Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na yau Alhamis 6 ga watan Fabrairun 2025

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Aisha Aliyu Ja'afar da Ahmad Bawage

  1. Masu zanga-zanga sun ruguza gidan tsohuwar firaministar Bangladesh

    yadda aka ruguza gidan Sheikh Hasina

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu zanga-zanga a Bangladesh, sun ci gaba da afka wa gine-gine masu alaƙa da iyalan tsohuwar firaiministar ƙasar Sheikh Hasina wadda aka hamɓarar da gwamnatinta a shekarar da ta gabata tare da cinna wuta.

    Daruruwan mutane yawancinsu dalibai ne suka yi amfani da ƙananan motocin ruguza gine-gine wajen farfarasa abubuwa da farwa gidan mahaifin tsohuwar firaiministar, Sheikh Mujibur Rahman, wanda shi ne shugaban ƙasar na farko, bayan samun 'yancin kan ƙasar daga Pakistan.

    Haka kuma masu zanga-zangar sun lalata gidajen biyu daga cikin ƙusoshin jam'iyyar tsohuwar firaministar, tare da cire allunan da ke ɗauke da sunanta ko na danginsu daga jami'ar ƙasar da ke birnin Rajshahi.

    Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da aka samu labarin Sheikh Hasina za ta yi wa magoya bayanta jawabi ta shafin sada zumunta daga Indiya, inda ta gudu bayan hamɓarar da ita a watan Agustan bara.

  2. Yadda rashin lantarki ke kawo cikas ga masu sana'o'i a Kaduna, Yusuf Tijjani

    wani mai sana'ar dinki

    Asalin hoton, Getty Images

    Al'ummomi da dama ne a jihohin Kaduna da Zamfara ke zaune cikin duhu sakamakon rufe hanyoyin wutar lantarki da ma’aikata na kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna wato Kaduna Electric suka yi.

    Ma’aikatan dai sun ce sun ɗauki matakin ne don nuna rashin jin daɗin su akan korar ma’aikata 900 da hukumomin kamfanin suka yi ba tare da biyansu hakkokin su ba.

    Matakin ɗauke wutar lantarkin ya haddasa wahalhalu ga dubban masu sana’o’i waɗanda ke dogaro da wutar lantarkin wajen gudanar da harkokin su.

    Auwalu Mai nama bakin Kawo Road a jihar Kaduna ya bayyana wa BBC yadda matsalar ta jefa su cikin takaici.

    nama

    Asalin hoton, Getty Images

    ''Wannan rashin wuta ta haifar mana da mummunar hasara, ga nama nan da yawa an fito da shi ya lalace, ga kifi nan shi ma an tafka hasararsa, kayan ciki da kai da ƙafa, mun yi hatsara ba ƙarama ba''.

    Shi kuwa Muftahu mai sana'ar ɗinki ya ce ya shafe tsawon kwana uku bai yi aiki ba, saboda rashin wutar lantarkin.

    ''Akwai ɗinkunan biki da za a yi amfani da su daga Juma'a da Asabar, amma yanzu haka kayan na nan ajiye ban ɗinka ko kala guda ba, na kunna inji na saka galan guda, amma ko rabi ban yi ba ya ƙare ''.

    Masu dinki

    Asalin hoton, Getty Images

    Shi ma Jamilu Idris mai sana'ar walda a birnin Kaduna ya shaida wa BBC yadda matsalar ta shafi sana'ar tasa.

    ''Ga ayyuka birjik a ƙasa, amma saboda rashin wutar dole sai dai mu haƙura, ɗan abin da muka ajiye don inganta sana'ar tamu, a yanzu shi muke ci'', kamar yadda ya bayyana.

    Ma’aikatan kamfanin na Kaduna Electric, sun ce za su maido da wutar ne kawai idan kamfanin ya yi abin da ya dace na biyan mutanen da ya sallama haƙƙokinsu, idan ma ba zai mayar da su aikin ba.

    A nasa ɓangare kamfanin na Kaduna Electric cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ma'aikata 450 ne ya sallama, ba 900 ba kamar yadda ƙungiyar ma'aikatan ke iƙirari, kuma ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon matsalar rashin kuɗi da kamfanin ke fuskanta.

    Haka kuma kamfanin ya bai wa mutane haƙuri sakamakon kwanaki da suka ɗauka ba tare da wutar lantarkin ba.

  3. Ministan tsaron Isra'ila ya goyi bayan kwashe Falasɗinawa daga Gaza

    Falasɗinawa

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan tsaron Isra'ila, mai tsattsauran ra'ayi, Israel Katz ya yaba wa shawarar Donald Trump na kwashe Falasɗinawa daga Gaza, yana mai cewa za a ƙyale su su tafi inda suke so.

