Sanata Natasha ta buƙaci a mayar mata da jami'an tsaronta bayan kai wa gidansu hari a Kogi
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza
Firaministan India ya gana da Elon Musk domin ƙulla alaƙa da Amurka
Asalin hoton, Getty Images
Firaministan India, Narendra Modi ya ce ya samu ganawa mai muhimmanci da attajitin ɗankasuwa, wanda yake shugabantar sashen gyara aikace-aikacen gwamnatin Amurka, Elon Musk ta wayar taho kan bunƙasa fasahar zamani da ƙirƙire-ƙirƙire.
Modi ya yi wannan tattaunawar ce a ƙoƙarin ƙasarsa ta ƙulla alaƙa da Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa kayayyakin India harajin kashi 27 a farkon wannan watan, kafin ya ɗaga ƙafa na kwana 90.
A wani ɓangare kuma Musk yana ta ƙoƙarin faɗaɗa kasuwancinsa a Indiya, inda tuni ɗankasuwar, wanda yake da kamfanin motar lantarki, Tesla ya fara ɗaukar ma'aikata a ƙasar, kuma kamfanin sadarwarsa ta Starlink tana jiran amincewar gwamnati domin fara aiki.
Kisa ta hanyar rataya ce hukuncin masu garkuwa da mutane a Edo – Okpebholo
Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya ce masu garkuwar da aka kama a jiharsa hukuncin kisa za su fuskanta ta hanyar rataya.
Gwamnan ya ce a shirye yake ya sanya hannu domin tabbatar da hukuncin kisar idan aka yanke wa duk wani mai garkuwa da aka kama.
Okpebholo ya bayyana haka ne a taron ƙara wa juna sani a garin Uromi, inda ya gana da ƴan arewa da ke zaune a ƙasar Esan, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito ta kalato daga sanarwar da sakataren watsa labaran gwamnan, Fred Itua ya fitar.
Ya ce majalisar dokokin jihar Edo ta amince da ƙudurin yi wa dokar haramta garkuwa da mutane ta jihar ta 2013 garambawul domin tabbatar da hukuncin kisa.
Ya ce dokar ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa, tare da ƙwacewa da rusa gidan da aka yi amfani da shi wajen aikata laifin, sannan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin tsaro, kashe-kashe da garkuwa da mutane ba.
A nasa jawabin, shugaban ƴan arewa na Edo ta Tsakiya, Bawa Umar godiya ya yi a madadin ƴan arewa ga gwamnan da Onojie na Uromi bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ƴanbindiga masu ikirarin jihadi sun kashe sojoji takwas a Benin
Wasu mahara da ake zargin ƴanbindiga ne masu ikirarin jihadi sun kashe sojoji takwas a arewacin ƙasar Benin, kamar yadda majiyar tsaro ta shaida wa AFP a ranar Juma'a.
Harin ya auku ne a sansanonin sojojin ƙasar guda biyu a ranar Alhamis, sai dai majiyar ta ƙara da cewa an kashe maharan guda 11 a gwabzawar.
Waɗanda suka jikkata yanzu suna kwance suna jinya a wani asibiti a ƙasar.
Sojojin Benin dai suna cigaba da gwabza yaƙi a yankin ne domin fatattakar ƴanbindiga, inda ko a Janairun 2022 ta aika ƙarin sojoji 3,000.
Ko a watan Janairun da ya gabata an kashe sojojin Benin 29 a wani hari da ƙungiyar GSIM mai alaƙa da Al Qaeda ta ɗauki alhaki.
Iran na da yaƙinin cimma yarjejeniya da Amurka kan shirin nukiliyarta
Asalin hoton, Reuters
Ministan harkokin wajen Iran ya ce yana da yaƙinin cewa ƙasarsa za ta iya cimma yarjejeniya da Amurka game da shirin nukiliyarta.
To sai dai Abbas Araghchi na da shakku kan muradun da Amurka ke neman cimmawa.
Ya ƙara da cewa yana fatan Rasha za ta taka rawa a tattaunawar.
Yana magana ne bayan wata ganawa da takwaransa na Rasha, Sergey Lavrov a birnin Moscow.
A gobe Asabar ne za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawa tsakanin Tehran da Washington a birnin Rome
Cututtuka masu bijirewa magani sun haddasa mutawar yara miliyan uku - Bincike
Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike da wasu manyan ɓangarorin masana kiwon lafiyar ƙananan yara suka gudanar ya gano cewa fiye da yara miliyan uku ne suka mutu a faɗin duniya a 2022 sakamakon cutakan da ke bijire wa magani.
Ƙananan yara a nahiyar Afirka da Kudu maso Gabashin Asiya na daga cikin waɗanda suka fi hatsari.
