Rufewa
Masu bibiyar mu a nan muke sallama da ku, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rabiatu Kabir Runka ke maku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najereiya da sassan duniya 18/12/2024
Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar,Rabiatu Runka da Umar Mika'il
Masu bibiyar mu a nan muke sallama da ku, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rabiatu Kabir Runka ke maku fatan alheri.

Asalin hoton, Reuters
A India masu aikin ceto na can na kokarin gano wadanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su, akan hanyar zuwa fitaccen wurin yawon bude ido na Elephanta Island, da ke birnin Mumbai.
Kwale-kwalen ya daki wani jirgin dauke da sojin ruwan kasar, kuma tuni aka tabbatar da mutuwar mutane 13 ciki har da sojin.
Masu gadin teku da 'yan sandan ruwa na ta jigilar wadanda sukai rai zuwa asibiti da ke kusa da wurin. Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane 80 ne a cikin kwale-kwale.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Ƴan majalisa a Brazil, sun kada kuri'ar amincewa da tsuke bakin aljihu wadda jam'iyya mai mulki ta shugaba Inacio Lula da Silva suka gabatar, a daidai lokacin da darajar kudin kasar ke kara faduwa idan aka kwatanta da dalar Amurka.
Matakan sun hada da rage kudin da ake kashewa a fannin ilimi da tabbatar da mafi kankantar albashin ma'aikatan gwamnati bai karu ba.
Darajar kudin Brazil ta fadi da sama da kashi 20 cikin 100 a wannan shekarar, lamarin da ya sanya masu zuba jari ɗari-ɗari kan yadda gwamnati ke kashe kudade ga kuma tashin farashin kayayyakin da kasar ke fama da shi.
Masana na cewa tsokacin da shugaba da Silva ya yi kan batun ya kara janyo zaman dardar da halin rashin tabbas.

Asalin hoton, OTHER
Ganau a Sudan sun bayyana yadda dakarun RSF sukai ruwan makamai masu linzami a birnin Al Fashir na kasar Sudan, lamarin da ya hallaka farar hula 10 da jikkata wasu 12.
Sun shaidawa BBC cewa harin ya shafi babban asibitin birnin, ya kuma lalata dakunan marasasa lafiya da na tiyata da wurin ajiyar magunguna.
Ko a ranar Juma'a da ta wuce sai da mayakan na RSF suka kai hari asibitin tare da hallaka mutum 9.
Haka ma lokacin da sojin Sudan da na RSF ke gwabzawa a arewacin Darfur, hare-hare ta sama sun hallaka farar hula.
Tun a watan Mayu ne dai RSF ta kaddamar da farmakin karbe iko da El Fasher, kuma tun daga lokacin ta ke yin nasarar mamaye birnin.

Asalin hoton, OTHER
Shugaban kungiyar tsaro ta NATO ya ce ya kamata kawancen ya maida hankali kan yadda za a aikewa Ukraine karin makamai domin ƙara mata ƙarfi a yaƙinta da Rasha, ba wai a zo ana muhawara kan batun a bainar jama'a ko batun tsagaita wuta ba.
Mark Rutte ya bayyana haka ne a Brussels, gabannin tattaunawa da yawancin shugabannin kasasashen turai ciki har da shugaba Vlodimir Zelensky na Ukraine.
Ya kara da cewa tattaunawar zaman lafiyar tamkar taimakon Rasha ne.
Mr Rutte ya yi kiran kasashe mambobin NATO su fito domin tallafawa Ukraine da kudade, a daidai lokacin da zababben shugaban Amirka Donald Trump ke gab da shan rantsuwar kama aiki, da kuma ake fargabar zai iya janye tallafin kasarsa ga Ukraine.
Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa kan halin da ake ciki a Syria, sama da mako guda da hambarar da gwamnatin shugaba Basharul Assad.
Amy Pope shi ne shugaban hukumar kaura ta kasa da kasa, ya ce har yanzu Syria ba wai ta farfado ba ne, kuma ba za ta iya daukar yawan 'yan kasar da sukai gudun hijira a baya ba a yanzu kuma su na son komawa kasarsu.
Shi ma tsohon jakadan Birtaniya a Turkiyya Peter Westmacott, ya shaidawa BCC fargabar shi kan mayakan Kurdawa na Syria.
Ya ce "sun kasance cikin jami'an tsaro musamman a arewacin Syria. Su na kare muradin Syria ta iyakar kudanci, babu jituwa tsakaninsu da dakarun da Turkiyya ke marawa baya a Kobani da yankin Manbij. Ina fargabar za su iya zama babbar matsala a halin da ake ciki a kasar."

Asalin hoton, State House
An ware naira tiriliyan 15.81 domin biyan basuka a cikin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gabatar a gaban majalisa.
A yau Laraba ne Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 47.9.
Haka kuma Tinubu ya ce gwamnati na hasashen tara naira tiriliyan 34.82 daga kuɗaɗen harajin da za su karɓa.
Ma'aikatun da suka fi samun kaso mai yawa sun haɗa da:
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa gwamnatin ta yi ƙiyasin farashin canjin dala kan naira 1,400.

Asalin hoton, EPA
Kotun Ƙolin Ghana ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da kungiyoyin kare hakkin dan'adam da MDD suka yi kan daftarin dokar masu neman jinsi.
Alƙalan kotun sun ce ba za su duba komai ba har sai shugaban kasa ya rattaba hannu kan ta kuma ta zama doka.
Masu neman jinsi dai sun jima suna adawa da dokar. A farkon shekarar nan 'yanmajalisa suka gabatar da kudirin da zai yanke hukuncin zaman gidan yarin na shekara uku ga duk wanda aka samu da bayyana kan sa a matsayin ɗan luwaɗi ko maɗigo.
Haka kuma, kudirin zai haramta yaɗa duk wani abu da ya shafe su, da bai wa mutane kwarin gwiwar kai rahoton duk wani da aka samu da aikata hakan.



