Ƴansandan Ghana sun kama wanda ake zargi da kashe jami'ar kiyaye haɗuran Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ƴansanda a Ghana sun ce sun samu nasarar kama wani ɗan Najeriya mai suna Victor Benjamin Fajemirokun wanda ake zargi da kashe wata jami'ar hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya da ƴarta a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Kwamandan sashen Gabas maso Kudanci a rundunar ƴansandan ƙasar Ghana, George Ohene-Boadi ne ya bayyana haka a taron ganawa manema labarai, inda ya ce wanda ake zargin mai shekara 36 ya tsere zuwa Ghana ne bayan ya yi aika-aikar.
Ya ce sun ga wani bidiyo ne wanda a ciki ake zargin matashin da sacewa tare da kashe jami'ar mai suna Lasisi Funmilayo da ƴarta Sewa a garin Abeokuta da ke jihar Ogun, sannan ya tsere.
"Ƴansandan Najeriya ne suka fara nemansa ruwa a jallo, maimakon ya miƙa kansa sai ya tsere zuwa Ghana," in ji Ohene-Boadi.
Ɗansandan ya ce yanzu haka wanda ake zargin yana hannunsu, "sannan idan muka kammala bincikenmu a nan za mu miƙa shi ga hukumomin Najeriya."


