Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/10/2024

Wannan shafi en da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Abdullahi Bello Diginza

  1. Majalisa ta amince a gudanar da ma'aikatar raya yankunan Najeriya da wani kaso na kuɗin jihohi

    Akpabio

    Asalin hoton, President of the Senate/X

    Majalisar dattawan Najeriya ta amince a riƙa cire kashi 15 na kuɗaɗen gudanar da ma'aikatar raya yankunan ƙasar daga asusun jihohin ƙasar.

    A ranar Alhamis ne Majalisar ta amince da ƙudirin bayan la'akari da rahoton kwamitin majalisar kan ayyuka na musamman, wanda shugaban kwamitin Sanata kaka Shehu ya gabatar.

    Wannan batu dai ya haifar da zazzafar muhawara a zauren majalisar, inda wasu 'yan majalisar suka nuna adawa da matakin.

    Sanata Yahaya Abdullahi, daga jihar Kebbi ya ce matakin zai sa gwamnatocin jihohi su yi ta shigar da gwamnatin tarayya ƙara, saboda a cewarsa babu jihar da za ta so a riƙa yanke mata kuɗi da nufin ɗaukar nauyin wata ma'aikata ta tarayya.

    To sai dai mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano ya kore fargabar takwaran nasa.

    Yana mai cewa ba wai yanke kuɗaɗen jihohin za a yi ba, a maimakon haka kashi 15 cikin 100 na gudanar da ma'aikatar jihohin za su bayar, yayin da gwamnatin tarayya za ta bayar da ragowar.

    A ranar Laraba ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanar da kafa sabuwar ma'aikata da za ta kula da sauran hukumomin raya yankuna, bayan rushe ma'aikatar raya yankin Naija Delta.

    A yanzu ƙasar na da hukumomin raya yankuna da suka haɗa da ta yankin Naija Delta da ta arewa maso gabas da ta arewa maso yamma, da kuma ta kudu maso gabas.

  2. Kotun Uganda ta yanke wa tsohon kwamandan LRA hukuncin ɗaurin shekara 40

    An yanke wa tsohon kwamandan mayaƙan ƙungiyar 'yan tawayen Uganda ta 'Lord’s Resistance Army', Thomas Kwoyelo, hukuncin ɗaurin aƙalla shekara 40 sakamakon samunsa da aikata laifukan yaƙi a arewacin Uganda da wasu makwabtan ƙasashe.

    Kotun hukunta manyan laifuka ta Uganda ta kauce wa yanke wa mista Kwoyelo hukuncin kisa ko ɗaurin rai da rai, saboda shekarunsa a lokacin da 'yan tawaye suka kama shi, kafin daga baya ya zama soja.

    A lokacin kotun ta ce mista Kwoyelo ya nuna nadamar abin da ya aikata, kuma bai nuna alamun sake zama barazana ga al'umma ba.

    Yanzu dai kotun ta same shi da laifuka 44 cikin tuhume-tuhume 78 da ake yi masa, da suka haɗa da kisan kai da fyaɗe da garkuwa da mutane da kuma sata.

    Da wannan hukuncin za a kwashe shekara 15 da ya riga ya yi a lokacin zaman jiran shari'ar.

    Hakan na nufin a yanzu zai kwashe shekara 25 a gidan yarin bisa wanna hukunci.

    To sai dai lauyoyinsa sun ce za su ɗaukaka ƙara game da hukuncin, inda kotun ta ba su wa'adin mako biyu domin yin hakan.

    Thomas Kwoyelo ne ɗan ƙungiyar LRA na farko da aka yanke wa hukunci a Ugandan court.

    Kungiyar ta yi fice wajen garkuwa da ƙananan yara tare da tilasta musu shiga aikin soji ko karuwanci.

  3. Harin Isra'ila ya kashe 'yan jaridar Lebanon uku

    motar 'yan jarida

    Asalin hoton, Reuters

    Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wani gida - wanda 'yan jarida ke zama a ckinsa a kudu maso gabashin Lebanon - ya kashe 'yan jarida uku, kamar yadda shaidu suka bayyana wa BBC.

    An kai harin ne kan gidan saukar baƙi - wanda gomman 'yan jarida na kafofin yaɗa labarai aƙalla bakwai ke amfani da shi - a Hasbaya da ke kudancin lebanon.

    Harabar gidan cike take da motocin da aka rubutawa alamar na 'yan jarida ne (Press) ƙarara a jikinsu.

    'Yan jaridar uku da aka kashe ma'aikatan gidajen talbijin na Al-Manar TV da Al Mayadeen TV ne a ƙasar, wadanda tuni suka fitar da saƙon ta'aziyya ga ma'aikatan nasu.

    Ministan yaɗa labaran Lebanon ya ce da gangan aka kai harin - wanda ya bayyana da ''laifin yaƙi''.

    Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba, to amma a baya ta sha musanta zargin kai wa 'yan jarida hare-hare.

  4. Ana ci gaba da neman mutanen da hatsarin jirgi ya rutsa da su a Rivers

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban anjeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin tsananta ƙoƙari domin gano tare da ceto mutane da hatsarin jirgi ya rutsa da su a Fatakwal.

