Labarin wasanni daga 29 zuwa 5 ga watan Disamba 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 29 zuwa 5 ga watan Disambar 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Suarez

    Asalin hoton, Getty Images

    Crystal Palace da Fulham na cikin jerin ƙungiyoyin da ake saka ido kan ɗan wasan Watford Rocco Vata, 20. Suna son siyen ɗan wasan kan fam miliyan 20. (Mail)

    Spurs na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan da itama Manchester United ke son ɗaukowa daga Brighton Carlos Baleba, mai shekaru 21. (Caught Offside, via the Daily Briefing)

    Brighton za ta rufe ƙofar dukkan wani tayi kan ɗn wasan ta Jack Hinshelwood, daga Nottingham Forest f(Football Insider)

    Ana sa ran Tsohon ɗan wasan Real Madrid Sergio Ramos, zai bar ƙungiyarsa ta Monterrey da ke Mexico, sai dai babau wani shiri na yin ritaya. (Marca - in Spanish)

    An fara jin ƙishin-ƙishin ɗin cewar ɗan wasan gaban Igila Ivan Toney, 29, hzai iya komawa taka leda a gasar Premier League, yayin da aka fara .ƙinshin ƙishin cewar zai bar ƙungiyarsa ta Al-Ahly a watan Janeru baɗi. (Talksport)

  2. Isak ya ci ƙwallon farko a Premier League a Liverpool

    Liverpool

    Asalin hoton, Reuters

    Alexander Isak, wanda Liverpool ta sayo a farashi mafi tsada a tarihin ta, ya zura kwallonsa ta farko a Premier League tun bayan komawarsa Anfield kan fara kakar nan, yayin da mai rike da kofin ta doke West Ham 2-0 ranar Lahadi.

    Liverpool ta shiga mawuyacin lokaci mafi muni cikin fiye da shekaru 70, wadda ta sha kashi a wasa tara daga cikin 12 da ta buga a baya.

    Kociya, Arne Slot ya fara da dauki mataki mai tsauri, inda ya fara da ajiye Mohamed Salah a benci — karo na farko a Premier League.

    Isak, wanda baya kan ganiya tun da aka fara kakar nan ya ɓarar da damarmaki tun kan hutu.

  3. AC Milan ta doke Lazio ta koma kan teburin Serie A

    Milan

    Asalin hoton, Getty Images

    Rafael Leao ya ci ƙwallon da ya mayar da AC Milan kan teburin Serie A, bayan nasara a kan Lazio ranar Lahadi

    Ɗan kasar Portugal ya yi nasarar cin ƙwallo, bayan da ya samu daga wajen Fikayo Tomori a lokacin da asuka yi hutu suka koma zagaye na biyu.

    Lokacin da wasa ke dab da karewa, Alessio Romagnoli ya buga ƙwallo ta taɓa hannun Strahinja Pavlović, amma bayan da aka duba a (VAR), ba a ba da bugun fanareti ba, lamarin da ya fusata ’yan wasan Lazio.

    Kociyyin Milan, Massimiliano Allegri, an bashi jan kati a fafatawar.

    Da wannan sakamakon Milan ta koma ta ɗaya a kan teburi da tazarar maki ɗaya tsakani da Roma, wadda za ta fuskanci Napoli ranar Lahadi da dare.

  4. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City, da Tottenham da Liverpool na son ɗaukar ɗan wasan Everton mai shekaru 25 Iliman Ndiaye. (Foot Mercato - in French)

    Manchester United cike da yaƙinin daukar ɗan wasan Crystal Palace Adam Wharton kan fam miliyan 70, a kakar wasannin mai zuwa, sai dai dan wasan mai shekaru 21, ba zai je Man United ɗin baida har basu yi nasarara samun damar buga wasannan Euro ba. (Mirror)

    Newcastle na shirye-shirye wajen ganin sun ɗauko ɗan wasan Raphinha a kakar wasanni mai zuwa daga Barcelona, idan har sun yake shawarar siya da dan wasan mai shekaru 28. (Fichajes - in Spanish)

    Ɗan wasan Nottingham Forest kuma ɗan ƙasar Brazil Murillo, mai shekaru 23, na cikin manyan cefanen da Barcelona ke son yi, don ingnata tsaron bayan ta a kakar wasanni mai zuwa. (Fichajes - in Spanish)

    Aston Villa na son ɗaukar ɗan wasan Igor Thaigo na Brentford da ya ciyo mata ƙwallaye 11 a gasa Premier League ɗin bana, kan fam miliyan 50. (Mirror)

  5. Manchester United ta je ta ci Crystal Palace a Premier

    United

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta koma cikin ƴan shidan teburin Premier League, bayan da ta je ta doke Crystal Palace 2-1 a Selhurst Park ranar Lahadi.

