Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida, Ahmad Bawage da Aminu Kutama

  1. Rufewa

    Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Israʼila ta zargi ƙungiyoyin agaji da janyo jinkirin shigar da agaji Gaza

    Firaministan Israʼila, Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Firaministan Israʼila, Benjamin Netanyahu

    Isra'ila ta zargi ƙungiyoyin agaji da janyo jinkiri wajen shigar da kayan agaji Gaza sakamakon rashin bin ƙa'idojin da aka shimfiɗa na kauce wa faɗawar kayyayakin hannun Hamas.

    Kakakin hukumar sa ido kan yankunan Falasɗinawa ya ce wannan ya ƙara ƙarfafa zargin da ake wa ma'aikatan na aiki da Hamas.

    A ranar Alhamis ne wasu ƙungiyoyin agaji sama da 100 suka fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa, inda suke zargin Isra'ila da neman wasu bayanan sirri kan ma'aikanatsu abin da suka ce ana amfani da shi domin daƙile shigar da kayyaykin agajin zuwa Gaza.

    Sun ce an yi watsi da aƙalla buƙatu 60 da aka tura na neman izinin shigar da kayan agaji Zirin a watan da ya gabata kaɗai.

  3. ECOWAS na zawarcin ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso

    Shugabannin Mali da Nijar, Assimi Goita da Abdourahamane Tiani

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugabannin Mali da Nijar, Assimi Goita da Abdourahamane Tiani

    Shugaban ƙungiyar raya tattalin arzƙin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, ya buƙaci ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da ke ƙarƙashin mulkin soji, su dawo cikin ƙungiyar.

    Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio ya ce ya tattauna da shugabannin sojin ƙasashen uku domin lalubo yadda za a magance musu matsalolinsu.

    Ƙasashen uku sun ɓalle daga ECOWAS ne bayan sun ƙi amincewa da buƙatar ƙungiyar ta komawa mulkin dimokraɗiyya.

    Shekaru biyun da suka gabata ƙasashen suka ƙulla ƙawancen ƙungiyar AES a tsakaninsu.

  4. Ina fatan cimma zaman lafiya da Putin ranar Jumaʼa - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka, Donald Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana fatan cimma zaman lafiya sakamakon tattaunawarsa da Vladimir Putin ranar Juma'a, sai dai ya ce hakan ya dogara kan yadda tattunawar za ta kasance.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar House ranar Alhamis, mista Trump ya ce idan aka samu nasara a tattaunawar, za a gudanar da wata tare da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce domin samun zaman lafiya, wajibi ne a yi wasu tattaunawa masu muhimmanci, kuma fatan Shugaba Trump shi ne a ɗan dakatar da yaƙin don a samu damar yin tattaunawar.

  5. NLC ta yi gargaɗin tsunduma yajin aiki saboda matsalar fansho

    Yan ƙungiyar ƙwadago ta NLC na zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Yan ƙungiyar ƙwadago ta NLC

    Kungiyar ƙwadago a Najeriya, NLC, ta bai wa gwamnatin tarayya waʼadin kwana bakwai sakamakon gazawarta wajen naɗa majalisar gudanarwa a hukumar kula da fansho ta Najeriya.

    Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya fitar ranar Laraba, NLC ta kuma zargi gwamnatin da karkata kuɗin maʼaikata ta hanyar amfani da asusun tallafa wa tsoffin maʼaikata a Najeriya, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

    A cewar Ajaero, shugabancin ƙungiyar ya zauna ranar Laraba kuma ya tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da rikicin shugabancin ƙungiyar a jihar Edo da kuma matsaloli a harkar fanshon ƙasar.

    Shugaban ƴan kwadagon ya kuma yi gargaɗin tsunduma yajin aiki idan gwamnatin ba ta ɗauki matakan da suka dace ba cikin mako gudan da ta bayar.

