Asuba ta gari
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarin wasanni kai-tsaye.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 24/06/2024.
Haruna Ibrahim Kakangi, A'isha Babangida, Umaymah Sani, Ahmed Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarin wasanni kai-tsaye.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi gargaɗin cewa manufofin yaƙin neman zaɓen jam’iyyu masu tsatsaurar ra’ayin rikau da na masu ra’ayin kawo sauyi na iya haifar da abin da ya kira yaƙin basasa.
Yayin da yake magana gabanin zagayen farko na zaben 'yan majalisar dokokin Faransa da za a fara a karshen wannan makon, ya ce ɓangarorin biyu na janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma.
Wannan shi ne karon farko da ake amfani da irin waɗannan kalaman a yakin neman zaɓe na bana wanda hakan ke nuni da irin badakalar da ke tattare da zaɓen da ke gabatowa.

Asalin hoton, FCT Police
Rundunar ‘yansandan Abuja ta ce ta kama wasu mutane huɗu da take zargi da hannu a kisan wani babban hafsan soji wanda ya yi ritaya a gidansa da ke birnin.
Rundunar ta ce tana kuma neman wasu karin mutane biyu da take zargi a lamarin.
Hakan na zuwa ne yayin da babban birnin na Najeriya ke ci gaba da fuskantar rashin tsaro da ya hada da sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa.
Kwamishinan ‘yan sandan birnin na Abuja, Beneth Igweh, ya kuma ce sun samu nasarar kam wasu manyan masu garkuwa da mutane da ake nema ruwa jallo da masu taimaka musu.
Benethya ƙara da cewa wasu ɓata-gari kan aikata laifi a Abuja, sannan su tsere zuwa wasu jihohi, abin da ke janyo wahala wajen kama su.
Sai dai, ya ce rundunar na shirye wajen tabbatar da ingantaccen tsaro a birnin na Abuja.

Asalin hoton, Getty Images
Manyan kamfanonin waka a Amurka guda uku sun maka wasu kamfanonin kirkirariyar basira ta AI guda biyar a kotu, bisa zarginsu da keta dokokin hakkin mallaka.
Kamfanonin Universal Music Group da Sony Music Entertainment da kuma Warner Records na namen kamfanonin Udio da Suna su biya su diyyar dala 150,000 kan duk wata wakar da suka kwaikwaya.
Sun ce kamfanonin na satar ayyukan mawaka suna amfani da su wurin samun riba.

Asalin hoton, TELEGRAM/SERGEI MELIKOV
Adadin waɗanda suka mutu a hare-haren da aka kai a Jamhuriyar Dagestan da ke kudancin Rasha ya kai mutum ashirin - ciki har da 'yan sanda 15, yayin da mutum ashirin da shida suka jikkata.
Maharan dai sun afka wa coci-coci da kuma wuraren bautan Yahudawa da ke yankunan Makhachkala da Derbent.
Masu bincike sun bayyana cewa an kashe maharan guda biyar.
Tun da farko dai, mai Magana da yawun shugaba Putin, Dmitry Peskov, ya shaida wa manema labarai cewa Mista Putin ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan duk waɗanda suka mutu a harin makami mai linzami da aka kai a Crimea da kuma Dagestan.
Ya ce za a ba da duk wani tallafn da ya dace ga dukkan mutanen da lamuran biyu suka shafa, kuma ma'aikatar kiwon lafiya tana bayar da agaji ga waɗanda suka jikkata.

Asalin hoton, NAHCON
Hukumar aikin Hajji ta 'kasar watau, NAHCON ta mayar da martani kan zargin da gwamnan jihar Neja ya yi mata na rashin shirya ingantaccen aikin Hajji a bana.
Hukumar ta ce gwamnan bai yi mata adalci ba idan aka yi la’akari da faduwar darajar kudin kasar naira da kuma kasancewarta mai sa ido ce ba mai daukar dawainiyar mahajjata ba.
Gwamna Umaru Bago ya yi zarge-zargen a Saudiyya, a wani taron manema labarai.
Mai magana da yawun hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta ce ƙasar Saudiyya ba ta hulɗa da jihohi a kan harkar aikin Hajji, illa ƙasashe kawai.
'Ba zai yiwu a ce jihar Neja ta je Saudiyya don yin yarjejeniya kan alhazanta ba. Idan gwamnan ya ce a ɗauki ayyukan a mayar da su kan jihohi akwai ayar tambaya a kai," in ji Fatima Sanda.
Ta ce " Sa ido ne kawai NAHCON ke yi ba ita take kwashe alhazai zuwa Saudiyya ba. Jiragen sama ne ke da alhakin haka.
Dangane da zargin da gwamnan na Neja ya yi kan yanayin lafiyar mahajjata kuwa, Hajiya Fatima ta ce ba abin da ya haɗa da NAHCON da wannan saboda alhakin ya rataya kan jihohi, inda ta ce haka ne ma yake sa wani lokaci ake samun mata masu ciki da ke tafiya zuwa aikin Hajji.
"Muna sonmu tunatrawa gwamna Bago cewa hukumomin jihohi ne ke zaɓar waɗanda za su ciyar da alhazansu da kuma irin abincin da suke so ba wai hukumar mu ba, don haka idan suka zauna da yunwa ba laifin mu bane," kamar yadda Fatima Usara ta shaida wa BBC.
Ta kuma yi watsi da batun cewa NAHCON ta gaza a ayyukanta na gudanar da aikin Hajji.
Hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Sudan ce ta fi kowace ƙasa yawan ƙananan yara masu gudun hjira a duniya, yayin da ake ci gaba da gwabza yakin basasa a ƙasar.
Shugabar UNICEF, Catherine Russell, ta bayyana cewa kusan dukkan yaran Sudan ba su zuwa makaranta.
Ta ce kimanin miliyan tara ba su samun isasshen abinci akai-akai yayin da miliyan huɗu ke fuskantar matsalar matsananciyar yunwa.
Ɓangarorin biyu da ke faɗa da juna sun takaita ayyukan agaji a ƙasar, lamarin da ya haifar da matsalar yunwa.
Duk da mummunar yanayin jin kai da ake fuskanta , yunkurin Amurka na sake farfaɗo da tattaunawar sulhu ya ci tura.

