Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na musamman kuma kai-tsaye daga Najeriya da sauran sassan duniya na 10/06/25

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ahmad Bawage, Aisha Babangida da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Mutane da dama sun mutu, wasu sun jikkata a harbi kan makaranta a Austria

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty

    Mutane da dama ne suka mutu wasu kuma suka jikkata a wani harbin bindiga da ya auku a wata makaranta a birnin Graz na Austria, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka ruwaito.

    Rundunar ‘yan sandan ƙasar ta bayyana cewa harbin ya faru ne a wata makarantar sakandare ta tarayya da ke kan titin Dreierschützengasse, a arewa-maso-yammacin birnin Graz, wanda ba shi da nisa da babbar tashar jirgin ƙasa.

    ‘Yan sandan sun ce har yanzu suna kan aikin ceto, kuma an tura jirgin sama mai saukar ungulu zuwa yankin Dreierschützengasse.

    Sun ƙara da cewa an ji ƙarar harbe-harbe a makarantar, kuma sun buƙaci jama’a da su bi umarnin jami’an tsaro.

    Har yanzu dai ba su bayyana adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata ba.

    Ana bai wa ɗaliban da suka jikkata kulawa a ɗakin taro na Helmut List Hall — wanda ke kusa da makarantar, a cewar jaridar Austria ta Kronen Zeitung,

    Graz dai shi ne birni na biyu mafi girma a Austria inda yake da kimanin kilomita 200 daga babban birnin ƙasar, Vienna.

  2. Isra'ila ta buƙaci al'ummomi da ke zaune a yankuna ƙarƙashin ikon Houthi su fice

    Yemen

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta yi kira ga al'ummar da ke zaune a yankunan tashohin ruwan da ke ƙarƙashin ikon mayaƙan Houthi a Yemen da su fice nan take.

    Kakakin rundunar sojin ya buƙaci mutane da su ƙauracewa Ras Isa da Hodeidah da Salif domin tsaron lafiyarsu.

    Ana kallon gargaɗin a matsayin wata sharar fage ta hare-haren Isra'ila kan cibiyoyin da ta ce ƴan Houthi masu samun goyon bayan Iran ke amfani da su wurin harba mata makamai masu linzami.

    Houthi dai ta ce tana kai hare-haren ne domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Gaza.

  3. Trump zai tura ƙarin dakaru kan masu zanga-zangar adawa da kama ƴan ci-rani

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa zai tura ƙarin sojoji guda 2000 da kuma sojojin ruwa har guda 700 zuwa birnin Los Angeles, duk da cewa zanga-zangar nuna adawa da kama ƴan ci-ranin da aka gudanar a ranar Litinin ta gudana cikin lumana.

    Trump ya ce masu zanga-zangar za su fuskanci "matakin da ya fi kowanne tsauri" a wannan karon.

    Sai dai gwamnan jihar California, Gavin Newsom, ya bayyana wannan mataki na tura sojoji a matsayin "hawan ƙawara" da kuma "mulkin kama-karya."

    Yiwuwar ganin sojoji suna sintiri a titunan birnin Los Angeles na haddasa fargaba da tsoro a tsakanin al’ummomin yankin.

    Sai dai jihar California ta shigar da ƙara gaban kotu tana ƙalubalantar matakin Trump, bisa zargin cewa zai aika da dakarun ba tare da izininta ba.

  4. Sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 10 a Zamfara

    ...

    Asalin hoton, @DefenseNigeria

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na hadin gwiwar Operation Fasan Yamma sun kashe ‘yan ta’adda 10 a jihar Zamfara.

    Rundunar ta ce sojojin sun kashe ƴan ta'addan ne a cikin wani mummunan farmaki da suka kai a wuraren da ‘yan ta’addan ke zama a Mai Tashi da Dan Jigba a ƙaramar hukumar Gusau, da kuma Munhaye a ƙaramar hukumar Tsafe a Zamfara, a jiya, 9 ga Yunin 2025.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.

    A yayin wannan aiki, an ƙwato makamai da dama da alburusai.

    Sannan kuma rundunar ta ce an ƙona babura guda 5 da ‘yan ta’addan ke amfani da su a wuraren da aka kai farmakin.

  5. An kashe mutum 570 a Najeriya a watan Afrilu - Rahoto

    Ƴanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce adadin mutum ɗari biyar da saba'in (570) aka kashe a watan Afrilun bana, a cewar wani sabon rahoto da ta fitar.

    Hukumar ta kuma ce mutum ɗari biyu da saba'in da takwas (278) aka yi garkuwa da su daga alƙaluman da ta tattara.

    A shafinta na intanet, hukumar ta ce ta tattara alƙaluman ne daga koken da ta samu na keta haƙƙin ɗan adam daga ofisoshinta da ke sassan Najeriya.

    Rahoton dai ya yi nazari ne tun daga watan Janairun 2025, zuwa watan Afrilun shekarar.

  6. Falasɗinawa a Gaza sun ce an sake buɗe musu wuta a cibiyar raba agaji

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Falasɗinawa a Gaza sun ce an sake buɗe musu wuta yayin da suke hanyarsu ta zuwa wata cibiyar rarraba kayan jin-ƙai ƙarƙashin gidauniyar agaji ta Gaza mai samun goyon bayan Amurka da Isra'ila.

    Shaidu sun ce ba kawai buɗe wuta sojojin Isra'ila suka yi ba, a karon farko wata ƙungiyar mayaƙa ta Falasɗinawa da ke da alaƙa da IDF ta kai masu hari.

    A cewar wakilin BBC, kusan kullum tun bayan da gidauniyar agaji ta Gaza ta soma ayyukanta, ana samun mummunan hari kan cibiyoyin rabon da ta ƙaddamar.

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce mutum shida aka kashe kuma zuwa yanzu rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba.

    A ƴan kwanakin da suka gabata, Firaiministan Isra'ila ya tabbatar cewa ƙasarsa tana mara wa ƙungiyoyin ƴanbindiga a Gaza baya a matsayin hamayya ga Hamas.

  7. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Talata.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeiya da sauran sassan duniya.

    Idan kun shirya ja mu je!