Yaƙin Iran da Isra'ila zai iya sa a manta da wahalar da muke ciki - Falasɗinawa

Asalin hoton, Reuters
A Gaza, falaɗinawa na bayyana ra’ayoyinsu dangane da sabon rikici tsakanin Iran da Isra’ila.
Wasu sun nuna jin daɗin ganin hare-haren Iran sun shafi Isra’ila, amma da dama sun ce hakan yana ƙara kau da hankalin duniya daga wahalhalun da suke ciki tsawon watanni 20.
Hassan Omar Talba, wanda ya rasa iyalinsa a harin Isra’ila, ya bayyana taƙaici dangane da irin tallafin da Iran ke iƙirarin bayarwa a Gaza.
“Iran ba ta taɓa gina makaranta ko asibiti ko aika da motar bayar da agaji zuwa Gaza ba,” in ji shi.
“Abin da suka yi kawai shi ne aika roka da marawa Hamas baya, wanda hakan ya kara dagula rayuwarmu.”
Duk da haka, ya kara da cewa, “Ina goyon bayan duk wanda ke kai hari kan Isra’ila. Aƙalla fararen hular Isra’ila su ɗanɗana irin wahalar da muke ciki a Gaza, ko da na dare ɗaya ne.”
Alaa Saleh, uba ga yara biyar, ya bayyana damuwa iri daya da Omar.
“Yaƙin da ke faruwa a Gaza har yanzu bai tsaya ba. Mutuwa da yunwa da gudun hijira sun zama ruwan dare a rayuwarmu. Amma yanzu duniya na mai da hankali kan abin da ke faruwa a Iran. Ko kafafen yada labarai sun daina bayar da rahotanni daga Gaza.”