    Jean-Philippe Mateta ne ya fara ci wa Palace ƙwallo a bugun fenariti a minti na 36 da fara tamaula, bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu United ta farke ta hannun Joshua Zirkzee, sannan Mason Mount ya kara na biyu.

    Rabonda United ta ci ƙwallo a filin nan tun bayan da Anthony Martial ya ci Palace a Julin 2020, sai dai rabon da ta yi nasara tun bayan wadda Bruno Fernandes ya zura a raga a Janairun 2023.

    Da wannan sakamakon United ta kawo karshen wasa uku ba tare da nasara ba a Premier League, bayan da ta yi canjaras biyu aka doke ta ɗaya.

  6. Inter Miami za ta buga wasan karshe da Whitecap a MLS Cup

    Messi

    Asalin hoton, EPA

    Lionel Messi ya taimaka wa Inter Miami ta kai wasan karshe na MLS Cup da za su kece raini da Vancouver Whitecaps, bayan duka kungiyoyin sun lashe wasan da ya kaisu zagayen karshe.

    Inter Miami ta doke New York City 5-1, inda Messi ya bayar da kwallo aka zura a raga, yayin da takwaransa, Tadeo Allende ya zura uku daga ciki da hakan ya sa suka zama zakarun shiyyar Gabashi.

    Ita kuwa Vancouver Whitecaps ta yi nasarar doke San Diego FC 3-1, inda tsohon dan wasan Jamus da Bayern Munich, Müller, ya jagorance su zuwa lashe kofin shiyyar Yammaci.

    Inter Miami za ta karɓi bauncin Whitecaps a ranar Asabar, 6 ga Disamba, zai zama karo na farko da kowace daga cikin za ta kara a wasan karshe a MLS Cup.

  7. Me kuke son sani kan wasan Chelsea da Arsenal a Premier League?

    Premier Laegue

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea za ta karɓi bakuncin Arsenal a wasan mako na 13 a Premier League da za su kece raini a Stamford Bridge ranar Lahadi.

    Arsenal tana matakin farko a kan teburi da maki 29, wadda ta ci wasa tara da canjaras biyu aka doke ta wasa ɗaya daga fafatawa 12 a Premier League.

    Ita kuwa Chelsea, wadda ta yi nasara bakwai da canjaras biyu aka doke ta karo uku tana ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 23.

    Wasan da suka buga a bara wato 2024/2025

    Premier League ranar Lahadi 16 ga watan Maris 2025

    • Arsenal 1 - 0 Chelsea

    Premier League ranar Lahadi 10 ga watan Nuwamba 2024

    • Chelsea 1 - 1 Arsenal.

