Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/06/2025

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin, nan muka kawo ƙarshen labaran da muke kawo muku na kai-tsaye a wannan rana ta Lahadi.

    Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya nuna mana.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Shugaban mulkin soji na Mali ya ziyarci Rasha

    Mali

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban mulkin soji na Mali, Assimi Goita ya kai ziyara Moscow, lamarin da ya zo a daidai lokacin da mayaƙa suke cigaba da kai hare-hare kan sojojin ƙasar.

    Wannan ne karo na biyu da Goita ya kai ziyara ƙasar Rasha bayan ziyarar da ya kai domin halartar taron ƙasashen Afirka da Rasha da aka yi a birnin St. Petersburg a bara.

    Shugaban ya isa Moscow ne a ranar Lahadi, a wata ziyara da ministoci da wasu jami'an gwamnati suka raka shi domin ganawa da takwarorinsu na Rasha.

    Ana tunanin Mali za ta tattauna tare da shiga yarjejeniya kan wasu muhimman ɓangarori da suka haɗa da makamashi da tattalin arziki da haɗakar soji da sauransu.

  3. Isra'ila ta kai hari a lardin Bushehr na Iran

    Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a cikin Iran, kamar yadda kafar yaɗa labaran gwamnatin Iran ɗin ta bayar da rahoton wata babbar fashewa a lardin Bushehr da ke kudu-maso-yamma, inda tashar samar da lantarki ta nukiliya ɗaya tilo ta ƙasar take.

    Hukumar kula da nukiliya ta duniya, IAEA, a baya ta yi gargaɗin cewa, idan aka kai hari wannan tasha, ta Bushehr, hakan zai iya janyo fitar tururin nukiliya mai yawan gaske.

    Rundunar sojin saman Isra'ila ta ce jiragen yaƙinta sun kuma kai hari kan wata hedikwatar ƙananan jiragen sama na yaƙi marasa matuƙa a yankin Yazd da ke tsakiyar ƙasar ta Iran da kuma wasu wuraren da ta ce cibiyoyi ne na soji da ke Isfahan da Ahvaz.

    A nata ɓangaren kuwa can a Isra'ila kusan mutum tamanin ne suka ji rauni bayan da makamai masu linzami na Iran suka keta garkuwar sama ta Israilar suka faɗa ƙasar.

  4. Harin ƙunar baƙin wake a Coci ya yi ajalin aƙalla mutum biyar a Syria

    Syria

    Asalin hoton, EPA

    Masu aikin ceto sun ce aƙalla mutum biyar ne suka rasu a sanadin wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai a wani coci da ke gabashin garin Dweila a babban birnin ƙasar, Damascus.

    Ministan harkokin cikin gida na ƙasar ya ce maharan ƴan ƙungiyar IS ne.

    Jami'an tsaro sun kwashe gawarwakin waɗanda suka rasu daga cocin mai suna Mar Elias, amma har yanzu ba su fitar da adadin waɗanda suka mutu ba a hukumance.

    Wannan harin zai zama babbar koma-baya ga shugaban ƙasar Ahmed al-Sharaa wanda ya ɗauki alƙawarin kare marasa rinjayen ƙasar bayan yawaitar rikice-rikice ƙabilanci a ƙasar.

    A farkon wannan shekarar ne aka riƙa samun kashe-kashen ƴan ƙabilar Alawy, ta tsohon shugaban ƙasar, Bashae al-Assad, wanda kuma aka zargi ƴan sunni masu goyon bayan gwamnati da aikatwa.

  5. An gargaɗi makiyaya su guji aikata miyagun ayyuka

    Makiyaya

    Asalin hoton, Kulen Allah

    Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Kullen Allah ta gudanar da wani taro a wani daji da ke kusa da garin Gudugurka da ke ƙaramar hukumar Funai ta jihar Yobe, inda ta wayar da kan makiyaya tare da kira gare su da su guji aikata miyugun ayyuka.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce taron ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar Yobe Chiroma Buba, wanda ya wakilci gwamnatin jihar.

