Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 05/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Matakan rage tsananin zafi da Saudiyya ta ɗauka a bana

    Hajji

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomin Saudiyya sun yi nanata cewa sun ɗauki matakai domin rage wa mahajjata wahalhalu na zafin rana a Hajjin bana yayin da ake tsammanin zafin zai ci gaba da ƙaruwa.

    A shekarar da gabata, mutum 1,300 ne suka mutu yayin aikin akasari saboda zafin mai tsanani a birnin Makkah.

    An shuka dubban binshiyoyi da kuma kakkafa ɗaruruwan na'urorin sanyaya wuri domin rage ɗumin da aka yi hasashen zai kai 44C a ma'auni.

    Sun kuma hana yara 'yan ƙasa da shekara 12 yin aikin ibadar. Kazalika, sun jibga tara da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama yana yunƙurin shiga Makkah ba tare da cikakken izini ba.

    Zuwa ranar Lahadi, hukumomi sun ce sun hana mutane fiye da 269,000 shiga birnin na Makkah, wanda shi ne mafi tsarki a addinin Musulunci.

    Arafa

    Asalin hoton, Reuters

  2. Yadda Musulmi miliyan ɗaya da rabi ke tsayuwar Arafa

    Hajji

    Asalin hoton, Reuters

    Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa a yau Alhamis yayin babbar ibadar Musulmai a Saudiyya.

    Hukumomin Saudiyya sun ce Musulmi kusan miliyan 1.5 ne ke gudanar da aikin Hajji na shekarar 1446 bayan Hijira.

    Hajj

    Asalin hoton, Reuters

  3. Alhazan Najeriya yayin shirin fita filin Arafa

    Alhazan Najeriya, kamar sauran takwarorinsu, na can na gudanar da aikin Hajjin bana.

    Yau Alhamis ce ranar Arafa, inda dubun dubatar mahajjata suke gudanar da tsayuwar a filin Arafa.

    A waɗannan hotunan, alhazan Najeriya ne a Minna lokacin da suke shirin fita filin na Arafa.

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, Nahcon

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, Nahcon

    Alhazan Najeriya

    Asalin hoton, Nahcon

  4. Trump ya haramta wa 'yan ƙasa 12 shiga Amurka

    Trump

    Asalin hoton, EPA

    Shugaba Trump na Amurka ya fitar da sanarwar haramta wa wasu 'yan ƙasashe 12 na Afirka da Asiya shiga Amurka, ciki har da Afghanistan da Iran da Somalia.

    Sannan za a taƙaita wa 'yan ƙasa bakwai shiga Amurkar, waɗanda suka hada da Cuba da Venezuela.

    Mista Trump ya ce Amurka ba za ta ci gaba da buɗe iyakokinta wasarere ga ƙasashen da "ba sa bin ka'ida ba".

    Ya ce sun yi amfani da yanayin barazanar da kowacce ƙasa ke da ita kan Amurka wajen sanya musu takunkumai.

    Wakilin BBC ya ce wannan haramci kusan ya shafi ƙasashen da ake samun 'yan gudun hijira da ke neman mafaka a Amurka.

    Wannan mataki na haramci da Trump ya bijiro da shi ba shi da maraba da abin da aka gani a lokacin mulkinsa na farko kan ƙasashen da Musulmi suka fi yawa.

  5. Barka

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye na ranar Alhamis - ranar Arafa.

    Za mu kawo yadda al'ummar Musulmi ke gudanar da ibadar aikin Hajji ta bana a Saudiyya, da kuma sauran rahotonni daga sassan duniya.