    Kamfanin mai na NNPCL ne ya ɗauki shatar jirgin mai saukar ungulu domin kai wasu ma'aikatan kwangila wata rijiyar man kamfanin da ke gaɓar teku.

    An tabbatar da mutuwar mutum uku daga cikin mutum takwas da ke cikin jirgin.

  5. Tinubu ya buƙaci sojoji su kawo ƙarshen matsalar 'yanbindiga a arewa maso yamma

    Shugaban Najeriya

    Asalin hoton, Bola Tinubu/X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci dakarun ƙasar da ke yaƙi da 'yan bindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar, su kawo ƙarshen matsalar nan ba da jimawa ba.

    Ministan tsaron ƙasar Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka lokacin wata ziyara da ya kai shalkwatar rundunar Operation Fansar Yamma mai yaƙi da 'yan bindigar da ke jihar Zamfara.

    Badaru ya ce ''shugaban ƙasa na matuƙar damuwa da matsalar rashin tsaro da jihar zamfara ke fuskanta, kuma ya umarci sojojin ƙasar su kawo ƙarshen matalar a yankin arewa maso yammacin ƙasar baki ɗaya''.

    A lokacin ziyarar ministan ya yaba da irin tsare-tsaren sojojin da ke yaƙi da 'yan bindigar tare da umartarsu su ci gaba da farautar manyan shugannin 'yan bindigar yankin.

    Ministan ya kuma ziyarci gidan gwamnatin jihar, inda ya tattauna da gwamnan jihar kan batutuwan da suka shafi tsaro a faɗin jihar.

    Badaru

    Asalin hoton, Ministry of Defence

    Bayanan hoto, Ministan tsaron Najeriya Muhammad Badaru Abubakar
    Badaru

    Asalin hoton, Ministry of Defence

    Bayanan hoto, A lokacin ziyarar, ministan ya yaba wa shirye-shiyen sojojin ƙasar a Zamfara
    Badaru da shugaban runddunar Opration fansan yamma

    Asalin hoton, Ministry of Defence

    Bayanan hoto, Ministan tsaro da shugaban rundunar Operation Fansan Yamma mai yaƙi da 'yan bindiga
    Badaru da Dauda Lawan Dare

    Asalin hoton, Minsitry of Defence

    Bayanan hoto, Ministan ya kuma ziyarci fadar gwamnatin jihar domin tattaunawa da gwamna kan matsalar tsaro a Zamfara
  6. Shettima ya fasa zuwa taron Samoa saboda lalacewar jirgi

    Mataimakin Tinubu

    Asalin hoton, Stanley Nkwocha/X

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya fasa zuwa taron ƙungiyar ƙasashen renon Ingila ta Commonwealth na 2024 da za a gudanar a tsibirin Samoa, bayan da jirginsa ya samu a matsala a lokacin da ya yada zango a Amurka.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ya ce a lokacin da jirgin ya yada zango a birnin New York na Amurka, wani abu daga waje ya daki jirgin wanda kuma ya lalata gilas ɗin direban jirgin.

    Sanarwar ta ce tuni shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da shirya wata tawagar ministoci, ƙarƙashin jagorancin ministan muhalli, Balarabe Abbas Lawal domin wakiltar Najeriya a taron, yayin da ake ci gaba da gyaran jirgin mataimakin nasa.

    An dai fara taron ne ranar 21 ga watan Oktoba, wanda kuma ake sa ran kammala shi ranar 26 ga watan Oktoba a tsibirin da ke tekun Pacific.

    Sanarwar ta ce mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima tare da tawagarsa da ta ƙunshi ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar sun kama hanyar komawa Najeriya daga Amurka.

  7. Babu wa'adin amfani da tsoffin takardun kuɗi - CBN

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi watsi da raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa a ƙasar cewa daga ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa za a daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar ranar Alhamis ya ce wannan iƙirari ba gaskiya ba ne kuma ba shi da tushe balle makama.

    ''Bisa hukuncin ci gaba da amfanin da tsoffin takardun kuɗin da kotun ƙolin Najeriya ta yi a ranar 29 ga watan Nuwamban 2023, ta ce a ci gaba da amfani da takardun ba tare da iyakancewa ba'', in ji sanarwar.

    Haka kuma sanarwar ta yi kira ga bankunan ƙasar su ci gaba da mu'amala da tsoffin takardun kuɗin.

    Matakin na zuwa ne kwana guda bayan majalisar wakilan ƙasar ta yi kira ga CBN ɗin ya fara shirye-shiryen janye tsoffin takardun kuɗin daga zagayawa.

    A shekarar 2022 ne dai tsohuwan gwamnatin Muhammadu Buhari, ta ɓullo da sabbin takardun kuɗin ƙasar na naira 200, da 500 da 1,000, sannan ta bayar da wa'adin daina amfani da tsoffin zuwa ƙarshen shekarar.

    Batun ya haifar da ruɗani da tayar da hankali, inda daga baya wasu jihohin ƙasar suka shigar da ƙara a gaban kotun ƙolin ƙasar, wadda kuma ta jinkirta wa'adin, zuwa wani lokaci, inda daga baya ma ta ce a ci gaba da amfani da su ba tare da iyakancewa ba

  8. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye barkanmu da wannan rana ta Juma'a, wato Haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.