    "An kira taron ne domin a yi nasiha da gargaɗi ga makiyayan jihar Yobe a kan su yi wa ƴaƴansu nasihar zaman lafiya don su guje wa shaye-shaye da aikata abubuwan da za su kawo illa ga zaman lafiyar jihar Yobe da ma ƙasa baki ɗaya."

    Haka kuma an gargaɗi makiyayan da su guje wa dukkan miyagun ayyuka da za su kawo tashin hankali a jihar, da ma ɓata sunansu.

  6. Gwamnonin arewa sun bayyana takaicinsu kan kisan matafiya a Filato

    Inuwa

    Asalin hoton, @GovernorInuwa

    Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 sun nuna takaicinsu kan kisan da aka yi wa wasu matfiya ƴan Kaduna a jihar Filato, lamarin da suka bayyana da kisan gilla, sannan suka yi kira da a gaggauta ɗaukar mataki.

    A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito daga shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ƙungiyar ta yi Allah-wadai da kisan.

    "Irin wannan kisan gillan bai dace na, kuma ba za ta saɓu ba. Ina jajanta wa ƴan jihar Kaduna, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa."

    Gwamnan ya ƙara da cewa dole a nemo waɗanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci, "domin hakan zai tabbatar da adalci," in ji shi.

    A ƙarshe gwamnan ya yi kira ga mutanen jihohin Kaduna da Filato da su kai zuciya nesa, "a guji ɗaukar doka a hannu domin hukumomi su samu damar yin abin da ya dace."

    A daren ranar Juma'a ne aka kashe mutum 13 daga cikin matafiya 31 a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan'uwansu.

  7. Hare-haren Amurka kan Iran na barazana ga zaman lafiya a duniya - MDD

    MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku a matsayin wani lamari da ke barazana kai tsaye ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

    Ƙasashen da ke kawance da Iran da suka hada da Venezuela da Cuba su ma sun soki hare-haren na Amurka.

    A Amurkan 'yan jam'iyyar Republican da dama sun fitar da sanarwar goyon bayan matakin na Donald Trump.

    Sai dai, wasu 'yan jam'iyyar Democrat da Sanata mai zaman kansa Bernie Sanders sun ce matakin da Mr Trump ya dauka na kai wa Iran hari ya sabawa kundin tsarin mulkin ƙasar.

    Yana daga cikin ‘yan majalisar da suka ce shugaban na bukatar amincewar majalisar dokoki kafin kaddamar da irin wadannan hare-haren.

  8. Wane martani Iran za ta mayar bayan harin Amurka?

    Iran

    Asalin hoton, EPA

    Da Benjamin Netanyahu ya fito domin jawabi game da halin da ake ciki a game da yaƙin da suke yi da Iran a ofishinsa na firaminista a safiyar yau, an riga an samu labarin harin Amurka da ya kawo sauyi dangane da yaƙin.

    Ya yi jawabin ne da Ingilishi, inda ya fito ƙarara ya yaba wa Amurka da shugabanta Donald Trump bisa ɗaukar matakin kai hari a sansanonin nukiliyar Iran.

    Maganar Netanyahu ta kasance cike da farin ciki, musamman ganin a tsawon lokacin da ya yi yana harkokin siyasa, ya kasance cikin yawan nanata maganar barazanar da Isra'ila ke fuskanta daga Iran.

  9. RHDP ta amince Ouattara ya tsaya takarar shugaban Ivory Coast karo na huɗu

    Ouattara

    Asalin hoton, AFP

    Jam'iyya mai mulki a ƙasar Ivory Coast wato Rally of Houphouetists for Democracy and Peace (RHDP) ta sake tsayar da shugaban ƙasar Alassane Ouattara domin tsaya takara a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

    Babbar jam'iyyar ta ɗauki wannan matakin ne kwana biyu bayan manyan jam'iyyun hamayya biyu na ƙasar sun yi haɗaka domin fafatawa a zaɓen.

