Jama'a masu
bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke
wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu
rufe shafin na yau Asabar, 31/08/2024.
A madadin
kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za ku kasance da mu gobe Lahadi 01 ga watan Satumba, 2024.
Mu rufe da
wannan karin maganar da ke cewa - Komai gaggawar ungozoma ta bari a haihu.
Duk gwamnan da ya shiga rikicin jihata zan tayar da wuta a jiharsa - Wike
Asalin hoton, RVGH
Ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike, ya lashi takobin haddasa gagarumin rikici a jihar da duk wani gwamnanta ya yi ƙoƙarin shiga rikicin jiharsa ta Rivers.
Wike ya sha alwashin cewa ba zai taɓa bari wani ya karɓe shugabancin jam'iyar PDP ba a jihar ta kudu maso kudancin Najeriya, yana mai cewa zai haddasa rikici a jihar da duk wani gwamna na PDP ya yi yunƙurin shiga rikicin.
A ranar 23 ga watan nan na Agusta ne gwamnonin PDP da suka yi taro a Taraba, suka nemi shiga rikicin da jam'iyyar ke fama da shi a jihar, ta Rivers inda suka nuna goyon bayansu ga gwamnan jihar
Siminalayi Fubara.
A sanarwar bayan taro da gwamnonin suka fitar wadda shugaban kungiyar tasu Gwamnan jihar Bauchi , Bala Mohammed, ya karanta sun nemi a sake sakamakon taron jamiyyar na jiha domin mayar da ikonta ga gwamnan jihar.
Wasu matasa a India sun ci mutuncin tsoho saboda naman shanu a jirgin ƙasa
Asalin hoton, Getty Images
Jami'an sufurin jirgin ƙasa a India na gudanar da bincike kan wani hoton bidiyo da ya ɗauki hankalin jama'a a shafukan intanet, wanda ke nuna wasu matasa na dukan wani tsoho a cikin jirgi bisa zargin yana ɗauke da naman shanu.
A hoton an ga wasu matasan fasinjoji suna ta zagi da marin mutumin mai suna, Haji Ashraf Munyar, daga Maharashtra, jiha ta biyu mafi yawan al'umma a ƙasar ta India.
Shanu suna da matsayi mai tsarki a addinin Hindu, abin da kan sa ma su tsattsauran ra'ayi na addinin ke yawan kai hare-hare kan mutanen da suke zargi da yanka dabbar domin nama.
Ƴansanda sun ce sun gano wasu daga cikin matasan da suka ci mutuncin dattijon, kuma suna ci gaba da bincike.
Jami'an lafiyar Falasdinu sun fara allurar riga-kafin Polio a Gaza
Asalin hoton, AFP
Jami'an lafiyar Falasɗinu sun fara yin allurar riga-kafin cutar Polio ga yara a Gaza, gabanin gagarumin shirin riga-kafin da za a fara gobe Lahadi.
Ma'aikatan lafiya sun fara yin alluran ne a asibitin Nasser da ke Khan younis.
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce a fara gangamin allurar riga-kafin a hukumance da misalin ƙarfe 7;30 na safiyar Lahadi a Deir al-Balah.
Hukumar UNICEF ta ce za a kwashe tsawon sa'o'i shida da rabi a kullum har zuwa huɗu ga watan Satumba.
Isra'ila da Hamas sun amince za su tsagaita wuta domin bayar da damar yin riga-kafin ga yara Falasdinawa sama da dubu ɗari shida.
Sojojin Isra'ila na kai hari mai muni a sansanin ƴan gudun hijira a Gaɓar Yamma
Asalin hoton, Getty Images
Iyalan Falasdinawa sun fara ficewa daga sansanin ƴan gudun hijira da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan bayan da Isra'ila ta rufe sansanin yayin wani gagarumin samame da take yi na tsawon kwana huɗu.
Ana ci gaba da jiyo ƙarar fashewa da kuma harbi ta ko ina daga cikin sansanin da ke tsakiyar birnin Jenin, yayin da jirage marasa matuƙa da jiragen yaƙi na Isra'ila suka yi wa wajen ƙawanya ta sama.
Wakilin BBC ya ce wasu daga cikin iyalan da suka samu damar fitowa daga sansanin a karon farko tun ranar Laraba, sun ce sun ɓoye ne a cikin gidajensu, Inda babu wuta babu ruwa.
