Jamus na neman wuce matakin rukuni a karon farko tun gasar 2014, Jamus v Ivory Coast
Nasarar da Jamus ta yi a kan Curacao ta yi daidai da yadda ta caskara Brazil 7-1 a wasan kusa da na ƙarshe a 2014 — karo na ƙarshe da ta lashe kofin — kuma hakan ya sa suka wuce Brazil (Selecao) a matsayin ƙasar da ta fi zura kwallaye da yawa a raga a wasa a tarihin kofin duniya da kwallaye 239.
Idan ta doke Ivory Coast ranar Asabar a wasa na biyu a cikin rukuni na biyar, za ta samu gurbin zuwa zagayen ƴan 32 — to shin za su iya wuce matakin rukuni a karon farko cikin shekaru 12?

Asalin hoton, Getty Images