    Sai dai har yanzu Mr. Ouattara bai sanar da shirinsa na tsayawa takara ba, amma magoya bayansa sun ce dole ya amince ya yi takarar domin neman shugabantar ƙasar karo na huɗu.

    Shugaban kamfe na jam'iyyar, Patrich Achi ne ya bayyana buƙatar ayyana Ouattara a matsayin ɗantakara, sannan wakilan jam'iyyar suka amince a wani taro da suka yi a ranar Asabar, wanda shugaban bai samu halarta ba.

    Amma ana tunanin Ouattara zai yi jawabi ga magoya bayansa a wani gangami da za a yi gobe Lahadi a filin wasan Ebimpe.

    Sai dai manyan jam'iyyun hamayya na ƙasar - African People’s Party (PPA-CI) da ke ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo, da Democratic Party of Ivory Coast (PDCI) da ke ƙarƙashin jagorancin tsohon ma'aikacin banki Tidjane Thiam - suna fuskantar ƙalubale, kasancewar an haramta wa jagororinsu tsayawa takarar a zaɓen wanda za a yi a ranar 25 ga watan Oktoba.

  10. Majalisar Iran ta amince da rufe mashigar Hormuz

    mashigar Hormuz

    Asalin hoton, Stocktrek / Getty Images

    Majalisar dokokin Iran ta kaɗa kuri'ar amincewa da rufe mashigar Hormuz.

    Wani babban ɗan majalisar ƙasar ya bayyana a ranar Lahadi cewa sun amince da batun rufe mashigar, wanda shi ne hanyar dakon man fetur mafi muhimmanci a duniya a matsayin martani ga harin da Amurka ta kai wa ƙasar.

    Ɗan majalisar ya ce sauran mambobin majalisar sun amince da batun, duk da cewa majalisar tsaron ƙasar ce ke da ikon yanke hukunci na karshe.

    Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.

  11. Ƙasashen Afirka 10 da suka fi girman kasafin kuɗi a 2025

    Kuɗi

    A makon da ya gabata ne wasu ƙasashen Afirka uku suka gabatar tare da amince da kasafin kuɗinsu na shekarar da muke ciki, a wani mataki na bunƙasa tatattalin arzikin ƙasashen.

    Ƙasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda sun gabatar da kasafin kuɗin da ya mayar hankali kan zaɓuka da tattalin arzikin ƙasashen.

    A kowace shekara ƙasashen Afirka kan ƙara yawan kasafin kuɗaɗensu, wataƙila sakamakon raguwar darajar kuɗaɗen ƙasashen.

    Alal misali Najeriya - wadda ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka - kasafin kuɗin ƙasar na bana ya zarta na shekarar da ta gabata da kusan rabi.

  12. Tinubu ya jajanta wa al'ummomin Kaduna da Kano da kuma Borno kan mutuwar mutanensu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook

    Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu matafiya 12 a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan'uwansu.

    Ya buƙaci jami'an tsaro su tabbatar da kama masu laifin tare ganin an hukunta su.

    Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labaru Bayo Onanuga ya fitar ranar Lahadi, shugaban ya ce ba za su lamunci aikata irin haka ba.

    "Kowane ɗan ƙasa na da ƴancin yin tafiya zuwa kowane ɓangare na ƙasar nan," in ji Tinubu.

    Ya jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe da kuma gwamnatin jihar Kaduna, inda ya yi kira da a kwantar da hankali tare da alkawarin cewa sai an hukunta maharan.

    A ɗaya gefen, Tinubu ya nuna kaɗuwa kan mutuwar wasu mutum 10 da ƴar ƙunar bakin wake ta hallaka a babbar kasuwar kifi da ke karamar hukumar Konduga na jihar Borno ranar Asabar.

    Ya miƙa sakon ta'aziyyarsa ga gwamnati da kuma al'ummar jihar kan lamarin da ya faru.