  6. Gwamnatin Sokoto ta ci gaba da shirin bai wa matasa jari na N-G Cares

    Gwamnan sokoto na jawabi

    Asalin hoton, Sokoto State Govt

    Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ci gaba da aiwatar da shirin bayar da jari domin bunƙasa ƙananan da matsakaitan sana'o'i a jihar.

    Yayin da yake jawabi wajen ƙaddamar da shirin a karo na biyu, gwamnan jihar Ahmad Aliyu ya ce ya ce gwamnatin ta ɓullo da shirin ne domin tallafa wa masu ƙananan sana'o'i da nufin inganta tattalin arzikin jihar.

    Jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin ƙasar da ke fuskantar koma-bayan tattalin arziki. Don haka ne gwamnan ya ce shirin ya bai wa dubban matasan jihar damar samun jari da kuma dogaro da kansu.

    Wani sarki na bayar da chekin kudi

    Asalin hoton, Sokoto State Govt

    "A yanzu gwamnati ta ƙara yawan jarin da za a bai wa masu matsakaitan sana'o'i daga naira 300,000 zuwa 500,000 yayin da za a bai wa masu ƙananan sana'o'i naira 100,000 domin amfana da shirin N-G Cares", in ji gwamnan.

    Ya ƙara da cewa a matakin farko na shirin gwamnati ta tallafa wa mutum 8,590 da jarin yayin da wannan karo kusan mutum 14,000 ne za su amfana da shirin - wanda na haɗin gwiwa ne da Bankin Duniya da kuma Bankin zuba jari.

    Wasu mata sanye da korayen hijabai

    Asalin hoton, Sokoto State Govt

  7. Cutar ƙyandar biri na ci gaba da yaɗuwa a Afirka - WHO

    wani hannu ɗauke da ƙuraje

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana damuwar kan ci gaba da yaɗuwar cutar kyandar biri da yadda take ƙara kashe mutane a Afirka.

    A shekarar da ta gabata ne dau WHo ta ayyana cutar a matsayin barazanar lafiya' ga ɗan'adam a duniya.

    Bayanai daga cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afirka sun tabbatar da ƙaruwar mace-mace sakamakon cutar da kashi 431% a 2025.

    CDC ta ce cutar ta yaɗu zuwa ƙasashe 25 a Afirka, kuma hijira tsakanin ƙasa da ƙasa ta janyo yaɗuwar cutar a ƙasashen China da Belgium, da kuma Birtaniya.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, WHO ta ce wasu ƙasashen na ƙoƙarin magance cutar, kamar Ivory Coast da Zimbabwe da kuma Angola.

  8. Ƴansiyasa ne manyan ƙalubalenmu a zaɓen cike gurbi a Kano - INEC

    Wani mai zaɓe na amfani da naʼurar BVAS a Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Naʼurar zaɓe ta BVAS

    Kwamishinan hukumar zaɓen Najeriya,mai zaman kanta (INEC) reshen jihar Kano, Zango Abdu ya ce hukumar ta shirya gudanar da zaɓen cike gurbi na ƴan majalisa a jihar.

    A ranar Asabar ne za a yi zaɓukan cike gurbi na ƴan majalisar jiha a mazaɓar Bagwai da Shanono, da kuma na Ghari (Kunchi) da Tsanyawa a jihar.

    Da yake magana da manema labarai ranar Alhamis, Zango ya ce babbar damuwar hukumar bai wuce ƴan siyasar da ke cikin zaɓen, duk da cewa sun sanya hannu kan jarjejeniyar zaman lafiya.

    "Babau abin da tashin hankali ke haifar wa a harkar zaɓe, dole ne a bar mutane su zaɓi shugabannin da suke so ba tare da tsangwama ba," kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ambatoshi yana cewa.

    Abdu ya kuma ce an raba muhimman kayayyakin zaɓe da sauran abubuwan da ake ɓukata ga ƙananan hukumomin huɗu gabanin zaɓen.