    Waɗanda za su yi alkalancin wasan

    Rafli: Anthony Taylor

    Mataimaki na farko: Gary Beswick

    Mataimaki na biyu: Adam Nunn

    Mai jiran ko-ta-kwana: Samuel Barrott

    Wanda zai kula da VAR: John Brooks

    Mataimakinsa: Edward Smart

    Bangaren Chelsea

    • Chelsea ta yi nasara ɗaya daga wasa 11 baya da ta kara da Arsenal da canjaras uku aka doke ta bakwai, kuma ba ta ci wasa bakwai ba tun bayan nasarar doke Gunners 2-0 a Emirates cikin watan Agustan 2021.
    • Cikin makin da Chelsea ta samu kaso 43.5 cikin 100 a Stamford Bridge ne wato 10 daga cikin 23, wadda take da karancin haɗa maki a gida ita ce Tottenham mai kaso 28 cikin 100.
    • Chelsea kan fara cin ƙwallo a wasa bakwai baya a Premier League - karon farko da ta jere ta ci ƙwallaye a wasa da yawa tun bayan Afirilun 2024, shima karo bakwai daga baya Arsenal ta taka mata burki da doke ta 5-0.
    • Pedro Neto yana da hannu a cin ƙwallaye a wasa biyar a Premier League, wanda ya ci uku ya bayar da biyu aka zura a raga - yana fatan zura ƙwallo a wasa na uku a jere a karon farko.
    • Ɗan kasar Portugal yana da hannu a cin Arsenal ƙwallo uku daga wasa huɗu baya, wanda ya ci biyu ya kuma bayar da ɗaya a ka zura a raga, shi ne ya farke ƙwallon da aka ci Chelsea a bara a gasar.

    Bangaren Arsenal

    • Wannan shi ne karo na biyar da za a buga wasan na hamayya da Arsenal ke saman Chelsea a teburin Premier, kuma Gunners ta lashe dukkan karawa huɗun baya.
    • Arsenal ta ci Chelsea 3-2 a Janairun 2003 a gida
    • Gunners ta yi nasarar cin Chelsea 2-1 a Fabrairun 2004 a waje.
    • Arsenal ta doke Chelsea 1-0 a Disambar 2007 a gida
    • Arsenal ta ci Chelsea 5-0 a cikin Afirilu 2024 a gida.
    • Bayan da Arsenal ta yi rashin nasara bakwai a Premier League a hannun Chelsea tsakanin 2013 zuwa 2018, yanzu dai Gunners ta yi karawa shida ba tare da an doke ta ba a fafatawa da Chelsea, inda ta ci uku da canjaras uku.
    • Tun daga kakar 2022/23, wasa uku aka ci Arsenal daga 40 a fafatawar hamayya ta ƴan birnin Landan a Premier League daga ciki ta yi nasara 28 da canjaras tara - ɗaya daga rashin nasara ukun har da wanda Fulham ta ci 2-1 a Disambar 2023.
    • Wasan farko da aka ci Mikel Arteta a matakin kociyan Arsenal shi ne a hannun Chelsea a fafatawarsa ta biyu a cikin Disambar 2019 - duk da haka ɗan kasar Sifaniya shi ne na uku a yawn doke Chelsea mai kaso 58.3 daga wasa 10 ko fiye da haka, biye da Pep Guardiola mai kaso 61.1 cikin 100 da kuma na farko Kenny Dalglish mai 76.9 cikin 100.
    • Ƙyaftin ɗin Arsenal, Martin Odegaard ya ci Chelsea ƙwallo biyu da bayar da biyar aka zura a raga, shi ne kan gaba mai hannu a cin ƙungiyar Stamford Bridge a Premier League mai bakwai kawo yanzu.
    • Haka kuma Odegaard da Gabriel Magalhaes, ba su taba rashin nasara a wasan Chelsea, Arsenal ta ci shida da canjaras biyu tare da su a cikin fili, yayin da Patrick Vieira ne kan gaba a wasa 10 ba tare da Chelsea ta yi nasara ba a kan Gunners yana cikin fafatawar.
  8. Parmer ya warke zai iya fuskantar Arsenal ranar Lahadi - Maresca

    Palmer

    Asalin hoton, Getty Images

    Cole Palmer ya murmure zai kuma iya buga wa Chelsea wasan hamayyar da Arsenal ranar Lahadi a Premier League mako na 13 a Stamford Bridge in ji koci, Enzo Maresca.

    Ɗan wasan mai shekaru 23 ya karya yatsan ƙafa ne, bayan tuntuɓe da ƙofa a makon da ya gabata, wanda ya sa bai buga wa ƙungiyar fafatawar da ta doke Burnley a Premier da kuma Barcelona a Champions League.

    Dan ƙwallon tawagar Ingila ya yi ta fama da jinya a wannan kakar, wanda ya buga wasa biyar a dukkan karawa a kakar nan.

    Wasan karshe da Palmer ya buga shi ne wanda Chelsea ta doke Manchester United 2-1 a Old Trafford ranar 20 ga watan Satumba - tun daga lokacin ƙungiyar Stamford Bridge ta yi karawa 13 da cin 10 daga ciki da shan kashi biyu da canjaras ɗaya.