Bijire wa magunguna - da a turance ake kira ''Antimicrobial resistance'', (AMR) na faruwa idan ƙwayoyin cutar da ke haddasa cuta suka yi ƙarfin da magani ba zai iya yaƙi da su ba.
Amurka ta bai wa Benin kayan aikin soji don yaƙi da masu iƙirarin jihadi
Asalin hoton, Getty Images
Ofishin Jakadancin Amurka a Benin ya miƙa wa ƙasar wasu kayyakin aikin soji ga rundunar sojin ƙasar domin ta ƙarfafa yaƙin da ƙasar ke yi da masi iƙirarin jihadi a arewacin ƙasar.
Kafar yaɗa labarai ta 24 Heures au Benin ta ruwaito cewa kayan aikin da Amurkan ta bai wa sojojin ƙasar sun haɗa da tufafin sojoji da motar buldoza a lokacin bikin miƙa kayan da aka gudanar a sansanin sojin ƙasar da ke Guezo.
Shafin Jaridar ya ce tallafin Amurkan zai taimaka wajen ƙarfafa dabarun yaƙin sojojin ƙasar, da kuma tallafa musu a daidai lokacin da suke fuskantar ƙalubalen masu iƙirarin jihadi.
Ko a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ma Amurka ofshin jakadancin Amurkan ya bai wa ƙasar kayan aikin soji na dala miliyan shida, da suka haɗa da motoci masu sulke da riguna masu sulke da kuma na'urorin oba-oba 35.
Ƙasashen Benin da Amurka - waɗanda suka jima suna abota - sun ƙulla wasu yarjejeniyoyi a fannoni har shida, ciki har da tsaron cikin gida da tattara bayanan sirri da lafiya da dabaru yaƙi da kuma yaƙi da ta'addanci.
A baya-bayan nan ƙasashen Afirka da ke gaɓar teku, irin su Benin da Togo da Ghana da Ivory Coast , sun riƙa fuskantar ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi daga ƙasashen yankin Sahel, waɗanda a yanzu suka faɗaɗa hare-haren nasu zuwa makwabtan nasu.
'Harin Isra'ila ya kashe mutum guda a Lebanon'
Ma'aikatar lafiya ta ƙasar Lebanon ta ce wani harin da Isra'ila ta kai kan wata mota a kusa da birnin Sidon ya yi sanadin mutuwar mutum guda.
Isra'ila - wadda har yanzu ba ta ce komai kan lamarin ba - na ci gaba da kai hare-hare kusan kullum a Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da da ta ƙulla da ƙungiyar Hezbollah a watan Nuwamba.
Ta kuma sha alwashin mayar da martani kan duk wata barazana ga sojojinta ko fararen hula daga jami'an Hezbollah.
PDP ba ta shirya wa zaɓen 2027 ba - Wike
Asalin hoton, Nyesom Wike/X
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce babbar jam'iyyar hamayyar ƙasar, PDP ba ta da kyakkyawan shiri da tsarin kayar da APC a zaɓen 2027 ba.
Yayin da yake jawabi a wata ganawa da manema labarai a Abuja, ranar Juma'a, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce a yanayin da jam'iyyar PDP ke ciki a halin yanzu ba za a ce ta shirya wa zaɓen 2027, saboda rikicin shugabanci da jam'iyyar ke ciki.
''PDP ba ta shirya wa zaɓen 2027 ba, wannan a bayyane yake. Ga yadda suke tafiya a yanzu rikicin jagoranci na ci gaba da yi wa jam'iyyar tarnaƙi'', in ji shi.
A baya-bayan nan dai wasu daga jam'iyyun hamayyar ƙasar ciki har da PDp na ƙoƙarin samar da wata haɗaka domin tunkarar APC a 2027.
To sai dai da alama tafiyar na ci gaba da fuskantar tasgaro, saboda muradun wasu ƴansiyasar.
Iran ta yi Allah wadai da harin Amurka kan ƴantawayen Houthi
Asalin hoton, EPA
Iran ta yi Allah wadai da harin Amurka da ta bayyana da na ''jahilci'' kan jirgin dakon mai na ƴantawayen Houthi a tekun Yemen - da ya kashe fiye da mutum 74.
Ƙungiyar wadda ke samun goyon bayan Iran ta ce fiye da mutum 170 ne suka samu raunuka a sanadiyyar harin.
Hotunan da aka yaɗa a gidan talbijin mallakin ƙungiyar, sun nuna yadda ɓaraguzan jirgin ke ƙonewa, yayin da ma'aikatan agaji na ƙungiyar Red Cresent ke ciro gawarwaki daga wurin da lamarin ya faru.
Rundunar sojin Amurka sun ce manufar harin - da aka kai a Tekun Ras Isa - shi ne taƙaita kai wa ƙungiyar kayan aiki da kuɗaɗe.