Harin ya kasance ɗaya daga cikin mafiya girma da sojojin Isra'ila ke kaiwa a Gabar Yamma tsawon shekaru.
Buhari ba ya bin Tinubu bashin komai - Sule Lamiɗo
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ''Tinubu, mutum ne da iya allonsa, kuma ya yi wa kansa aiki ya samu shugabanci''
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin jajircaccen mutum, wanda ya iya allonsa da kyau, da ba wanda ya zai fito fili ya bugi ƙirji ya ce shi ya taimaka masa ya samu mulkin Najeriya hatta wanda ya gada Muhammadu Buhari.
Lamiɗo wanda yana daga cikin ƙusoshin jam'iyyar hamayya ta PDP, ya ce Tinubu mutum ne da ya iya ruwa, kuma ya yi nazarin yadda abubuwa kw tafiya a lokacin ya kuma yi amfani da dabarunsa da kyau, ya cimma burinsa.
''Saboda haka ba wani mutum da zai fito fili ya ce shi ne silar cin zaɓen Tinubu, hatta Buhari,'' in ji shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jigon na PDP ya bayyana hakan ne a wata hari da jaridar Nigerian Tribune.
Ya ce: Kafin babban taron jam'iyyar (APC) shi (Tinubu) yana Abeokuta, a jihar Ogun, inda ya bugi ƙirjin cewa lokacinsa ne ya mulki Najeriya. Kuma Buhari, yana nan sangan-sangan yana kallo. Bai so Tinubu. Akwai wanda yake so.''
“Hatta mataimakinsa ma Farfesa Osinbajo bai yarda da shi ba; ya so Ahmed Lawan, ne amma lissafinsa bai yi ba. Ka yi shekara takwas ga Arewa kuma kana son wani ɗan Arewa ya sake wata shekara takwas?! A'a No. Wataƙila dai sai nan gaba, domin akwai abubuwan da ba za ka iya jirkitawa ba, ba dai a Najeriya ba a yau,'' in ji Lamiɗo.
Ya ƙara da cewa: “Kana shugaban Najeriya, bayan shekar takwas a ofis , ba shi da ƙwarin gwiwa da ƙarfin halin da zai dasa zaɓinsa.''
''Yana wajen babban taron, kuma Tinubun da ba ya so, da bai taɓa tsammanin zai yi nasara ba, ya yi nasara. Sabboda haka Tinubu ya san cewa nasararsa ba daga Buhari take ba, saboda haka ba wani abu da Buhari zai ce ya yi masa.
Haka kuma tsohon gwamna na Jigawa ya ce Tinubu ba shi ne zaɓin ƙungiyar kishin Yarabawa ta Afenifere, ba kuma hatta Obasanjo ma ba ya sonshi, to amma ya zama shugaban ƙasa.
''Duk wasu ƙungiyoyi suna nan, ciki har da gwamnoni, amma ya yi nasara. Ya ƙudiri aniyar murƙushe duk wani abu da ya sha masa gaba, kuma ya murƙushe su.
Ya ce, PDP na aiki tuƙuru don ganin ta yi nasara a zaɓukan 2027 , duk da matsalolin da take fama da su.
Nan ba da jimawa ba za mu kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya - Sojoji
Asalin hoton, Nigerian Army/X
Bayanan hoto, Laftanar Janar, Taoreed Lagbaja
Babba hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar, Taoreed Lagbaja ya tabbatar wa 'yan ƙasar cewa nan ba da jimawa ba sojoji za su kawo karshen matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Janar Lagbaja ya bayaya hakan ne cikin jawabin da ya yi a lokacin bikin rufe babban taron rundunar sojin ƙasa ta Najeriya na shekarar 2024 da aka gudanar a jihar Akwa ibom da ke kudancin ƙasar.
Taron na kwanaki biyar - wanda manyan hafsosjin rundunar sojin ƙasa ta Najeriya suka halarta ya duba irin nasarori da rundunar ke samu, da kuma irin tsare-tsare da rundunar ke yi wajen gudanar da ayyukanta a faɗin ƙasar..
''Ina son tabbatar muku cewa rundunar sojin ƙasa ta Najeriya na kan hanyar kawo ƙarshen matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta'', in ji Janar Lagbaja.
Ya ƙara da cewa ya samu wannan tabbaci ne sakamakon irin bayanan da yake samu daga sassa daban-daban na rundunar a faɗin ƙasar.