    Kazalika baturen zaɓen ya ce an kammala yi wa mutanen da za su yi aikin zaɓen horo, kuma an samar da cikakken tsaro.

  9. 'Ganawar Trump da Putin za ta kawo ƙarshen yaƙin Ukraine'

    Starmer da Zelensky

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Starmer da Zelensky

    Shugabanni ƙasashen Birtaniya da Ukarine sun amince cewa taron da za a yi tsakanin Amurka da Rasha a ranar Juma'a zai bayar da wata muhimmiyar dama ta kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine, muddin shugaba Putin zai iya nuna cewa da gaske yana son zaman lafiya.

    Taron da aka yi tsakanin Keir Starmer da Volodymyr Zelensky a birnin Landan a yau Alhamis, na zuwa ne a yayin da ake samun ƙwarin gwiwar cewa ba za a yi watsi da matsayar Ukraine ba a taron da za a yi tsakanin Shugaba Trump da Putin.

    Taron da suka yi na tsawon sa'a ɗaya ya ƙunshi aniyar ƙasashen Turai ta nuna wa Ukraine cewa suna goyon bayanta ɗari bisa ɗari.

  10. Gwamnan Katsina ya tafi hutu don kula da lafiyarsa

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda

    Asalin hoton, Gwamnatin Jihar Katsina

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya sanar da tafiya hutun mako uku don kula da lafiyarsa.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango ya fitar, ya ce gwamnan zai fara hutun ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agustan 2025.

    “Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi aiki cikin yanayi mai kyau, na ɗauki wannan matakin tafiya hutu, kuma zan dawo da zarar likitoci sun gama duba ni,'' in ji Gwamna Radda.

    Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Malam Faruk Jobe.

    A watan Yuli ne gwamna Radda ya yi hatsarin mota a kan hanyar Katsina zuwa Daura.

  11. 'Dole gwamnatin Tinubu ta rage wa ƴan Najeriya raɗaɗin da suke ciki'

    Tsohuwar ministar kuɗin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala yayin wani taro

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugabar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala

    Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tanadi tsare-tsaren sauƙaƙa wa talakawan Najeriya da ke jin raɗaɗin tsare-tsaren tattalin arziƙi na gwamnatin Tinubu.

    Okonjo-Iweala ta faɗi hakan ne ranar Alhamis bayan ta gana da shugaban ƙasar a Abuja.

    Duk da ta yaba wa shugaban ƙasar kan tsare-tsarensa na tattalin arziƙi da suka haɗa da cire tallafin man fetur, tsohuwar ministar kuɗin Najeriyar ta ce dole ne gwamnatin ta tallafa wa ƴan ƙasar.

    Iweala ta ce “muna ganin shugaban ƙasar da gwamnatinsa sun daidaita tattalin arziƙin Najeriya, amma duk da haka sai sun tabbatar da ɗorewar sauyin mai kyau da aka samu zuwa yanzu."

  12. Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunoni gabanin ganawar Trump da Putin

    Rasha da Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwana guda kafin tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha a Alaska, Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunoni.

    A wannan karon, ƙasashen biyu sun yi musayar fursunoni 84 daga kowane ɓangare.

    Shugaba Zelensky ya ce daga cikinsu akwai fararen hula, wasu daga ciki kuma na hannun Rasha tun 2014.

    Fursunonin sun kuma haɗa da sojojin da aka kama lokacin da suke ƙoƙarin kare birnin Mariupol.

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce ta shiga tsakani domin musayar.

  13. Sojojin Najeriya sun musanta miƙa wuyan Bello Turji

    Bello Turji

    Asalin hoton, Sheikh Gumi

    Shelkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotanni da ke cewa riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan wanda ya yi ƙaurin suna, Bello Turji ya miƙa wuya ga sojojin ƙasar.