A watan da ya gabata ne sojojin Amurka suka tsananta hare-hare kan ƴantawayen Houthi.
Muhimmancin ranar ''Good Friday'' a addinin Kirista
Yau Juma'a 18 ga watan Afrilu, rana ce mai matuƙar muhimmanci ga mabiya addinin Kirista, wadda ake yi wa laƙabi da Good Friday a Turance.
Kiristoci sun yi imanin cewa a irin wannan rana ce aka gicciye Yesu Almasihu, kafin daga baya ya taso daga matattu a ranar Lahadi da ta biyo baya.
Rabaren Mati Dangora ya ce rana ce da kowane Kirista zai yi tunani don ba da rayuwarsa ga Ubangiji.
“Ana murnar Esther Monday kuma saboda tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu,” in ji Rabaren ɗin.
Ya ce Good Friday rana ce da ya kamata Kiristoci su yi addu’o’i a majami’u da komawa ga Ubangiji da kuma aikata abubuwan alheri.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Cire Fubara daga gwamnan Rivers na so a yi ba dakatarwa ba - Wike
Asalin hoton, Nyesom Wike/X
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya goyi bayan ayyana dokar ta-ɓaci da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers.
Da yake jawabi ga wasu manema labari a birnin Abuja, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce so ya yi a cire gwamnan jihar Siminalayi Fubara ba dakatarwa ba.
A wani mataki da ke ci gaba da raba kan ƴan ƙasar, shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan Fubara tare da mataimakiyarsa, Ngozi Odu da mambobin majalisar dokokin jihar, bayan kwashe watanni ana dambarwar siyasa a jihar.
Wike ya ce matakin shugaban ƙasar ya ceto jihar daga faɗawa rikici, yana mai cewa naɗa kantoman riƙo a jihar kyakkyawan mataki ne.
Ba da yawunmu wani tsagin tsohuwar CPC ya goyi bayan Tinubu ba - Malami
Asalin hoton, Abubakar Malami
Tsohon Ministan Shari'a na Najeriya, Dakta Abubakar Malami, SAN, ya yi watsi da iƙirarin da wasu ƴan tsohuwar jam'iyyar CPC - da ta narke cikin haɗakar APC - suka yi na nesanta tsohuwar jam'iyyar daga ficewa daga haɗakar.
A farkon makon nan ne wani tsagin tsohuwar jam'iyyar CPC ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Nasarawa, Umaru Tanko Almakura suka yi taro a Abuja, inda suka jaddada goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Tinubu tare da nesanta kansu daga ficewa daga APC.
Daga cikin waɗanda suka harci taron har da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da tsohon ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu da Hon Farouk Adamu Aliyu, tsohon ɗan majalisar daga jihar Jigawa da wasu ƙusushin tsohuwar CPCn.
To sai toshon Ministan ya yi watsi da wannan iƙirari da tsagin Almakuran suka yi, yana mai bayyana matsayar tasu da ta raɗin kai ba da yawun tsohuwar tafiyar CPCn ba.
Cikin wata sanarwa da kakakin tsohon ministan, Muhammad Bello Doka ya fitar, ya ce jagorancin tsohuwar jam'iyyar CPCn ne kawai ke da alhakin fitar da matsayar tsohuwar jam'iyyar kan kan batun fita daga APC, ba tsagin su Almakura ba.
Malami ya zargi Tanko Al-Makura da Adamu Adamu da Aminu Bello Masari da kuma Farouk Adamu Aliyu ya janye jikinsu daga jikin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
Dangane da batun komawarsa jam'iyyar SDP kuwa, Malami ya ce aikin masu yaɗa jita-jita ne, amma ya ce yana kan tattaunawa da magoya bayansa kan batun.
“Malami fitaccen mutum ne a Najeriya, don haka ba zai fice daga jam'iyya a asirce ba, har yanzu yana APC, amma yana ci gaba da tattaunawa da magoya bayansa, idan ya kammala kuma zai bayyana matsayinsa'', in ji kakakin tsohon ministan.
'Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 10 a Khan Yunis'
Asalin hoton, Getty Images
Jami'an agaji a Gaza sun ce hare-haren da Isra'ila ta kai da tsakar dare wayewar yau Juma'a sun hallaka aƙalla Falasɗinawa 10 a kudancin birnin Khan Yunis.
Cikin wata sanarwa da hukumar tsaron fararen hula ta Gaza, Mahmoud Bassal, ya wallafa a shafin Telegram ya ce mutane da dama sun jikkata a lokacin harin.
Sojojin Isra'ila dai ba su ce uffan kan wannan harin ba.
Hukumar ta ce aƙalla mutum 40 ne suka mutu a harin na ranar Alhamis da daddare, da yawansu na zaune ne a sansanonin ƴan gudun hijira.
