Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 6 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Amurka da Iran za su tattauna a Oman kan shirin nukiliya

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka da Iran za su yi tattaunawa kai-tsaye a karon farko cikin wata takwas, yayin da Washington ke neman daƙile shirin nukiliyar Tehran.

    Shugaba Trump ya yi barazanar daukar matakin soja idan ba a samu wata mafitar diflomasiyya ba. Wakilli na musamman na Amurka Steve Witkoff, da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ne ke halartar ganawar da za a yi a Oman.

    Iran ta ce ba laifi idan an nemi a tattauna kan rage tasirin shirinta na Nukila, amma duk wani batu na neman ta daina kera makamai masu linzami, da daina goyon bayan kungiyoyin yan gwagwarmaya a gabas ta tsakiya tamkar tsallaka jan layi ne a gareta.

  2. Farawa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'a daga sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.