    Daraktan yaɗa labarai da aikace-aikacen shelkwatar tsaron, Manjo-Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a yau Alhamis.

    "Maganar ita ce Bello Turji bai miƙa wuya ba, muna ci gaba da farautarsa," in ji shi.

    Ana zargin Turji wanda ake nema ruwa a-jallo da kai hare-hare kan al'ummomi a yankin arewa maso yamma, musamman jihohin Zamfara da Sokoto.

    A baya-bayan nan, rahotanni sun bayyana cewa ɗan bindigar ya ajiye makamansa, kuma ya saki mutum 32 da yake garkuwa da su, bayan tattaunawar zaman lafiya da malaman addini suka jagoranta a jihar Zamfara.

  14. 'Gina gidaje a Gaɓar Yamma zai kawar da burin samar da ƙasar Falasɗinu'

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan kuɗi na Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Bezalel Smotrich, ya ce amincewarsa da shirin gina gidaje fiye da dubu uku a gaɓar Yamma, zai shafe duk wani shiri na samar da ƙasar Falasɗinawa.

    Ya shaida wa manema labarai cewa shirin Maale Adumim, wanda zai farfaɗo da wani shiri da aka dakatar na tsawon shekara 20 saboda rashin goyon bayan ƙasashen duniya, na da goyon bayan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

    Shirin zai raba gaɓar Yamma da aka mamaye zuwa yankin arewaci da na kudanci, ya kuma ware gabashin birnin ƙudus- wanda hakan zai kawar da burin Falasɗinawa na samar da ƙasa.

  15. Ɗalibin jami'a ya kashe kansa bayan faɗuwa jarabawa

    Jami'a

    Asalin hoton, @OfficialOAU

    Hukumar jami'ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun, sun tabbatar da mutuwar wani ɗalibi, mai suna Ajibola Ibitayo - wanda ake zargin ya kashe kansa.

    Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar Mista Abiodun Olarenwaju ya fitar ranar Alhamis, ya ce ɗalibin wanda yake aji na biyu - ya kashe kansa ne bayan faɗuwa jarabawa da ya rubuta.

    Olarenwaju ya ce an sake sakamakon jarabawar ne ranar Laraba, kuma sakamakon ya nuna cewa ɗalibin zai sake maimaita aji, wanda shi ne karo na biyu da zai yi hakan, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    "Ɗaukacin jami'ar Obafemi Awolowo na cikin alhinin rashin wannan ɗalibi da aka yi," in ji sanarwar.

    Rahotanni sun bayyana cewa ɗalibin ya yi wa kansa allura a gidan mahaifansa bayan ganin sakamakon jarabawarsa.

    Shugaban jami'ar Farfesa Simeon Bamire, ya buƙaci iyaye da su riƙa shawartar ƴaƴansu cewa samun koma-baya yayin neman nasara na cikin wani darasi na rayuwa.

  16. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Kilishi ta Labarina

    Shirin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon, ya kawo muku hira da fitacciyar jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam da aka fi sani da 'Kilishi' a cikin shirin Labarina mai dogon zango.

    An haifi Hauwa a ƙauyen Dulum da ke garin Jos a jihar Plateau.

    Bayan faɗan ƙabilanci da aka yi a garin Jos a 2002/2003 Hauwa Musa Adam ta daina zaman ƙauye inda ta koma cikin garin Jos domin ci gaba da rayuwa.

    Jarumar - wadda ƴar ƙabilar Birom ce - ta ce kodayake ba ta yi karatu mai zurfi ba, ta yi firamare da sakandire, sai kuma ilimin zama da jama'a da ta samu.

    Kilishi ta ce tun tana Furamare take da sha'awar shiga harkar film.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  17. Ambaliya ta kashe mutum aƙalla 30 a Indiya

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum aƙala 30 sun mutu bayan afkuwar ambaliya sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a ƙauyen Himalaya da ke kan tsauni a ƙasar Indiya.

