, Netherlands 0-0 Japan
An je hutun minti 15 kafin su sake komawa cikin fili, domin a karasa wasan.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed Abdu tare da taimakon AI
An je hutun minti 15 kafin su sake komawa cikin fili, domin a karasa wasan.
Netherlands ta samu bugun kusurwa ta kuma buga, amma daga baya mai tsaron ragar Japan Suzuki ya kama ƙwallon.
An yi karin minti uku daga nan sai suje su huta.
Wannan ce dama mai kyau da Japan ta samu.
Keito Nakamura ya samu ƙwallo daf da da'ira ya kuma buga amma ta yi faɗi ta fita daga fili. Shi kuma ya kama kai yana tunanin damar da ya samu.
The Netherlands na ci gaba da ɓarar da dama, inda Cody Gakpo ya buga ƙwallo da karfi, amma ta yi sama da yawa.
Netherlands na samu damarmaki, inda Donyell Malen ya sa kai, mai tsaron ragar Japan ya tare amma sai ƙwallon ta koma wajen van Micky van de Ven, amma ba wani haɗari.
Netherlands ta kasa ratsa bayan Japan.
Donyell Malen ya ratsa cikin ƴan Japan, bayan wani kuskure da aka yi, Sai dai Takefusa Kubo ya yi wani abun..
Kwallon ta je wajen Keito Nakamura a cikin da'ira ta bugun fenariti, sai dai kamar ya rasa mai zai yi, amma ya sa kafa ya taɓa, amma babu wata barazana.
Sai dai Hiroki Ito ya gwada sa'a, sai dai ƙwallon da ya buga ta yi sama sosai.
An ci gaba da wasa, amma dai karawar nan ba haka aka sa ran za a buga wasan ba, an sa ran za a ga kazar-kazar daga Japan, amma sai aka ga tana bin wasan a hankali, domin ta sa Netherlands ba karamar kasa bace.
An je hutun shan ruwa domin ƴan wasa su huta, saboda yanayin zafin kasar.
Netherlands ta samu ta shiga gidan Japan ta kuma yi ɗan kazar-kazar da ƙwallo, amma ba ta samu wata dama ba, an kuma fitar da ƙwallon.
Ana raba ƙwallo mai ƙyau, inda Japan ke fatan shiga gidan Netherlands
Shogo Taniguchi ya yi gudu a gefen hagu da ƙwallo, ya kuma buga amma ta yi faɗi.
Ritsu Doan ya bar kwallon yayi tunanin akwai nasa a bayansa wanda zai iya karɓar ƙwallon, amma sai ta je wajen Netherlands.
Japan da sauri ta dawo ta tare gida.
Ana gara leda mai ban sha'awa.
Babu wani kazarkazar sosai, amma dukkansu sun ƙwan da sanin mahimmacin samun maki uku a wannan karawar. Wasan ya fara ɗan nutsawa.
An yi wa Keito Nakamura laifi daga Micky van de Ven kenan Japan ta samu bugun tazara.
Mai tsaron bayan Liverpool, Virgil van Dijk bai samu hutu da yawa ba.
Wannan shi ne wasa na 66 da yake buga wa a 2025-26 daga ciki 55 a Liverpool da kuma 11 a Netherlands, kuma kowanne da shi ake fara wasa.
An yi hasashen cewa nan gaba za a yi guguwa a birnin Dallas amma hakan ba zai shafi wasan ba, domin ana rufe saman filin babu wata matsala.
An fara wasan kuma Neterlands ce ta fara take leda da mayar da ƙwallo gida.
Za a buga minti 45, za kuma a bayar da hutun shan ruwa domin an wasa su huta, saboda yanayin zafi. Daga nan aje hurtun rabin lokaci.
Ko za a ci ƙwallo a cikin waɗan nan mintunan ko kuma yaya?
An kammala rera taken kasashen biyu, yanzu ake sa ran fara wasan, ƴan ƙwallo na cikin fili.
Tawagar Jamus ta fara gasar bana da kwarin gwiwa, sakamakon doke Curucao 7-1.
Scotland da Australia dun sun fara da samun maki uku-uku.