Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 16/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 16/01/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Abdullahi Diginza

  1. Abin da ya sa aka binne Sardauna a Kaduna maimakon Sokoto

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan cika shekara 60 da juyin mulkin soji na farko a Najeriya, wanda ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin jamhuriya ta farko, wasu na ci gaba da tattaunawa kan tabon da matsalar ta haifar.

    Juyin mulkin ne ya yi sanadiyar mutuwar fitattun ƴansiyasa irin su Firaministan Najeriya na wancan lokaci Abubakar Tafawa Ɓalewa da Firimiyan Arewa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da takwaransa na Yamma Ladoke Akintola da sauransu.

    A yunƙurin juyin mulkin, wanda aka yi a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, wasu hafoshin sojin Najeriya ne suka yi yunƙurin juyin mulki, wanda shi ne na farko da aka fara samu bayan samun ƴancin kai.

    Baya ga manyan 'yan siyasa, juyin mulkin ya kuma rutsa da manyan jami'an sojin Najeriya.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da Hausawa ke yi wa kirari da Hajji babbar rana.

    Abdullahi Diginza da Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafa a shafukanmu na sada zumunta.