Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 18 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. 'Hanyoyi huɗu na kawo ƙarshen yaƙin Iran'

    ....

    Asalin hoton, EPA

    Yayin da yaƙin Iran ya doshi mako uku, wasu na ci gaba da kiraye-kierayen tsagaiatw wuta a yaƙin.

    Tuni dai yaƙin ya shafi duniya musamman ta fannin makamashin man fetur da iskar gas.

    Musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi.

    Haka ma a ƙasashe maƙwabta hare-haren da Iran ke kai musu sun janyo asarar dukiyoyi a ƙasashen, musamman yadda take kai wa cibiyoyin makamashi da sansanonin sojin Amurka hare-hare a ƙasashen.

    Yaƙin dai kamar yadda aka yi hasashe ya shafi kusan duka yankin Gabas ta Tsakiya.

    Wannan ne dalilin da ya sa ake ta kiraye-kirayen kawo ƙarshen yankin.

    Jaridar New York Times ta lissafo wasu hanyoyi huɗu da take ganin su ne za su kawo ƙarshen yaƙin da suka haɗa da:

  2. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan kasance wa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za kumu ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.