Tun da farko babban hafsan sojin ƙasan ya yi watsi da kiraye-kirayen da ya ce wasu da ya kira ''masu son rai na yi wa sojoji na kawo ƙarshen mulkin dimokraɗiyya''.
Ya ce a yanzu abin da ke gaban rundunar sojin Najeriya shi ne maido ta martaba ta ƙimarta, bayan shafe shekaru masu yawa suna jagorantar ƙasar, don haka ya ce sojojin ƙasar ba za su yi abin da zai zubar musu da ƙimar da suka yi shekara 25 suna ginawa kansu ta hanyar barin wanzuwar mulkin dimokraɗiyya a ƙasar.
Ambaliya ruwa ta haifar da asarar rayuka a Maraɗin Jamhuriyar Njar
Asalin hoton, Amira Souley
Bayanan hoto, Gidaje da dama ne suka rushe sakamakon ambaliyar
Mamakon ruwa sama da ake samu a 'yan kwanakin nan a wasu sassan ƙasar Jamhuriyar Nijar ya haddasa mummunar ambaliyar ruwa a yankin Maraɗi na ƙasar.
Ambaliyar ta haifar da asarar rayukan mutanen da ba a iya tabbatar da adadinsu ba.
Haka kuma ɗaruruwan gidaje ne suka rushe, yayin da titunan da dama suka lalace, sakamakon ambaliyar.
Ambaliyar ta yi munin da aka jima ba aga irinta ba
A shekarun baya-bayan nan an jima ba a ga ɓarnar ambaliya ruwa irin wannan a garin Maraɗi ba.
'Hare-haren Rasha sun kashe mutum biyar a Ukraine'
Hukumomin Ukraine sun ce mutum biyar ne suka mutu sakamakon hare-haren da Rasha ta kai garin Chasiv Yar da ke kusa da yankin Donest da ake fafatawa.
Gwamnan yankin, Vadym Filashkin ya ce hare-haren Rasha sun faɗa kan wani gidan a mutanen ke ciki.
Ya ƙara da cewa mutanen da suka mutu duka maza ne, inda ya yi kira ga sauran fararen hula su fice daga garin.
A wani labarin na daban kuwa, ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta sun ƙwace iko da garin Verezamske a yankin na Donetsk.
Sojojin Rasha na ƙara dannawa tare da ƙwace garuruwan yankin Donetsk, yayin da dakarun Ukraine a ɗaya gefen ke ƙara nausawa tare da ƙwace iko da garuruwan yankin Kursk na Rasha.
Jirgin Rasha ɗauke da mutum 22 ya ɓata a gabashin ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Wani jirgi mai saukar ungulu ɗauke da mutum 22 ya ɓata a tsibirin Kamchatka da ke gabashin Rasha.
Jirgin - wanda ke ɗauke da 'yan yawon buɗe idanu - ya ɓace daga kan layinsa jim kaɗan bayan tashinsa daga yankin Vachkazhets mai ɗimbin tarihin dazukan namun daji.
Jami'an ƙasar sun ce rashin kyawun yanayi, ciki har da mummunan hazo na kawo tarnaƙi kan ƙoƙarin neman jirgin.
Al'amarin ɓacewar jirage ko faɗuwarsu na neman zama ruwan dare a yankin gabashin Rasha, mai cike da wuraren yawon buɗe idanu da kuma rashin kyawun yanayi.
Ko a shekaru uku da suka gabata ma sai da wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗi tare da kashe mutum takwas ciki har da 'yan yawon buɗe idanu a yankin na tsibirin Kamchatka skamakon rashin kyawun yanayi.
Ƙungiyoyin da suka hauro gasar Premier sun kashe kusan fam miliyan 300
Ƙungiyoyi ukun da suka hauro gasar Premier Ingila sun kashe maƙudan kuɗi a ƙoƙarinsu na ƙarfafa tawagoginsu don tunkarar gasar mai cike da tarin ƙalubale.
Ipswich ta kashe fam miliyan 109 kan 'yan wasa 10, bakwai daga cikinsu daga ƙungiyoyin da ke buga gasar, ciki har da ɗan wasan Chelsea Omari Hutchinson.
Ita kuwa Southampton cikin 'yan wasan da ta ɗauka har da mai tsaron ragar Arsenal Aron Ramsdale, da ta ɗauka a ranar ƙarshe ta cinikin 'yan wasan.
