Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye : Batun takarar Tinubu tare da Kashim da hare-haren Benue
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Yadda batun takarar Tinubu tare da Kashim ya fara jefa APC cikin ruɗani
Tun farkon makon ne aka batun tazarcen shugaba Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima a matsayin mataimaki, lamarin da ya fara jefa jam'iyyar APC cikin ruɗani bayan abin da ya faru a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a shiyyar arewa maso gabas.
An samu ruɗani a taron da shugabannin yankin suka gudanar a ƙarshen mako a jihar Gombe bayan da shugabannin jam'iyyar APC na ƙasa suka ambaci shugaba Tinubu shi kaɗai a matsayin wanda za iyi wa APC Takara a zaɓen 2027 ba tare da ambatar mataimakinsa ba Kashim Shettima.
Matakin ya haifar da yamutsi a zauren taron, lamarin da ya sa har ta kai ga ba wa hammata iska a taron wanda ya ƙunshi shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje da gwamnonin yankin na jam'iyyar APC da ministoci da tsaffin gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar.
Abubuwan da ba ku sani ba kan hare-haren Benue da suka kashe gomman mutane
Haka kuma a farkon makon an wayi gari da wasu jerin hare-haren ƴanbindiga da suka hallaka mutane da dama a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
Hukumomi a Najeriya sun ce hare-haren sun halaka fiye da mutum 100, yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki, ana sa ran adadin zai zarta haka.
Jihar Benue na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi ƙaurin suna wajen rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya.
Hare-haren baya-bayan nan biyu da aka kai ranar 13 da 14 ga watan Yuni sun tayar da hankalin ƴan ƙasar, lamarin da ya sa shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta kawo ƙarshen rikicin.
Miƙa wuyar ƴanbindiga a Katsina
A makon ne kuma wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar hukumar Dan Musa ta jihar Katsina sun ajiye makamansu tare da sakin mutum 16 da suka yi garkuwa da su.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ta ce matakin na cikin wani shiri na ci gaba da karɓar makamai da ficewa daga harkar aikata laifuka wanda rundunar Operation Fasan Yamma ke jagoranta tare da hadin gwiwar hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.
Jagororin 'yan bindigar da suka miƙa wuya sun haɗa da Kamulu Buzaru da Manore da Nagwaggo da Lalbi da Alhaji Sani da Dogo Baidu da Dogo Nahalle da Abdulkadir Black.
Jita-jitar Namadi ya koma APC
Haka kuma a cikin makon ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC, yana mai jaddada cewa har yanzu shi mamba ne na jam'iyyar PDP.
A wata sanarwa da tsohon mai taimaka masa a harkar yaɗa labarai, Umar Sani, ya fitar, Namadi Sambo ya bayyana jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya mai cike da ruɗani da kuma wata don ɓatar da jama'a.
Sanarwar ta bayyana cewa hoton da ke yawo da ya tayar da wannan jita-jitar wanda ke nuna Sambo tare da gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, tsohon hoto ne da aka ɗauka shekaru da suka wuce a lokacin da gwamnan ya kai masa ziyara ta jaje a gidansa da ke Abuja, bayan rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sani Sambo.
"Wasu na ƙoƙarin amfani da hoton domin yaudarar jama'a da ƙirƙirar labarin da bai da tushe ne kawai." Sanarwar ta ƙara da cewa
Gurfanar da Sanata Natasha a kotu
A makon ne kuma dai wata kotu a Abuja ta bayar da belin Sanata Natasha kan naira miliyan 50 tare da ɗaga shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Satumba.
Gwamnatin Najeriya ce ta shigar da ƙarar Sanata Natasha bisa zarge-zarge uku da suka ƙunshi zargin ɓata sunan shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanat Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Barazanar Lakurawa a jihar Kebbi
Haka kuma a cikin makon mayaƙan ƙungiyar nan ta Lakurawa sun gargaɗi al'ummomin garuruwa fiye da goma na yankin ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi, a kan su yi watsi da dabarar sayar da shanun huɗa suna sayen wasu na'urorin zamani na huɗa da ke amfani da man fetur.
Mayakan sun ce za su halaka duk wanda ya ki jin gargadin nasu.
Manoman dai kan sayar da shanun su sayi na'urorin huda saboda tsoron da suke yi, cewa 'yan bindigar suna sace musu dabbobi.
Kashedin da ake zargin 'yan kungiyar ta Lakurawa sun yi wa jama'ar garuruwan, ya jefa fargaba da zaman dar-dar ga mutanen yankin.
Ziyarar Tinubu a Kaduna
Haka kuma daga cikin abubuwan da suka ɗauki hankali a makon akwai ziyarar da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kai a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Tinubu na ziyarar ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Sanat Uba Sani ya aiwata tsawon shekara biyu da ya shafe yana mulkin jihar.
Cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar sun haɗa da wani asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya.
Haka kuma shugaban ya ƙaddamar da cibiyar koyar da sana'o'i, sai kuma motocin safa masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100.
Neman rajistar sabuwar jam'iyyar adawa a Najeriya
A ranar Juma'ar makon ce kuma jagororin jam'iyyun hamayya na Najeriya a ƙarƙashin inuwar gamayyar jam'iyyun hamayya ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam'iyyar da za su yi amfani da ita domin fafatawa da jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
Tuni NNCG ta miƙa takardar neman rajistar jam'iyya ga Hukumar INEC a hukumance.
Wasiƙar wadda suka aika zuwa ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa tare a ranar 20 ga Yunin.
A wasiƙar, sun rubuta cewa, "muna neman INEC ta amince da buƙatarmu ta yi wa ƙungiyarmu ta All Democratic Alliance ta zama jam'iyyar siyasa."