Daizen Maeda na Japan mai taka leda a Celtic zai ja ragamar ƴan wasa a kokarin da tawagar ke yi na ci gaba da taka rawar gani a wasannin.
Haka kuma za ta fara wasan da mai tsaron bayan, Bayern Munich Hiroki da kuma Ritsu Doan mai taka leda a Eintracht Frankfurt.
Ƴan wasan Japan 11: Suzuki, Ito, Taniguchi, Watanabe, Nakamura, Kamada, Sano, Doan, Maeda, Kubo, Ueda.
Kyaftin din Netherlands, Virgil van Dijk na Liverpool, zai jagoranci tawagar da Ronald Koeman ke horarwa. Haka kuma Van Dijk zai taka leda tare da takwarorinsa da suke wasa a Liverpool da ya haɗa da Cody Gakpo da kuma Ryan Gravenberch.
Mai tsaron bayan Tottenham, Micky van de Ven yana ciki tare da ƴan wasa biyun da ke wasa a Brighton, wato mai tsaron raga, Bart Verbruggen da kuma Jan Paul van Hecke. Ɗan wasan Manchester City, Tiijani Reijnders, yana ciki, tare da na West Ham United Crysencio Summerville.
Ƴan wasan Netherlands 11: Verbruggen, Van de Ven, Van Dijk, Van Hecke, Dumfries, Reijnders, De Jong, Gravenberch, Gakpo, Malen, Summerville.