RSF ta bai wa dakarunta umarnin bari a shigar da kayan agaji yankunansu
Shugaban dakarun RSF a Sudan, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, ya bayar da umarni ga dakarunsa su bayar da dama don shigar da kayan agaji zuwa yankunan da ke ƙarƙashin ikonsu.
Hakan na zuwa ne bayan wata tattaunawa da Amurka ta jagoranta a baya-bayan nan a birnin Geneva.
A farkon wannan wata ne ɓangarori biyun da yaƙi da juna a ƙasar - RSF da sojojin gwamnati - suka bayar da umarnin buɗe wasu manyan muhimman tituna biyu don kai kayan agaji yankunan da yaƙin ya fi ƙamari a yankin Darfur.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga ƙasashen duniya su ƙara yawan tallafin da suke bai wa ƙasar, don taimaka wa mutum miliyan shida da ke cikin tsananin buƙatra tallafi a faɗin ƙasar.
Ambaliya ruwa: Fiye da mutum 18,000 ne suka rasa muhallansu a Sudan ta Kudu
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin duniya ta ce fiye da mutum 18,000 ne suka rasa muhallansu sakamakon mummunar ambaliya ruwa a Sudan ta Kudu.
Jami'an ƙasar sun ce mamakon ruwan sama da ake samu a ƙasar ya haifar da mummunar ambaliyar da ta lalata gidaje tare da cinye gonaki a jihar Lafon da ke gabashin ƙasar.
Mutanen da lamarin ya shafa a yanzu na neman mafaka a makarantu da wuraren ibada da hukumomin gwamnatin jihar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ambaliyar ta shafin gundumomi 78 a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa ayyukan jin ƙai suka munana a yankunan da ke fama da rikice-rikice da ƙarancin abinci, da kuma matsalar yaƙin Sudan mai makabtaka
Arsenal ta ɗauki Sterling aro daga Chelsea
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sterling ya buga wa ingila wasa 82, tare da zura kwallo 20
Ɗan wasan gaban Chelsea Raheem Sterling ya kammala komawa Arsenal a matsayin aro a rana ta ƙarshe ta rufe musayar kasuwar 'yan wasa.
Tun da farko Sabon kocin Chelsea, Enzo Maresca ya shaida wa ɗan wasan Ingilan cewa ba ya cikin 'yan wasan da zai yi amfani da su.
"Abu ne da bai min daɗi ba, amma zuwana Arsenal ya faranta mini rai," in ji Sterling a lokacin da ya saka hannu kan jarjejeniyar komawar sabuwar ƙungiyar.
Ya ƙara da cewa 'ƙungiya ce da na jima ina fatan taka wa leda, ita ce ƙungiyar da ta dace da ni a yanzu, na yi farin ciki ƙwarai da gaske''.
Sterling ya taka leda manyan ƙungiyoyin gasar Premier da suka haɗa da Liverpool da Manchester City da Chelsea sai kuma Arsenal yanzu da ya koma.
Asalin hoton, Getty Images
Don maye gurbin ɗan wasan, Chelsea ta ɗauki aron Jodan Sancho daga Manchester United.
Daga cikin yarjejeniyar, Chelsea za ta sayi ɗan wasan na Ingila mai shekara 24 kan kuɗi tsakanin fam miliyan 20 zuwa 25 a kakar wasa mai zuwa.
Sancho ya je United kan kuɗin fam miliyan 73 daga Borussia Dortmund a watan Yulin, sai dai bai taka rawar gani ba a ƙungiyar.
Ya buga wa ƙungiyar wasa 83 cikin kaka uku da ya yi tare da ita, sai dai ya riƙa samun saɓani da kocin ƙungiyar, Erik ten Hag lamarin da ya sa dangantaka ta yi tsami tsakani.
Rasha ta kashe mutum bakwai a harin da ta kai Ukraine
Asalin hoton, ....
Jami'ai a Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine sun ce aƙalla mutum bakwai aka kashe yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren Rasha, ciki har da wani harin bam.
Wata yarinya mai 14 da ke filin wasan yara na cikin waɗanda suka mutu.
An kuma kashe mutane da dama da harin ya rutsa da su a cikin wani bene.
Shugaba Zelensky ya ce - ƙasarsa za ta iya daƙile harin idan da masu ba ta tallafi sun amince ta yi amfani da makamansu domin kai hari har cikin Rasha.
Birnin Kharkiv da ke arewa maso-gabashin Ukraine yana kusa da kan iyaka wanda Rasha ke kai wa hare-hare.
