Fiorentina ta kori kociyanta Pioli

Asalin hoton, Getty Images
Fiorentina ta kori Stefano Pioli, kamar yadda mai buga Serie A ta sanar ranar Talata. bayan kasa cin wasanni da hakan ya kai ƙungiyar karshen teburin gasar.
Pioli ya sake karɓar aikin kocin a karo na biyu a cikin watan Yuli, sai dai maki huɗu Fiorentina ta samu daga wasa 10 - kaka mafi muni da ƙungiyar ta samu kanta a babbar gasar tamaula ta Italiya, kuma hakan ya sa magoya baya suka yi ta zanga-zanga.
An sanar da cewar Daniele Galloppa ne zai karɓi aikin horar da Fiorentina a matakin rikon ƙwarya nan take.
Haka kuma tun a ranar Asabar daraktan wasannin ƙungiyar, Daniele Prade ya yi murabus.
Wasan karshe da Pioli ya ja ragama shi ne ranar Lahadi da Lecce ta yi nasara a Serie A.
Pioli, wanda ya lashe Serie A tare da AC Milan a 2022, ya karɓi aikin kwantiragin kaka uku a Fiorentina, bayan maye gurbin Raffaele Palladino wanda ya bar ƙungiyar mako uku da fara aikin daga watan Mayu.
Fiorentina za ta kai ziyara Jamus, domin karawa da Mainz 05 ranar Alhamis a Conference League a gasar da Pioli ya ci wasa biyu.
Haka kuma ranar Lahadi Fiorentina za ta je Genoa a gasar Serie A.
















