An bayyana jagoran 'yan hamayya na Mauritius a matsayin Firaminista bayan gagarumar nasara a zaɓe

Asalin hoton, REUTERS/Ally Soobye
Shugaban Mauritius, Prithvirajsing Roopun ya bayyana sunan babban jagoran 'yan hamayya na ƙasar Navin Ramgoolam, a matsayin sabon firaministan ƙasar, bayan da jam'iyyarsa ta samu gagarumar nasara a zaɓen majalisar dokoki.
Kafar yaɗa labarai mai zaman kanta ta Defi Media da ke ƙasar ita ce ta ruwaito labarin a jiya Talata.
Haɗakar jam'iyyun hamayya ta ci kujeru 60 na majalisar dokoki, inda wannan nasara ta zama mai tarihi a siyasar ƙasar.
Sabuwar gwamnati da za a kafa ta yi alƙawarin yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima, tare da gudanar da zaɓen hukumomin ƙauyuka da birane duk bayan shekara biyar.
Tsohon Firaminista na baya-bayan nan Pravind Jugnauth, ya amince da shan kaye a zaɓen wuri da aka yi ranar 11 ga watan nan na Nuwamba, ya kuma sauƙa bayan shekara bakwai a kan mulki.
A shekara ta 2017 ya gaji mahaifinsa a matsayin firaminista.
Ramgoolam, mai shekara 77, zai kasance firaminista a karo na uku, kasancewar ya riƙe muƙamin a baya daga shekarar 1995 zuwa 2000, sannan kuma ya sake hawa tsakanin 2005 da 2014.
Ya fito ne daga gidan iyalan ɗaya daga gidajen da suka mamaye siyasar ƙasar ta Mauritius, tun da ta samu 'yanci a 1968.