Lafiya Zinariya: Bayanai kan cutar Ƙyandar biri
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Fiye da mutum 24,000 ne suka ɓata a Najeriya cikin shekara 10 - Red Cross
Ƙungiyar Agaji ta Red Cross a Africa ta ce sama da mutum 24,000 ta yi rijistar sun ɓata a Najeriya.
Red Cross ta ce cikin shekara 10 na tattara wadannan alƙalumma, jami’anta a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun yin ƙoƙari wajen sanar da iyalan waɗanda suka rasa ‘yan'uwansu sakamakon ayyukan ‘yan bindiga.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne albarkacin ranar ɓatan mutane ta duniya da ake gudanarwa a ƙarshen watan Agustan kowacce shekara.
Kuma kan hakan Buhari Muhammad Fagge ya haɗa mana rahoto. sai dai rahoton zai iya sosa ranku
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton
Jamus ta kammala janye dakarunta daga Nijar
Asalin hoton, Getty Images
Jamus ta kammala janye ragowar dakarunta da suka rage a Jamhuriyar Nijar, a wani mataki na kawo ƙarshen ayyukan sojinta a yankin Sahel.
Da maraicen ranar Juma'a ne dai wasu manyan jiragen dakon kaya biyar suka sauka a ƙasar Jamus ɗauke da sojoji 60 da ton 146 na kayan aikinsu daga Jamhuriyar ta Nijar.
A cikin watan Mayu ne hukumomin na Nijar suka amince da ci gaba ayyukan sojojin Jamus a ƙasar har zuwa ƙarshen watan Agusta.
Yarjejeniyar ci gaba da aiki da juna ta citura tsakanini ɓangarorin biyu, bayan da Nijar ta kasa bayar da tabbacin kariya daga tuhuma ga dakarun na Jamus.
Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da jam'ian ƙasashen biyu suka fitar, sun ce ''janye dakarun ba shi ne ƙarshen haɗin gwiwa soji tsakanin ƙasashen ba''.
To sai dai sanarwa ta saɓa da kalaman da ministan harkokin wajen Jamus ya yi cikin watan Yuli cewa Jamus ba za sake haɗa kai da Nijar saboda abin da ya kira ''rashin amana''.
A shekarar 2016 ne Jamus ta fara aikin soji a Nijar, inda take da dakaru 3,200 a ƙasar da ke yankin Sahel.
Amurka za ta sake aika 'yan sama jannati bayan maƙalewar biyu a sama tun cikin watan Yuni
Asalin hoton, Space Perspective
Amaurka za ta sake aika wata tawagar 'yan sama jannati zuwa tashar ta sararin samaniya ta duniya.
To sai dai hukumar binciken sararin samaniyar ƙasar, NASA ta rage yawan 'yan sama jannatin - da ke shirin wannan tafiya sararin samaniyar- domin bayar da dama ga wasu mutum biyu - da suka maƙale a tashar sararin samaniya tun cikin watan Yuni - su dawo.
A watan Satumba ake sa ran sake tura 'yan sama jannatin - waɗanda ake sa ran saukowarsu cikin duniyarmu a cikin watan Fabrairu shekra mai zuwa tare da waɗanda suka maƙalen.
A cikin watan Yunin da ya gabata ne Suni Williams da Butch Wilmore Suka tafi ne da niyyar yin kwana takwas kawai, amma suka maƙale har yanzu .
Brazil ta toshe dandalin X a ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Brazil ta dakatar da amfani da dandalin X na Elon Musk , bayan kamfanin ya gaza gabatar da sabon lauyansa a ƙasar.
Dandalin na da masu amfani da shi fiye da miliyan 22 a ƙasar da ke yankin Latin.
Alkalin Kotun Ƙolin ƙasar ne ya bai wa hukumomin sadarwa umarnin su toshe kafar sadarwar intanet ta dandalin na X, har sai kamfanin ya bi umarnin kotu tare da biyan tarar dala miliyan uku.
Matakin na zuwa ne bayan taƙaddama ta tsawon lokaci bayan da alkalin kotun ya umarni kamfanin X ya dakatar da wasu shafukan da ƙasar ke zargi suna yaɗa labaran ƙarya.
Mista Musk ya kira matakin a matsayin siyasa, tare da bayyana alƙalin a matsayin mai kama karya da ke hana faɗin albarkacin baki