    "Na bai wa jami'an tsaro umarnin matsa ƙaimi don farauto ƴan Boko Haram da suka rage don daƙile ayyukansu. Na kuma bai wa hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA umarnin tallafawa waɗanda abin ya shafa," in ji shugaban Najeriyar.

    Har ila yau, ya sake miƙa ta'azziyarsa ga mutum biyar da suka mutu a wata fashewa a jihar Kano.

    Ya buƙaci hukumomi su gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa fashewar tare da ɗaukar matakan da suka dace don kare afkuwarsa a gaba.

  13. Ko yaƙin Isra'ila zai tursasa wa Iraniyawa yin kaura zuwa Turkiyya?

    Iran

    Asalin hoton, OZAN KÖSE/AFP/GETTY IMAGES

    Rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Iran, wanda ya barke a ranar 13 ga watan Yuni ya haifar da fargabar kwararan ‘yan gudun hijira masu dimbin yawa daga Iran zuwa Turkiyya.

    Idan aka tuna da abin da ya faru na tarwatsewar al’umma a lokacin yakin basasan Syria, wasu na cewa kila abin da zai faru ke nan game da rikicin Iran da Isra’ila.

    Sai dai ya zuwa yanzu dukkanin kafafen yada labarai da sashen BBC mai yada labari da harshen Turkanci ya tattauna da su, sun nuna cewa ba a fara samun tudadar ‘yan gudun hijira masu yawa ba tukuna.

    Hukumar kula da kaura ta Turkiyya ta mayar da martani game da labarin kamfanin dillanci labarai na Anadolu, tana mai cewa ikirarin cewa akwai kwararan ‘yan gudun hijira a yanzu haka daga Iran zuwa Turkiyya ”karya ce tsagwaron ta”.

  14. Sakataren tsaron Amurka ya gargaɗi Iran kan mayar da martani

    Pete Hegseth

    Asalin hoton, The White House

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth ya gargaɗi Iran kan mayar da martanin harin da Amurka ta kai mata, inda ya nanata cewa burin Trump shi ne "samun zaman lafiya".

    "Shugaba Trump ya ce ba ya son janyo ɓarna, zaman lafiya yake buƙata kuma ya kamata Iran ma ta ɗauki ɓangaren," in ji Hegseth.

    Ya kuma ce ya kamata Iran ta guji mayar da martani.

  15. Martanin ƙasashen Larabawa kan harin da Amurka ta kai Iran

    Muna ci gaba da samun martani daga ƙasashen duniya kan harin da Amurka ta kai cibiyon nukiliyar Iran.

    Ƙasashen Larabawa ma ba a bar su a baya ba, ga abin da suke cewa:

    Oman, wadda ke shiga tsakani a tattaunawar Amurka da Iran kan shirin nukiiyar Tehran, ta yi ƙaƙƙausar suka tare da Alla-wadai kan hare-haren na Amurka kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

    Ƙasashen yankin Gulf "sun nuna matukar damuwa, da Alla-wadai kan harin Amurka da kuma barazanar bazuwar rikicin da harin zai haifar".

    Saudiyya, wadda ke da alaƙar tsaro mai ƙarfi da Amurka da kuma ta kasance ƙawarta, ta yi "Alla-wadai da saɓa wa ƴancin ƙasar Iran da kuma buƙatar a kai zuciya nesa", inda ta yi kira ga al'ummomin ƙasashen waje da su "ƙara ƙaimi domin ganin an samu mafita na warware rikicin".

    Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta yi gargaɗin cewa "zaman ɗar-ɗar sakamakon rikicin zai haifar da babban bala'i a yankin da kuma ƙasashen duniya." Ta ce tana "fatan dukkan ɓangarori za su kai zuciya nesa a daidai wannan lokaci."

    Masar ta yi gargaɗin cewa rikicin "zai janyo babban bala'i da kuma ruɗani a yankin," inda ta nanata cewa "tattaunawar diflomasiyya ita ce kaɗai hanyar fita daga wannan rikici, ba ɗaukar matakin soji ba".