Amurka ta yi gargaɗin daina ƙoƙarin dakatar da yaƙin Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za ta daina ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine idan ba a ga alamun ci gaba nan da ƴan kwanaki masu zuwa ba.
Marco Rubio ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi bayan ganawa da ƴan siyasar Turai a birnin Paris na ƙasar Faransa.
Ya ce har yanzu Shugaba Trump na fatan cimma yarjejeniyar, amma ya ce akwai sauran abubuwa masu muhimmanci a gaban Amurka.
Da safiyar yau ne Ukraine ta ce ta sanya hannu kan yarjejeniyar ma'adinai da Amurka, sai dai ba ta fitar da bayanan cikakkiyar yarjejeniyar ba.
Sanata Natasha ta buƙaci a mayar mata da jami'an tsaronta bayan kai wa gidansu hari a Kogi
Asalin hoton, Sanata Natasha
Ƴar Majalisar Dattawan Najeriya, mai wakilitar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan - da aka dakatar - ta yi kira ga babban sifeton ƴansandan ƙasar, ya mayar mata da jami'an tsaronta da aka janye mata lokacin da majalisa ta dakatar da ita.
Kiran na zuwa ne bayan da wasu mahara suka auka wa gidan kakanninta da ke jihar Kogi ranar Talatar da ta gabata.
Jaridun Najeriya sun ambato wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran ƴar majalisar ya fitar, na cewa an kai harin ne a lokacin da ƙaninta ya je garin domin duba wani aikin mazaɓu da Natasha ke gudanarwa a garinta na Obeiba-Ihima.
Sanata Natasha ta yi zargin cewa ita aka ƙudiri aniyar kai wa harin, tana mai cewa maharan sun kai harin ne saboda a tunaninsu tana gidan.
Harin ya lalata wasu ɓangarorin gidan, wanda ƴar majalisar ta ce na kakanta ne.
To sai dai jami'an tsaro sun yi asarar daƙile harin, kamar yadda ta yi ƙarin haske.
A watan da ya gabata ne dai Majalisar Dattawan Najeriyar ta dakatar da ƴar majalisar tsawo wata shida, tare da tsayar da alawus-alawus da ake ba ta da jami'an tsaron da ke ba ta kariya, saboda zargin rashin ɗa'a.
Dakatarwar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasar, Sanata Godswill Akpabio da yunƙurin cin zarafi na lalata da amfani da ofishinsa wajen tursasawa da kuma daƙile mata aikinta.
Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta buƙaci jagororin Plateau su haɗa kan al'ummar jihar
Ƙungiyar Gwamnoni ta Najeriya, (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al'ummar jihar mai tarin al'adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.
Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara - Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.
“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al'ummar jihar tare da maido da zaman lafiya mai ɗorewa'', in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.
“Ya kamata shugabannin matasan al'umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,'' a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.
Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.
A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.
Ƴan ƙasar da dama ciki har da shugaban ƙasar, Bola Tinubu sun yi Allah wadai da kashe-kashen.
Faransa da Amurka sun tattauna kan yaƙin Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Faransa da Amurka sun yi tattaunawa mai armashi bayan ganawar kwana guda a birnin Paris, kan yadda za a kawo karshen yakin Ukraine.
Gwamnatin Faransa ta yi maraba da matakin Amurka na sanya Ukraine da Tarayyar Turai cikin shirin tsagaita wuta a yaƙin.
A nasa ɓangaren sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce shirin zaman lafiya da ƙasarsa ta gabatar ya samu karɓuwa.
Daga bisani ya kira takwaranta na Rasha, Sergei Lavrov ta wayar tarho inda suka tattauna batun.
Mista Lavrov ya sake nanata muhimmancin tattaunawa kan ainahin abubuwan da suka haddasa yaƙin na Ukraine.
'Harin Amurka ya kashe mutum 40 a tekun Yemen'
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan tawayen Houthi a Yemen sun ce harin da Amurka ta kai kan jirgin dakon mai a tashar ruwa ta Rasal Isa ya kashe akalla mutum 40, yayin da wasu fiye da 100 sun jikkata.
Hotunan da aka nuna a gidan Talbijin ɗin da Houthi ke tafiyarwa, sun nuna yadda wuta ke ci a jirgin man, ya yin da ma'aikatan ƙungiyar agaji ta Red Crescent ke aikin cire gawarwakin waɗanda suka rasu.
Sojin Amurka sun ce, sun kai harin ne domin hana ƴantawayen Houthi samun kayayyakin da Iran - da ke goyon bayansu - ke tallafa mu su da shi.
Sama da wata guda kenan da sojin Amurka suka zafafa hare-hare kan ƴan tawayen da ke goyon bayan Falasɗinawa.
Assalamu alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa wa