    Ministan yankin Kashmir Omar Abdullah ya ce "mamakon ruwa" ya afka wa lardin Kishtwar, kuma lamarin babu kyau.

    Jami'ai a yankin sun ce wasu gomman mutane sun jikkata.

    Dandazon mutane da suka zaƙu sun taru a asibitin Kishtwar lokacin da aka kai mutanen da suka jikkata.

    Firaministan Indiya, Narendra Modi ya ce za a bai wa mutanen dukkan kulawar da suke buƙata.

  18. Harin Ukraine ya jawo gobara a matatar mai a Rasha

    Rasha

    Asalin hoton, Social Media

    Wata matatar mai a Rasha ta kama da wuta bayan harin da Ukraine ta kai kan matatar da ke yankin Volgograd a kudancin ƙasar.

    Gwamnan yankin ya ce ɓaraguzai ne suka faɗa wa matatar bayan harin na jirgi mara matuki.

    Hotunan bidiyo sun nuna yadda wuta ke ci da kuma hayaki da ya turnuke sama daga matatar.

    A ɗaya gefen, gwamnan ya ƙara da cewa an jikkata mutum 13 a wani hari na daban da Ukraine ɗin ta kai yankin Rostov - bayan da harin ya faɗa kan gine-ginen mutane.

  19. Amurka za ta sayar wa Nijeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makamai wanda kuɗinsu ya kai dala miliyan 346.

    Ma'aikatar harkokin tsaron Amurkar ta ce makaman da za a sayar wa Najeriyar sun haɗa da manyan bama-bamai da kuma rokoki.

    Washington ta ce sayar da makaman zai ƙara inganta ɓangaren tsaron Najeriya da kuma taimakawa tsarin harkokin wajen ta a yankin kudu da Hamadar Saharar Afirka.

    "Cikin makaman har da wasu rokoki na zamani sama da 5,000," in ji sanarwar Washington.

    A 2014 lokacin mulkin Barack Obama, Amurka ta ki amincewa ta sayar wa Najeriya wasu muggan makamai, bayan nuna damuwa kan zargin sojojin ƙasar da take hakkin ɗan'adam.

    A lokacin, gwamnatin Najeriya ta yi ƙorafin cewa hakan na yin cikas a yaƙi da take yi da masu iƙirarin jihadi a arewa maso gabas.

    Har zuwa yau, ƙasar na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da hare-hare da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ke kai wa da kuma ayyukan masu garkuwa da mutane a arewa maso yamma da kuma ƴan aware a kudu maso gabashin ƙasar.

  20. Ƴansanda sun kama wani fasto kan zargin 'lakaɗa wa" yara duka a jihar Ribas

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansanda a jihar Ribas ta kama wani fasto da wasu ma'aikatansa biyu a jihar Ribas, kan zargin lakaɗawa yara duka lokacin wani taro da aka kwatanta da "taron tsarkakewa".

    Jami'in ƴansanda na yankin Eneka a jihar, Akpo Lewis, shi ya tabbatar da kama faston da wasu ma'aikatan cocin, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna malaman cocin na mai suna Ifediorah Joseph, na lakaɗawa yaran waɗanda ba su haura shekaru biyar zuwa tara ba duka ta hanyar amfani da iccen kwakwa lokacin bikin.

    Har ila yau, ana iya ganin yadda faston ya yi ta dukan yaran sau da dama, kafin ya miƙa su hannun wani mamba a cocin, wanda shi kuma ya aika su ga wata ƙungiya da ake wa lakabi da "ƙungiyar tsarkakewa".

    Sauran waɗanda aka kaman sun haɗa da sakataren walwala na cocin, Promise Nwikegha da kuma wata mai addu'a Deborah Ohia.

    Sai dai rahotanni sun bayyana cewa a idon iyaye aka lakaɗawa yaransu duka kuma sun ce suna da matsaniya kan bikin.