Manyan ƴan wasan Japan da ke jinya, Netherlands v Japan
Kyaftin din Japan, Wataru Endo, wanda ya hakura da buga gasar cin kofin duniya a wannan makon, yana ɗaya daga cikin manyan da ba za su buga wasan ba.
Ɗan wasan, Brighton Kaoru Mitoma ya ji rauni, haka shima Takumi Minamino na jinya.
, Netherlands v Japan
Magoya bayan Netherlands sun je filin wasan makil suna tafiya ta gargajiya kamar yadda suka saba a kowacce gasa.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
, Netherlands v Japan
Magoya bayan Japan je birnin Dallas kwai da kwarkwata.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Ko Japan za ta ci gaba da yin abin ban mamaki a gasar cin kofin duniya?, Netherlands v Japan
Kowacce gasa da Japan ke halarta ta yi yin abin ban mamaki, wanda ke wuce tsammani ko hasashen masana tamaula.
A wannan gasar kasashe kalilan ne ke wasa irin na Japan, wanda take sa sauri da kai hare-hare ta kowacce kusurwa ga kuma ɗan karen gudu.
A gasar da aka buga a 2022 a Qatar ta doke Jamus da Sifaniya ta kuma ja ragamar rukuni na biyar a lokacin.
To sai dai an yi waje da ita a zagayen ƴan 16 a hannun Croatia a bugun fenariti.
Yanzu dai shekara huɗu tsakani, kenan tana da damar yin wasu abubuwan bajinta a wasannin bana.
Sauran tawagogin da suke rukuni na shida sun haɗa da Sweden da kuma Tunisia.
, Netherlands v Japan (21:00 BST)
Netherlands za ta fara wasan gasar cin kofin duniya ba tare da wani ɗan wasa da ke buga babbar gasar tamaula ta Netherlands, wato Dutch Eredivisie a karon farko a tarihi, yayin da abokiyar hamayya, Japan take da ƴan wasa biyu da ke taka leda a gasar ta Dutch da ya haɗa da Tsuyoshi Watanabe da kuma Ayase Ueda.
Labaran da ya shafi ƴan wasan tawagogin biyu, Netherlands v Japan
Daizen Maeda na Japan mai taka leda a Celtic zai ja ragamar ƴan wasa a kokarin da tawagar ke yi na ci gaba da taka rawar gani a wasannin.
Haka kuma za ta fara wasan da mai tsaron bayan, Bayern Munich Hiroki da kuma Ritsu Doan mai taka leda a Eintracht Frankfurt.
Kyaftin din Netherlands, Virgil van Dijk na Liverpool, zai jagoranci tawagar da Ronald Koeman ke horarwa. Haka kuma Van Dijk zai taka leda tare da takwarorinsa da suke wasa a Liverpool da ya haɗa da Cody Gakpo da kuma Ryan Gravenberch.
Mai tsaron bayan Tottenham, Micky van de Ven yana ciki tare da ƴan wasa biyun da ke wasa a Brighton, wato mai tsaron raga, Bart Verbruggen da kuma Jan Paul van Hecke. Ɗan wasan Manchester City, Tiijani Reijnders, yana ciki, tare da na West Ham United Crysencio Summerville.
Ƴan wasan Netherlands 11: Verbruggen, Van de Ven, Van Dijk, Van Hecke, Dumfries, Reijnders, De Jong, Gravenberch, Gakpo, Malen, Summerville.
Asalin hoton, BBC Sport
Asalin hoton, BBC Sport
, Netherlands v Japan
Wannan shi ne ake kira filin wasa na AT &T!
A nan filin Ingila za ta buga wasan farko a rukuni da za ta kara da Crotia ranar Laraba.
Wasan farko da Dallas zai karɓi bakuncin gasar kofin duniya a bana, Netherlands v Japan
Wannan shi ne wasan farko da katafaren filin da yake birnin Dallas zai karɓi bakuncin gasar cin kofin duniya a bana daga tara da aka tsara za a buga a ciki.
Yana Arlington mai kilomita 17 tsakani daga garin Dallas, kuma saman filin ana rufe shi da kuma buɗe shi duk lokacin da ake bukata.
An buɗe shi a 2009, inda ƙungiyar ƙwallon zari rugar Amurka NFL, Dallas Cowboys ke buga wasanninta.
Tun farko an tsara ƴan kallo 90,000 za su cika filin daga baya aka rage zuwa 70,649.
Asalin hoton, Getty Images
Za a karasa wasa a rana ta huɗu da fara gasar kofin duniya 2026
Wannan shi ne wasa na huɗu a ranar Lahadi, kuma rana ta huɗu da aka fara wasannin cin kofin duniya a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Asalin hoton, BBC Sport
, Netherlands v Japan
Tawagar Japan da ke neman tsawaita wasa takwas da tare da an doke ta ba.
Ita kuwa tawagar Netherlands za ta buga gasar cin kofin duniya karo na 12 da fatan lashe kofin bana.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
An sanar da ƴan wasan da za su buga wa tawagogin tamaula, kuma sun fara motsa jiki.
Barkanmu da shiga fagen gasar cin kofin duniya 2026
Jama'a barkanmu da kasancewa a wannan lokacin da za mu kawo muku kai tsaye wasan gasar kofin duniya tsakanin Netherlands da Japan a karawar cikin rukuni na shida.
Sunana Mohammed Abdu zan gabatar muku da shirin tare da taimakon AI, za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.