    Israel Katz ya shaida wa sojojin ƙasar cewa su tsara yadda Falasɗinawa za su fice daga Gaza salun-alin.

    Ya bayyana shawarar Shugaba Trump a matsayin kyakkyawa.

    Falasɗinawa da dama sun nuna ƙwarin gwiwarsu na ci gaba da zama a Gaza, duk kuwa da ruguza gidaje masu yawa da Isra'ila ta yi a tsawon wata 15 da aka ana kai hare-hare.

    A ranar Laraba, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi gargaɗin ƙoƙarin kawar da wata al'umma daga doron ƙasa.

  4. 'Newcastle ta ci mutuncin Arsenal'

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ARsenal na ci gaba da bayyana ra'ayinsu kan rashin nasara da ƙungiyar ta yi a hannun Newcastle a wasan kusa na da ƙarshe a gasar Carabao.

    Ƙungiyar dai ta yi rashin nasara da ci 2-0 da nema a wasan da suka kara a filin wasa na St. James' Park.

    Rashin nasarar da Arsenal ta yi a gidan Newcastle na nufin ta sha kaye da ci 4-0 gida da waje da suka buga a matakin wasan kusa da na ƙarshe na gasar.

    Alhaji Yaman mai Arsenal ɗan asalin jihar Kano mazaunin Legas, ya ce wannan wasa bai yi musu ɗaɗi ba.

    ''Newcastle sun ci mutuncin Arsenal, a gidanmu sun ci mu 2-0, sannan a gidansu sun yi mana 2-0''.

    ''Wannan abin takaici ne yadda ƙungiyarmu ke kan ganiya a bana, amma a ce ko ƙwallo guda mun kasa ci a duka wasannin biyu, gida da waje''.

    Shi kuwa Safiyan Mai Arsenal cewa ya yi wasan bai ba shi mamaki ba, la'akari da cewa tuna wasan farko Newcastle ta ci su 2-0 a wasan farko da aka buga a Emirates.

    ''Dama na san zai yi wahala mu je gidansu mu yi musu 3-0,'' kamar yadda ya ce.

    Ƙungiyar - da Mikel Arteta ke jagoranta - yanzu za ta mayar da hankali kan kofin Premier da take fatan lashewa, bayan da take mataki na biyu da tazarar maki shida tsakaninta da Liverpool ta ɗaya.

    Haka kuma Gunners ɗin ta kai matakin wasan zagayen 'yan 16 a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

    Rabon da Arsenal ta ɗauki wani kofi dai tun 2020 lokacin da ta ɗauki kofin FA Cup.

  5. MSF ta zargi sojojin Isra'ila da Yahudawa da ƙoƙarin daƙile shigar wa Falasɗinawa agaji

    ...

    Asalin hoton, JAKE MORLAND

    Ƙungiyar Likitoci ta Duniya, Medicine San Frontieirs ta zargi sojojin Isra'ila da Yahudawa ƴan kama-wuri-zauna da yin kafar ungulu wajen shigar da agaji ga Falasɗinawa.

    Cikin wani rahoto da MSF ta fitar bayan tattaunawa da marasa lafiya da ma'aikatanta sun tabbatar da yadda rayuwar marasa lafiyar ke cikin haɗari.

    MSF ta ce an kai wa asibitoci da cibiyoyin lafiya ɗaruruwan hare-hare a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, tun daga watan Oktoba kawo yanzu.

    Sai dai Isra'ila ta kafe cewa tana bin dokokin ƙasa da ƙasa a yaƙin da ta ke yi a Gaza.

  6. Gwamnatin Ghana ta rage kuɗin aikin hajji

    Hajjin Bana

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Ghana ta sanar da rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2025 daga cedi 75,000 zuwa cedi 62,000, wanda yayi daidai da dala $4,130.

    Wannan na daga cikin matakin cika alƙawarin da shugaban ƙasar, John Dramani Mahama ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe, inda ya sha alwashin rage kuɗin aikin hajji domin ƙara samar sauƙi ga musulmin Ghana wurin gudaanar da aikin hajji.

    A makonnin da suka gabata ne dai shugaban ƙasar ya aika wata tawaga zuwa ƙasar Saudiyya, domin sabunta tattaunawa da mahukuntan ƙasar kan tsare-tsaren aikin hajjin bana ciki har da batun kuɗaɗe.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ƙasashen ciki har da Najeriya suka yi ƙari a kan kuɗin aikin hajjin.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Aisha Aliyu Ja'afar tare da Abdullahi Bello Diginza ne ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kar dai ku manta kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.