Asalin hoton, AFP
A wani rahoton daban na hukumar ƙididdiga ta Najeriya, wato NBS, ce an sace motoci aƙalla 1,587,363 a shekara ɗaya a Najeriya.
A cikin ƙunshin rahoton da hukumar ta fitar, ta ce satar ta fi ƙamari a yankin arewa maso yamma, inda aka sace motoci 603,756 tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.
Sai yankin arewa ta tsakiya ke biye da 246,329, sai kuma yankin arewa maso gabas mai 228, 793.
A yankin kudancin ƙasar kuma, yankin kudu maso yamma da aka samu rahoton sace-sace guda 140,144.
Sai dai duk da haka, rahoton ya ƙara da cewa wasu da dama da aka yi wa satar, ba sa kai ƙara, inda rahoton ya ce kashi 57.6 cikin 100 ne kawai suka kai ƙara.

Asalin hoton, Tajuddeen Abbas/Facebook
Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas ya ce matakan da shugaban ƙasa Bola Tinubu yake ɗauka wajen inganta tattalin arzikin Najeriya na nuna yadda shugaban ya damu da damuwar ƴan ƙasar.
Abbas ya bayyana haka ne a jawabinsa a lokacin da shugaban ƙasa Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 a gabatan majalisar dokokin ƙasar a ranar Laraba.
A cewarsa, "majalisar dokoki za ta ci gaba da goyon bayan matakan gyare-gyaren da kake ɗauka ta hanyar yin dokoki da kuma tattaunawa tare da wayar da kan mutane domin ƙarin fahimta da amincewa
Abbas ya ƙara da cewa tafiye-tafiyen da shugaban yake yi sun ƙara ɗaga darajar ƙasar a idon duniya.
Sai dai ya ce akwai buƙatar a yaba da sadaukawar da ƴan Najeriya suka nuna, inda ya ce cire tallafin man fetur da hauhawar farashin kayayyaki da wasu matakan inganta tattalin arziki sun haifar da ƙalubale sosai
"Sai dai ana buƙatar irin wannan sadaukarwar domin ƙasa ta ci gaba."

Asalin hoton, Twittter/@officialABAT
Shugaban ƙasa Bola Tinubu na Najeriya ye ca matakan da suka ɗauka na inganta tattalin arzikin ƙasar sun fara haifar da ɗa mai ido.
Tinubu ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya gabatar a majalisar dokoki, inda ya ce, "gyare-gyaren da muka yi sun fara haifar da ɗa mai ido.
"Ƴan Najeriya sun kusa fara jin gajiyar ingantaccen tattalin arziki. Ƙasarmu tana samun ci gaba sosai a fagen tattalin arziki."
Ya ƙara da cewa tattalin arzikin Najeriya ya inganta, inda a cewarsa ya haɓaka da kashi 3.46 a rubu'i na uku na shekarar 2024, daga kashi 2.54 a rubu'i na uku na shekarar 2023.

Asalin hoton, Godswill Akpabio
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ja kunnen "ministocinsa masu taurin kai" waɗanda ba sa amsa gayyatar majalisar dokoki.
Akpabio ya ce bai kamata irin waɗannan ministocin su samu gurbi a gwamnatinsa ba.
Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Laraba, a lokacin da shugaban ƙasar yake gabatar da kasafin kuɗin 2025.
"Waɗanda suke ƙin amsa gayyatar majalisar dokoki ba ƴansiyasa ba ne, don haka bai kamata su samu gurbi a gwamnatinka ba," kamar yadda Akpabio ya bayyana wa Tinubu.

Asalin hoton, Getty Images
Kuɗaɗen da gwamnatin Najeriya ke biya a matsayin tallafin lantarki ya ƙaru zuwa naira biliyan 199.64 a watan Disamban 2024, kamar yadda alƙaluma daga hukumar kula da lantarki NERC suka nuna.
Tashar Channels ta ruwaito daga wani rahoto da hukumar ta fitar cewa kuɗin tallafin ya ƙaru da kashi 2.76 wato naira biliyan 199.64 a wannan watan na Disamban, daga naira biliyan 194.26 a watan Nuwamban bana.
Hukumar NERC ta ce an samu ƙarin ne saboda faɗuwar darajar naira, kasancewar an ƙiyasta darajar dala ne a naira 1,687.45 a kasafin kuɗin kasar, da hauhawar farashin kayayyaki da ya ƙaru zuwa kashi 33.9.
Rahoton ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ba ta canja farashin lantarki ba a ɗan tsakankanin.

Asalin hoton, OTHERS
Wani rahoto da hukumar tattara alƙaluman Najeriya, NBS ta fitar ranar Litinin ya nuna irin girman matsalar tsaro a Najeriya musamman abin da ya shafi garkuwa da mutane.
Rahoton mai taken Laifukan da aka fuskanta da kuma jin ra'ayin mutanen kan sha'anin tsaro na 2024, ya ce tsakanin watan Mayun 2023 da Afrilun 2024, an kashe ƴan Najeriya 614,937 sannan an yi garkuwa da mutum miliyan 2,235,954.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an biya masu garkuwa da mutane kuɗin fansar da suka kai yawan naira tiriliyan 2.2, kuma hakan na nufin akan biyu naira miliyan 2.7 ga kowane mutum.