Mutane da dama sun mutu, wasu sun jikkata a harbi kan makaranta a Austria
Mutane da dama ne suka mutu wasu kuma suka jikkata a wani harbin bindiga da ya auku a wata makaranta a birnin Graz na Austria, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka ruwaito.
Rundunar ‘yan sandan ƙasar ta bayyana cewa harbin ya faru ne a wata makarantar sakandare ta tarayya da ke kan titin Dreierschützengasse, a arewa-maso-yammacin birnin Graz, wanda ba shi da nisa da babbar tashar jirgin ƙasa.
‘Yan sandan sun ce har yanzu suna kan aikin ceto, kuma an tura jirgin sama mai saukar ungulu zuwa yankin Dreierschützengasse.
Sun ƙara da cewa an ji ƙarar harbe-harbe a makarantar, kuma sun buƙaci jama’a da su bi umarnin jami’an tsaro.
Har yanzu dai ba su bayyana adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata ba.
Ana bai wa ɗaliban da suka jikkata kulawa a ɗakin taro na Helmut List Hall — wanda ke kusa da makarantar, a cewar jaridar Austria ta Kronen Zeitung,
Graz dai shi ne birni na biyu mafi girma a Austria inda yake da kimanin kilomita 200 daga babban birnin ƙasar, Vienna.