya ta Duniya ce dai ke jagorantar riga-kafin, bayyan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas
Wike ya yi barazanar haifar wa gwamnonin PDP rigima a jihohinsu
Ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike, ya sha alwashin haifar wa gwamnonin PDP matsaloli a jihohinsu idan ba su janye hannunsu daga rikicin siyasar jihar Rivers ba.
Wike ya bayyana haka ne ranar Asabar lokacin da yake jawabi a taron jam'iyyar PDP a jihar Rivers da aka gudanar a birnin Fatakwal.
Mista Wike dai na taƙun saƙa da gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara kan jagorancin jam'iyyar PDP a jihar.
A makon da ya gabata ne dai gwamnonin PDP suka fitar da sanarwa bayan taro, wadda shugabansu - gwamnan Bauchi, Bala Mohammed - ya karanta, inda ya ciki ya ce ƙungiyar gwamnonin PDP ta jaddada goyon bayanta ga gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.
To sai dai a martanin da ya mayar, Ministan na Abuja ya zargi gwamnonin da yunƙurin ƙwace jam'iyyar daga hanunsa, abin da kuma ya ce ba zai saɓu ba.
“Ina son tabbatar muku cewa, ba wai ba za mu bari wani ya ƙwace PDP daga hannunmu ba ne, a a bari na gaya muku, na ji wasu gwamnoni na cewa za su ƙwace jam'iyyar su bai wa wani, to ina tausaya wa waɗannan gwamnoni, domin zan kunno musu wutar da ba za iya kashe ta ba a jihohinsu'', in ji shi.
“Idan Allah ya wanzar maka zaman lafiya a jiharka, kuma ka ce ba ka buƙatar zaman lafiyar, to duk abin da kake so za ka samu, domin kuwa masu iya magana na cewa kowa ya kwana lafiya shi ya so,” in ji Wike.
Tsohon gwamnan Rivers ya ce saboda gwamnonin na ganin wuyansu ya yi kauri, saboda wasu kuɗin da ya ce sun tara, shi yasa suke ƙoƙarin sa bakinsu a jiharsa, ''To ku shirya ni ma ina da jan wuyan da zan iya yi muku hakan a jihohinku''.
Isra'ila ta ce an kashe 'yansandanta uku a Gaɓar Yamma
Asalin hoton, Reuters
Hukumomin Isra'ila sun ce an kashe 'yansandan ƙasar uku - maza biyu , mace guda - bayan an harbi motar da suke ciki a kusa da birnin Hebron da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ilar ta mamaye.
Yayin da yake jawabi a wurin da aka yi harbin, kwamishinan 'yansandan ƙasar, Daniel Levy ya ce jami'an da aka harbe na aiki ne a gundumar 'Judea da Samaria', kalmar biyibul da Isra'ila ke kiran Gabar Yamma da Kogin Jordan.
Biyu daga cikin jami'an sun mutu nan take a wurin da lamarin ya faru a kusa da mashigar Tarkumiya, yayin da gudan ya cika daga baya a asibiti.
Wasu sassan Gaɓar Yamma - da ke ƙarƙashin mamayar Isra'ila tun lokacin yaƙin Gabas ta Tsakiya na 1967 - sun kasance wuraren da ake yawan kai hare-hare, inda kuma a makon nan Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran dakatar da hare-haren.
Muna so gwamnatin Najeriya ta janye dokar ƙayyade shekarun kammala sakandire - SSANU
Ƙungiyar manyan malaman jamai'o'i ta Najeriya, (SSANU), ta yi kira ga gwamnatin ƙasar ta dakatar da shirin ma'aikatar ilimin ƙasar na taƙaita shekarun rubuta jarrabawar kammala sakandire a ƙasar.
A baya-baya nan ne ministan Ilimin ƙasar, Farfesa Tahir Mamman ya ce babu yaron da za a sake bari ya rubuta jarrabawar kammala sakandire ba tare da ya cika shekara 18 da haihuwa ba.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin shirya jarrabawar kammala sakandire na WAEC da NECO su sanya dokar cikin sharuɗansu na yi wa ɗalibai rajista.
To sai ƙungiyar SSANU ta bayyana matakin da koma-baya tare da haifar wa ɗalibai da iyayensu wasu sabbin matsaloli.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron ƙungiyar a Abuja, shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta janye matakin tare da sake tuntuɓar masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi domin kauce wa haifar da matsaloli a fannin ilimin ƙasar.
Tun bayan sanar da sabon matakin ne dai, yake shan suka daga mutane da ƙungiyoyi da dama, a ƙasar, ciki har da jagoran adawar ƙasar Atiku Abubakar, wanda ya ce matakin zai daƙushe ɗalibai masu hazaƙa da fikira.
An fara yi wa ƙananan yara allurar riga-kafin Polio a Gaza
Asalin hoton, Reuters
Dubban ƙanannan yaran Falasɗinawa sun fara karɓar allurar riga-kafin cutar Polio a yankin Gaza.
Majalisar Dinkin Duniya ce ke jagorantar aikin riga-kafin da aka ƙiyasta yi wa ƙananan yara kusa 600,000 a faɗin Gaza.
Isra'ila da ƙungiyar Hamas duka sun amince da tsagaita wuta a lokacin riga-kafin domin bai wa ma'aikatan lafiya damar gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali.
A baya-bayan nan ne Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta tabbatar da ɓullar cutar Polio a Gaza karon farko cikin shekara 25.
Chidimma Adetshina ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Najeriya ta 2024
Asalin hoton, FAWAZ OYEDEJI / AFP
Chidinma Adetshina daga jihar Taraba ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Najeriya ta shekarar 2024, bayan doke abokan takararta 24.
Ms Adetshina ta zama gwarzuwar gasar ne a bikin zaɓen sarauniyar kyau da aka gudanar ranar Asabar a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Matashiyar mai shekara 23, a baya-bayan na ta shiga kanun labarai sakamakon janyewarta daga shiga gasar sarauniyar kyau ta Afirka ta Kudu, saboda ce-ce-ku-cen da aka samu kan kasancewar asalinta 'yar Najeriya.
A yanzu sabuwar sarauniyar kyawun, za ta wakilci Najeriya a babbar gasar sarauniyar kyau ta duniya da za a gudanar a ƙasar Mexico nan gaba cikin wannan shekara.