    Palmer ya koma Chelsea daga Manchester City kan fam miliyan 40 a Satumbar 2023, ya zama gwarzon cin kwallo na ƙungiyar mai 22 a kakarsa ta farko, sannan ya zura 15 a raga a kaka ta biyu.

    Rashin Palmer sai Estevao Willian, ya haskaka da cin ƙwallo biyar, kuma Maresca ya ce zai iya amfani da su tare a cikin fili a fafatawar da Arsenal ta ƴan birnin Landan.

  9. Vinicius

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan Brazil Vinicius Jr na dab da rattaba hannu kan wani sabon kwantaragi da Real Madrid bayan ya rage yawan kudin da yake son a biya shi. Kwantaragin dan wasan mai shekara 25 na yanzu zai zo karshe ne a watan Yunin 2027 (Mundo Deportivo)

    Manchester United ta tuntubi wakilan Vinicius Jr, kuma watakila Manchester City ta bi sahunsu idan dan wasan ya yanke shawarar barin kungiyar ta La Liga . (Caught Offside via The Daily Briefing)

    Watakila Liverpool ta sayi dan wasan Bournemouth Antoine Semenyo a watan Janairu ko ta jira har zuwa lokacin bazara lokacin da ake sa ran Manchester City za ta shiga kasuwa don siyan dan wasan na Ghana mai shekara 25.(i Paper),

    Tsohon kocin Nottingham Forest Ange Postecoglou da kuma tsohon kocin Celtic Brendan Rodgers na cikin wadanda ake ganin za su maye gurbin kocin Leeds United Daniel Farke wanda ke ci gaba da fuskantar matsin lamba. (Talksport),

    Manchester City ta bi sahun Arsenal wajen duba dan wasan Elche dan kasar Sifaniya, Rodrigo Mendoza, mai shekara 20, inda ita ma Real Madrid ke zawarcinsa (Mail, external)

  10. Bayern ta doke St Pauli ta ci gaba da jan ragamar teburin Bundesloga mako na 44

    Bayern

    Asalin hoton, Getty Images

    Wadda ke jan ragamar teburin Bundesliga, Bayern Munich, ta doke St Pauli, kuma biyu daga ciki daf a tashi ta zura su a raga.

    Minti shida da take Leda St Pauli ta fara cin ƙwallo ta hannun Andreas Hountondji, wanda ke buga wasannin aro daga Burnley.

    Haka kuma Lennart Karl da Tom Bischof daga St Pauli sun buga ƙwallo ya bugi turke kowannensu a karawar ta Allianze Arena.

    Daf da za a je hutu ne Luis Diaz, ya taɓa kwallo da tafin ƙafarsa zuwa ga Raphael Guerreiro wanda bai ɓata lokaci ba ya farkewa Bayern Munich.

    Haka kuma Harry Kane ya buga ƙwallo ya bugi turke.

    Ana shiga minti uku na karin lokaci, tsohon ɗan wasan Liverpool, Diaz ya kara na biyu daga baya Nicola Jackson, wanda ya shiga wasan daga baya ya kara na uku a minti na shida da karin lokaci.

    Da wannan sakamakon Bayern ta yi nasara 11 a Bundesliga ta bana da kunnen doki - wasa ɗaya aka doke ta daga 19 a dukkan fafatawa a bana, shi ne da Arsenal ta yi nasara 3-1 a Champions League a makon jiya.

  11. Newcastle

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwantiragin kocin Brazil Carlo Ancelotti zai kare bayan gasar cin Kofin Duniya ta 2026 amma ana tattaunawa kan tsawaita shi.(ESPN), external

    Kungiyar Sheffield Wednesday na nazari kan tsohon dan wasan Middlesbrough Duncan Watmore, mai shekara 31, wanda ke atisaye tare da Owls.(Sky Sports News),

    Leeds United ta nemi a ba ta Kalvin Phillips, mai shekara 29, a matsayin aro daga Manchester City amma da wuya yarjejeniyar ta kasance, kuma wannan ya sa dan wasan na Ingila ba shi da wani zabi illa ya yi la'akari da tayin daga Faransa, da Sifaniya da Jamus.(Mirror)

    Nottingham Forest ta yi bincike tare da Pogon Szczecin game da samun dan wasan Poland Adrian Przyborek, mai sekara 18.(Teamtalk).

