Muna ci gaba da samun martani daga ƙasashen duniya kan harin da Amurka ta kai cibiyon nukiliyar Iran.
Ƙasashen Larabawa ma ba a bar su a baya ba, ga abin da suke cewa:
Oman, wadda ke shiga tsakani a tattaunawar Amurka da Iran kan shirin nukiiyar Tehran, ta yi ƙaƙƙausar suka tare da Alla-wadai kan hare-haren na Amurka kan cibiyoyin nukiliyar Iran.
Ƙasashen yankin Gulf "sun nuna matukar damuwa, da Alla-wadai kan harin Amurka da kuma barazanar bazuwar rikicin da harin zai haifar".
Saudiyya, wadda ke da alaƙar tsaro mai ƙarfi da Amurka da kuma ta kasance ƙawarta, ta yi "Alla-wadai da saɓa wa ƴancin ƙasar Iran da kuma buƙatar a kai zuciya nesa", inda ta yi kira ga al'ummomin ƙasashen waje da su "ƙara ƙaimi domin ganin an samu mafita na warware rikicin".
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta yi gargaɗin cewa "zaman ɗar-ɗar sakamakon rikicin zai haifar da babban bala'i a yankin da kuma ƙasashen duniya." Ta ce tana "fatan dukkan ɓangarori za su kai zuciya nesa a daidai wannan lokaci."
Masar ta yi gargaɗin cewa rikicin "zai janyo babban bala'i da kuma ruɗani a yankin," inda ta nanata cewa "tattaunawar diflomasiyya ita ce kaɗai hanyar fita daga wannan rikici, ba ɗaukar matakin soji ba".
A ɗaya gefen, shugaban Lebanon Joseph Aoun ya ce "kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran ya janyo fargabar da ake da ita na bazuwar rikicin wanda zai haifar da rashin tsaro da kuma ɗorewar yankin".