Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/06/2025

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed

  1. 'Harin Amurka ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa'

    Seyed Ali Mousavi

    Jakadan Iran a Birtaniya, Seyed Ali Mousavi, ya bayyana cewa harin da Amurka ta kai Iran ya "saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa".

    Ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da BBC, sai dai ya ki cewa uffan lokacin da aka tambaye shi kan irin ɓarnar da harin ya yi kan cibiyoyin nukiiyar Iran.

    Ya ce hare-haren sun kuma saɓa wa ƴancin ƙasar Iran.

    Wakiliyar BBC Laura Kuenssberg ta tambaye shi ko Iran za ta yi watsi da shirinta na nukiiya da kawo karshen rikicinta da Isra'ila idan Amurka ta sake far mata.

    Mousavi ya ce Iran da Amurka na cikin tattaunawa kan shirin nukiliya kafin "Isra'ila ta far mana".

  2. Hukumar da ke sa-ido kan makaman nukiliya za ta yi taron gaggawa

    IAEA

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar da ke sa ido kan makaman nukiiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, IAEA, ta ce za ta gudanar da taron gaggawqa a gobe Litinin "kan halin da ake ciki a Iran", a cewar shugaban hukumar.

    A ɗaya gefen, shugaban nukiliyar Iran Mohammad Eslam ya rubuta wasika zuwa ga IAEA, inda ya ce Tehran na son a yi bincike kan hare-haren Amurka - inda ya buƙace ta da ta yi Alla-wadai da lamarin, a cewar kafofin yaɗa labaran Iran.

    Tun da farko, IAEA ta tabbatar da cewa babu wani "ƙarin hatsarin watsuwar sinadarai" bayan hare-haren da Amurka ta kai cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku.

  3. Za a fara yanke wa masu garkuwa hukucin kisa ta hanyar rataya a Ondo

    Ondo

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin jihar Ondo ta sanar da cewa daga yanzu za ta fara yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane.

    Babban attoni janar na jihar, Kayode Ajulo shi ya bayyana haka a birnin Akure ranar Asabar bayan taron majalisar zartaswa na jihar.

    Ya bayyana cewa za a rushe duka gine-gine da kuma wurare da masu garkuwa ke amfani da su wajen aikata laifuka bayan samun umarnin kotu, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Ajulo ya ƙara da cewa za a yi wa dokar yaƙi da ayyukan masu garkuwa a jihar garambawul, domin saka batun hukuncin kisa ta hanyar rataya a cikinsa.

    Ya ce sun kuma damu kan ƙaruwar ayyukan ƙungiyoyin asiri a jihar, inda ya ce za su yi duk abin da ya kamata wajen magance batun.

    Ondo ta bi sahun jihar Edo wadda ta bijiro da irin wannan hukunci ga masu garkuwa a watan Afrilu, da nufin magance matsalar garkuwa da ta yi kamari.

  4. An samu fashewar abubuwa a birnin Tel Aviv bayan harin Iran

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    An shiga ruɗani a yankuna da dama na Isra'ila yayin da sojoji suka ce sun gano makamai masu linzami da aka harba daga Iran.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce na'urorin tsaronta na sama na aiki don daƙile barazanar amma an shawarci jama'a da su fake har zuwa wani tsawon lokaci.

    An samu rahotannin fashewar abubuwa a sararin samaniyar birnin Tel Aviv da kuma birnin Kudus.

    Isra'ila da Iran sun ci gaba da kai wa juna hare-hare ta sama a 'yan kwanakin da suka gabata amma wannan sabon harin na zuwa ne bayan da Amurka ta kai hari kan wasu muhimman cibiyoyin nukiliya guda uku a Iran.

  5. 'Kwanaki da ke tafe za su kasance masu wahala' - shugaban Isra'ila

    Herzog

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Isra'ila ya fitar da sanarwa, inda ya kwatanta harin da Amurka ta kai wa Iran a matsayin "abin tarihi".

    Isaac Herzog ya ce kalaman Trump sun nuna "tsantsar haɗin-kai" tsakanin Amurka da Isra'ila.

    Sai dai ya yi gargaɗin cewa "yaƙin bai kare ba", inda ya ƙara da cewa "kwanaki masu zuwa za su kasance masu wahala", ya kuma buƙaci Isra'ilawa da su riƙa bin matakan kariya daga wajen hukuomi.

  6. Abin da muka sani kan hare-haren da Amurka ta kai a cikin Iran

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce jiragen yaƙin Amurka sun jefa bama-bamai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lamarin da ya ƙara girman yaƙin da ke gudana tsakanin Isra'ila da Iran.

    Ɗaya daga cikin cibiyoyin da aka kai wa harin ita ce Fordo, wata cibiyar inganta makamashin uraniun wadda ke ɓoye a ƙarƙashin ƙasa, wadda kuma ke da matuƙar muhimmanci ga shirin nukiliyar Iran.

    Ya zuwa yanzu ba mu san irin ɓarnar da harin na Amurka ya yi wa cibiyar ba.

  7. Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran

    Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ƙasarsa ta kai wasu hare-hare kan muhimman cibiyoyin nukiliya guda uku da ke cikin Iran.

    A lokacin da yake jawabi a fadar White House, ya ce hare-haren da za a kai nan gaba za su fi yawa kuma za su fi muni matukar Iran ba ta nemi sasanci ba.

    "Mun tarwatsa duka muhimman cibiyoyin makamasin nukiliya na Iran, kuma yanzu ya zame mata dole ta nemi a yi sulhu don kawo karshen hare-haren," in ji Trump.

    Trump ya taya firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu murna, ya kuma ce sun yi aiki tare don kawar da abin da ya bayyana a matsayin mummunar barazana ga Isra'ila.

  8. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Lahadi.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.