  12. Monaco ta ci Paris St Germain a Ligue 1 ranar Asabar

    Monaco

    Asalin hoton, Getty Images

    Takumi Minamino ne ya zura kwallo ɗaya tilo a lokacin da Monaco ta doke mai rike da Ligue 1, Paris St-Germain.

    Ɗan wasan Japan ya ci ƙwallon daga tazarar yadi 16.

    Sai dai kuma mai masaukin baki ta kammala fafatawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Thilo Kehrer jan kati, saboda ƙetar da ya yi wa Ibrahim Mbaye, bayan da VAR ta tabbatar da laifin.

    Monaco ta saka Paul Pogba a ƙarshen wasa, yi mata wasansa farko a gida tun komawarsa ƙungiyarsa, kuma karo na biyu da ya taka mata leda a bana, karon farko tun bayan fiye da shekara biyu da aka dakatar da shi kan laifin shan abubuwan kara kuzarin wasa.

    Monaco ta yi sama zuwa matsayi na shida a teburin Ligue 1, yayin da PSG za ta iya rasa matakin farko ga Marseille daga baya.

    Marseille, wadda take biye da PSG da tazarar maki biyu, za ta kece raini da Toulouse a dai ranar Asabar.

  13. Olmo ya mayar da Barcelona kan teburin La Liga

    Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta yi nasarar doke Deportivo Alaves 3-1 a gasar La Liga da suka kara ranar Asabar.

    Lamine Yamal ne ya farke wa Barcelona ƙwallon, sannan Dani Olmo ya kara biyu a karawar, yayin da Alaves ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Pablo Ibáñez a minti ɗaya da take leda a Camp Nou.

    Da wannan sakamakon Barcelona ta koma ta farkon teburi da maki 34 da tazarar biyu tsakani da Real Madriid, wadda za ta kece raini da Girona ranar Lahadi.

    A wasan da Barcelona ta yi nasara, mai shekara 23, Pedri ya buga karawar a karon farko sama da wata ɗaya da ya sha jinya.

    Barcelona ta saka shi, bayan da aka shiga zagaye na biyu, kenan ƙungiyar ta samu ƙwarin gwiwa a shirin da take na fuskantar Athletico Madrid ranar Talata.

    Athletico, wadda take ta huɗu a teburin La Liga da maki 28, ba ta yi rashin nasara ba a La Liga tun daga cikin watan Agusta.

  14. Manchester City ta koma ta biyun teburin Premier Leeague

    City

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City ta koma ta biyun teburin Premier League bayan da ta doke Leeds United 3-2 a wasan mako na 13 da suka kara a Etihad ranar Asabar.

    Phil Foden ne ya fara cin ƙwallo a minti na ɗaya da take leda, kuma wanda aka ci a ƙanƙanin lokaci a tarihin Premier League a kakr nan.

    Minti 25 tsakani City ta kara na biyu ta hannun Josko Gvardiol, haka aka je hutu ƙungiyar Etihad na cin 2-0.

    Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Leeds ta kara sa ƙwazo da ta kai ta farke biyun ta hannun Dominic Calvert-Lewin da kuma Lukas Nmecha.

    Sai dai kuma daf a tashi Poden ya kara na biyu daf a tashi da hakan ya sa ta samu maki ukun da take bukata.

    Kenan City ta yi nasara ta takwas a kakar nan da canjaras ɗaya da rashin nasara huɗu da maki 25, kenan ta koma ta biyun teburin babbar gasar tamaula ta Ingila

    Har yanzu Erling Haaland bai ci ƙwallo na 100 ba a Premier League, wanda ya zura 14 a kakar nan na neman cikin ta 100, domin ya zama wanda ya yi wannan bajintar a wasa 109.

    Mai rike da tarihin shi ne Alan Shearer mai ƙwallo 100 a wasa 124.

    City za ta je gidan Fulham a zagayen mako na 14 a Premier League.

  15. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.