    A ɗaya gefen, shugaban Lebanon Joseph Aoun ya ce "kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran ya janyo fargabar da ake da ita na bazuwar rikicin wanda zai haifar da rashin tsaro da kuma ɗorewar yankin".

  16. 'Dole ne a kama tare da hukunta waɗanda suka kashe ƴan ɗaurin aure a Plateau'

    Uba Sani

    Asalin hoton, Uba Sani/FB

    Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da kisan wasu ƴan jihar 12 a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan'uwansu.

    An ruwaito cewa mutanen su 31 sun taso ne daga garin Basawa da ke ƙaramar hukumar Zaria a jihar Kaduna cikin motar bas mallakin Jami'ar ABU Zaria, kafin su faɗa hannun maharan.

    Nan take aka kashe 12 da kuma jikkata 11 lokacin da aka far musu.

    Gwamna Uba Sani ya nuna kaɗuwarsa matuka kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya umarci jami'an tsaro da su gaggauta kama waɗanda suka aikata laifin da kuma hukunta su.

    Ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar ba za ta gajiya ba har sai ta ga an gurfanar da maharan.

    "Lokaci ya yi da za mu kawo karshen irin waɗannan abubuwa na kashe mutanen da ba su yi laifin komai ba, musamman yayin tafiya tsakanin jihohi. Babu wata hujja ta far wa kowane ɗan Nijeriya a kowane ɓangare na ƙasar. Ya kamata mu dakatar da wannan ɗanyen aiki," in ji gwamnan.

    Ya kuma jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa, inda ya yi kira ga al'ummar jihar da su kwantar da hankali domin ana ƙoƙarin ganin an hukunta masu laifin.

  17. Trump ya 'yaudari' Iran da ƴan Amurka ta hanyar kai hare-hare - Ministan wajen Iran

    Abbas

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa Trump ya "yaudari" ɗaukacin Iran da kuma al'ummar Amurka.

    Abbas ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Istanbul lokacin da yake mayar da martani kan hare-haren da Amurka ta kai.

    "Yayin da aka zaɓi Trump don kawo karshen shigar Amurka cikin yake-yake a sassan duniya, ya yaudari Iran ta hanyar take tsarin diflomasiyya har ma da waɗanda suka zaɓe shi ta hanyar miƙa kai don shiga yaƙi, inda ya gwammace ya saka rayuwar ƴan ƙasar cikin masifa da kuma kashe dukiyar Amurka don cimma burin gwamnatin Isra'ila," in ji Araghchi.

  18. Labarai da dumi-dumi, Iran ta yi Alla-wadai da hare-haren da Amurka ta kai ƙasar

    Abbas

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai da hare-haren da Amurka ta kai ƙasar, inda ya ce ba za su lamunci haka ba kuma Iran "za ta yi amfani da duk abin da ya kamata wajen kare kanta".

    "Hare-haren za su haifar da tarin matsaloli. Ya kamata kowane mamba na MDD ya san da wannan abu mai hatsari, rashin mutunta doka da kuma aikata babban laifi," kamar yadda ya wallafa a shafin X.

    Araghchi ya ƙara da cewa Amurka ta "aikata mummunan laifi" kan bil'adama a matsayinta na mamba a kwamitin tsaro na MDD.

  19. Me harin ƙunar baƙin wake a Borno ke nunawa a Najeriya?

    Borno

    Asalin hoton, @ZagazOlaMakama

    Ƙaruwar hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya na ƙara jefa fargaba kan makomar yankin inda masana tsaro suka ce akwai buƙatar sauya salon yaƙi.

    Wannan na zuwa bayan wani mummunan harin ƙunar bakin wake da aka kai a garin Konduga a jihar Borno a ranar Juma'a da ya kashe mutane da dama.

    Rundunar ƴansandan jihar Borno ta ce mutum 10 aka kashe, yayin da mutanen yankin suka ce sama da mutum 20 aka kashe a harin.