Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida, Ahmad Bawage da Aminu Kutama

  1. 'Akwai yiwuwar dakarun gwamnatin Syria sun aikata laifukan yaƙi'

    Dakarun Syria

    Asalin hoton, Reuters

    Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce akwai yiwuwar dakarun gwamnatin Syria da ƙawayensu sun aikata laifukan yaƙi a rikicin lardin Latakia a watan Maris, wanda ya janyo mutuwar ɗaruruwan mutane.

    Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun ce an kashe ɗaukacin iyalai waɗanda yawanci suka fito daga ƴan ƙabilar Alawi - kisan kuma ya kasance dagangan.

    An aika dakarun da ke goyon bayan gwamnati kusan 2,000 zuwa yankin, bayan hare-hare da masu mubaya'a ga tsohon shugaban ƙasar, Bashar al-Assad suka kai.

    Masu bincike na MDD sun karkare cewa duk da rahotanni da suka ce an kama yawancin waɗanda ake zargi da aikata laifukan, amma ana buƙatar ɗaukar ƙarin matakan shari'a.

  2. Dalilai shida da ke haddasa fasa gidajen yari a Najeriya

    Gidan yari

    Asalin hoton, @CorrectionsNg

    A farkon makon nan ne aka samu wani hari kan gidan yarin Keffi da ke jihar Nasarawa a Najeriya, lamarin ya sa fursunoni 16 suka arce, kodayake daga baya hukumomi sun ce sun kama bakwai daga ciki.

    Cikin wata sanarwa da hukumar kula da gidajen yarin ƙasar ta fitar, ta ce harin ya yi sanadiyyar raunata jami'an kula da gidan aƙalla biyar, inda biyu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

    Sanarwar ta ce ɗaurarrun sun ci ƙarfin maʼaikatan da ke tsaron gidan yarin ne, lamarin da ya bai wa wasu daga ciki damar guduwa nan take.

    Latsa nan don sanin dalilan...

  3. Sudan ta Kudu ta ƙaryata tattaunawa da Isra’ila kan tsugunar da Falasɗinawa

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta Kudu ta karyata wani rahoton da kamfanin dillancin labarai na Associated Press AP ya wallafa a ranar 12 ga Agusta, wanda ya ce kasar na tattaunawa da Isra’ila kan karɓar ‘yan Falasdinawa daga Gaza.

    A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, ma’aikatar ta ce: "Rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka wallafa, waɗanda ke ikirarin cewa gwamnatin ƙasar Sudan ta Kudu na tattaunawa da gwamnatin Isra’ila kan batun sake tsugunar da ‘yan Falasdinawa daga Gaza a Kudancin Sudan ƙarya ne. Babu kamshin gaskiya a rahoton."

    "Babu hannun hukuma ko manufar gwamnatin Sudan ta Kudu a ciki," in ji sanarwar.

    Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa wasu mutane guda shida da ke da matsaniya kan lamarin sun tabbatar da tattaunawar, sai dai har yanzu ba a san matakin da ake ciki kan tattaunawar ba.

    A ranar Laraba ne dai Sudan ta Kudu da Isra’ila suka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan haɗin gwiwar ɓangarori daban-daban, yayin ziyarar mataimakiyar ministan harkokin wajen Isra’ila, Sharren Haskel, a birnin Juba.

    Haka kuma, ministan harkokin wajen Sudan ta Kudu, Monday Semaya, ya ziyarci birnin Urushalima a kwanakin baya, inda ya gana da shugaban Isra’ila Isaac Herzog da Firaminista Benjamin Netanyahu.

  4. Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami'o'i masu zaman kansu guda tara

    ...

    Asalin hoton, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Facebook

    Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami'o'i masu zaman kansu guda tara a faɗin Najeriya.

    Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan taron majalisar zartarswa ta ƙasa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja.

    Ya ce jami’o’in da aka amince da su sun haɗa da:

    • Jami’ar Tazkiyah da ke jihar Kaduna
    • Jami’ar Leadership da ke babbar birinin tarayya, Abuja
    • Jami’ar Jimoh Babalola a jihar Kwara
    • Jami’ar Bridget, Mbaise a jihar Imo
    • Jami’ar Greenland da ke jihar Jigawa
    • Jami’ar JEFAP a jihar Neja
    • Jami’ar Azione Verde da ke jihar Imo
    • Jami’ar Unique Open a Jihar Legas
    • Jami’ar American Open da ke Jihar Ogun

    Alausa ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaji buƙatu 551 na kafa sababbin jami'o'i, inda aka saka tsauraran ka’idojin tantancewa kafin amincewa da su.

    Ƙa'idojin tantancewar ta saka buƙatun kafa sabbin jami'o'in zuwa guda 79 wanda kuma daga cikinsu ne aka amince da kafa guda tara a ranar Laraba.

    Ministan ya ƙara da cewa da dama daga cikin jami’o’in da aka amince da su suna jiran samun izinin aiki sama da shekaru shida, duk da cewa masu hannun jari sun riga sun gina harabar makaranta tare da zuba biliyoyin naira a ciki.

