An shiga rana ta uku a tarzomar Los Angeles kan kamen baƙin haure

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake yi a birnin Los Angeles na jihar California ta Amurka inda masu zanga-zanga ke dauki-ba-dadi da dakarun tsaron kasa da Shugaba Trump ya tura tun farko domin kwantar da zanga-zangar da ta barke sakamakon kamen bakin aure.

Dakarun tsaron da Shugaban ya tura sabanin ra'ayin gwamnan jihar da kuma shugabar birnin suna amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashin roba wajen tarwatsa masu tarzomar.

Yayin da zanga-zangar da ta rikide ta zama tarzoma ta shiga kwana na uku, lamarin na ci gaba da kazanta inda masu tarzomar suke kona motoci da tayoyi kuma dakarun tsaron da 'yansanda da ke artabu da su, sun kama gommansu.

Shugaba Trump ya bayyana masu tarzomar da gungun masu tayar da hankali da tawaye, yana mai cewa dole ne a tabbatar da doka da oda.

To amma kuma gwamnan jihar Gavin Newsom, wanda ya zargi shugaban da rura wutar rikicin, bayan da ya bayar da umarnin tura dakarun tsaron kasa dubu biyu, da keta haddin 'yancin jihar, ya yi barazanar shigar da gwamnatin tarayyar kara.

Gwamnan ya ce tun da farko sun ce babu dalilin tura dakarun domin 'yansandan jihar sun iya kwantar da zanga-zangar kafin ta fara girma, amma umarnin shugaban kasar na tura dakarun ya kara harzuka jama'a.

A ka'ida ana tura dakarun tsaron kasa ne bisa bukatar gwamnan jiha, a don haka gwamnan ya soki Trump da kauce wa wannan ka'ida ya bayar da umarnin tura dakarun ba tare da bukatar hakan ba daga gwamnan, inda Mista Newsom ya ce shugaban ya yi wa doka dan-waken zagaye – ya keta tsarin mulki.

Mista Newsom wanda ya ce Los Angeles ta kasance cikin kwanciyar hankali ya yi kira a sanarwar da ya fitar da cewa ''kada jama'a su bari su fada tarkon masu tsattsauran ra'ayi.''

Gwamnonin jihohi 22 na jam'iyyar Democrat sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suke nuna goyon bayansu ga gwamnan jihar.

Yayin da aka shiga dare 'yansandan birnin sun ce masu zanga-zangar sun karkasu zuwa wasu sassan birnin

Rundunar 'yansandan na gargadin mazauna birnin da masu harkokin kasuwanci da masu ziyara a kan su kula sosai tare da bayar da rahoton duk wani abu na mugun laifi da suka gani.

'Yansandan a kan dawaki da motoci na ta kokarin kawar da masu zanga-zangar da sauran tarkace da ke warwatse wadanda aka kona a tituna sakamakon zanga-zangar.