    “Rashin inganci a cikin hukumar NUC ne ya jawo jinkirin amincewa da buƙatun. Mun aiwatar da wasu gyare-gyare don sauƙaka tsarin.”

    Ministan ya kuma ƙoƙa da cewa ana ɓarnar kuɗi ne kawai wajen kafa jami'o'i saboda wasu ba su ma da isassun ababen koyarwa.

    "Alal misali, akwai wata jami'a a ƙasar nan da ke da ɗalibai ba ba su haura 800 ba da malamai 1,200. Haka lamarin yake a yawancin jami'o'i a ƙasar nan," in ji Alausa.

  5. Trump ya ce ba zai tattauna raba yankunan Ukraine ba idan ya gana da Putin

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce Donald Trump ya fadawa shugabannin ƙasashen Turai cewa ba zai tattauna yiwuwar raba yankuna a Ukraine ba, idan ya gana da Vladimir Putin gobe Juma'a.

    Rahotanni sun ce Trump ya yi alƙawarin saka Ukraine a cikin duk wata shawara da ta shafi rabon filaye.

    A wani mataki na kawar da damuwar da shugabannin Turai suka nuna , rahotanin sun ce shugaba Trump ya yi alkawarin ba za su tattauna kan batun raba filaye, idan Ukaraine ba ta cikin tataunawar.

    Shugaba Trump ya sha nanata cewa wataƙila sai an yi mussayar yankunan domin samun zaman lafiya wanda wani abu ne da ya tayar da hankalin shugabanin ƙasashen turai.

  6. PDP za ta ƙaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyi

    ...

    Asalin hoton, PDP

    Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP na shirin kaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyi da kuma kwamitin tsara zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyar na shekarar 2027 a yau Alhamis a Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Wannan na zuwa ne yayin da ake samun rabuwar kawuna tsakanin mambobin kwamitin zartaswa na ƙasa na jam'iyar wato NEC kan yunƙurin dawo da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, cikin jam’iyyar.

    Wasu daga cikin shugabannin PDP na ganin cewa Jonathan ya bar jam’iyyar a lokaci mai muhimmanci, yayin da Obi kuma ya yi sauya sheƙa zuwa Labour, lamarin da ya rage wa jam'iyyar damar samun nasara a zaɓen 2023.

    Sai dai wasu mambobin kwamitin zartaswar sun yi maraba da wannan yunƙuri, suna cewa PDP na da isassun jiga-jigai masu kwarewa waɗanda za su iya wakiltar jam’iyyar a zaɓen 2027.

    Rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar ba ta kai ga tuntuɓar Jonathan da Obi a hukumance ba, sai dai wasu mutane ne daban-daban ke yin hakan a madadinta.

    Kakakin jam’iyyar PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce ƙaddamar da kwamitin zartarswar zai gudana ne a yau Alhamis, tare da jaddada cewa jam’iyyar na da wadatattun masu neman takarar shugabanci a cikinta.

  7. Cutar kwalara ta kashe dubban mutane a Sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar agaji ta MSF, ta ce Sudan na fama da ɓarkewar cutar kwalara mafi muni, wadda ba a taba ganin irinta ba a tsawon shekaru da dama, inda ta kashe mutane fiye da dubu biyu da dari hudu.

    Ƙungiyar agajin ta ce mutane fiye da dubu dari ne suka kamu da cutar a shekarar da ta gabata kuma cutar ta yi ƙamari ne sakamakon yaƙin basasar ƙasar.

    Almarin ya fi ƙamari ne a yankin Tawila da ke arewacin Darfur, inda ake da ɗimbin 'yan gudun hijira daga birnin El Fasher da aka yi wa kawanya.

    Ma’aikatan agaji da ke wurin sun shaida wa BBC cewa sansanonin ba su da isassun wuraren ba haya ko ruwan sha mai tsafta.

  8. Ƙungiyoyin agaji sun zargi Isra’ila da hana shigar da kayan jin ƙai zuwa Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyoyin agaji fiye da 100 sun zargi Israila da ci gaba da hana shigo da kayan jin kai cikin Gaza duk kuwa da alƘawarin da ta yi na bada damar shigo da kayan agaji masu yawa domin sauƘaka matsalar yunwa.

    ƙungiyar agaji ta Oxfam ta ce an hanata shigo da kayan agaji da aka yi ƙiyasin sun fi dala miliyan biyu, yayin da ƙungiyar agaji ta Care ta ce akwai kayan agaji na iyaye mata da jarirai da suka shafe tsawon wata biyar suna jiran su shigo da su Gaza wanda kuɗinsu ya zarce dala miliyan guda.

    Ƙungiyoyi masu yawa sun ce ba a samu ko da mota ɗaya daga cikin manyan motocinsu da Isra'ila ta bari ya shiga cikin Gaza tun watan Maris daya gabata .

    Ƙungiyoyin agajin sun yi gargaɗi kan sabbin dokokin tantancewa na israila , na hana su samun damar shiga cikin Gazan

  9. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Alhamis

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.