Asalin hoton, DAULAR USMANIYYA
Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya ce za a iya ɗaukar tsawon shekaru kafin a shawo kan matsalar ‘yan bindiga da ta dabai-baye arewa maso yammacin Najeriya.
Sultan ya faɗi haka ne a taro don inganta yanayin tsaro wanda ake yi a jihar Katsina yau Litinin.
“Abin da ya kamata mu yi shi ne kalubalantar waɗannan ƴan bindiga saboda mun san irin illar ƴan ta-da-ƙayar baya ga rayuwarmu. Sai dai za a shafe tsawon shekaru kafin a magance matsalar gaba-daya,” in ji Sultan Sa’ad.
Ya ce sarakunan gargajiya a shirye suke domin haɗa gwiwa da jami’an tsaro da kuma gwamnoni bakwai na yankin domin ceto shi daga ɗimbin matsaloli da yake fuskanta.
Ya yi imanin cewa a karshen taron, za a samu hanyoyin rage barazanar da ‘yan bindigar ke da shi domin mutane su koma rayuwa ba tare da fargaba ba da kuma gudanar da harkokin kasuwanci.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaba Bola Tinubu, da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnoni bakwai na jihohi da ke arewa maso yamma, shugabannin hafsoshin tsaro da kuma sufeton ‘yan sanda.

Asalin hoton, COAL CITY CONNECT/INSTAGRAM
Al’ummar garin Ogurute Oombe da ke jihar Enugu sun mika sabon asibitin da suka gina ga gumakansu domin samun kariya.
Wannan shawarar dai ta zo ne biyo bayan yawaitar satar kayan aikin asibitin a lokacin da ake gina shi.
A wani faifan bidiyo da BBC Igbo ta samu, wakilin al’ummar Ogurute Oombe ya bayyana takaicin mutanen kauyen tare da bayyana irin asarar da aka yi.
Kayayyakin da aka sace sun hada da motar daukar marasa lafiya da na'urar talabijin da injin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, da sauran muhimman kayayyakin aiki da na’urorin da suka dace don gudanar da ayyukan asibitin.
“Mutanen da suke nan a yau ‘yan asalin garin Ogurute Oombe ne, kuma wannan shi ne babban asibitin Ogurute Oombe da gwamnati ta gina mana,” in ji kakakin.
“Gwamnati ta kawo mana kayayyakin da za mu yi amfani da su wajen kula da marasa lafiya, sun kawo injinan wutar lantarki mai amfani da hasken rana da motar daukar marasa lafiya da na’urar talabijin, da sauran abubuwa masu kyau da za ku iya tunani a kai."
Ya ci gaba da cewa, "Amma yanzu babu wanda ya ga waɗannan kayayyakin aikin cikin kankanin lokaci bayan an kawo su, ba mu ji dadin hakan ba."
Satar da aka yi ba wai kawai ta hana asibitin samun kayan aiki masu mahimmanci ba, har ma da kashe wa al’ummar fatar da suka sa rai da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Dangane da irin wadannan sace-sacen da ake ta yi ne mutanen ƙauyen suka yanke shawarar neman kariya daga gumakansu da suke bautawa.

Asalin hoton, NPFL
A ƙarshe dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enugu Rangers ta jinjina kofin babbar gasar firimiyar Najeriya a karo na takwas bayan doke Gombe United har gida da ci 2-1.
Rangers ta samu jimillar maki 70 a gasar ta Nigeria Professional Footbal League (NPFL) kakar 2023-24, wanda hakan ke nufin ta samu tikitin zuwa gasar zakarun Afirka.
An gudanar da bikin ba ta kofin ne a filin wasa na Jos International Stadium - inda Gome United ke buga wasa - bayan wasan mako na 38.
Rangers ce ta fara cin ƙwallo minti uku da take wasa ta hannun Ogunleye, sannan Obaje ya ƙara minti huɗu bayan haka, kafin Hassan ya farke wa Gombe ƙwallo ɗaya a minti na 25.
Karanta cikakken labarin a nan: Yadda Rangers ta zama gwarzuwar firimiyar Najeriya karo na takwas

Asalin hoton, NPFL

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Tarayyar Turai sun zargi kamfanin Apple da laifin keta sabbin dokokin da aka tsara don sarrafa manyan kamfanonin fasaha.
Hukumar ta ce manhajar Apple na murƙushe kasuwannin abokan hamayya, wanda ke zama karo na farko da ya sami kamfani da ke saɓa dokar Kasuwar Dijital (DMA).
Kamfanin na fuskantar yuwuwar tarar kusan kashi 10 cikin 100 na kuɗaɗen shigar sa na duniya idan ya gaza bin ka'idoji.
An bai wa kamfanin Apple ɗin damar yin nazari kan sakamakon binciken farko da aka samu, kuma zai iya kaucewa cin tarar idan ya dawo da wata shawara wacce ta gamsar da Tarayyar Turai.
Kamfanin yana cajin masu haɗa manhajoji kaso 30 akan manhajarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da damuna ke ƙara kankama a Najeriya, Cibiyar Kare Cutuka masu yaduwa ta ƙasar (NCDC) ta ce akwai yiwuwar cutar kwalara ta ci gaba da yaɗuwa tare da yin illa.
Tuni cutar ta hallaka mutum 30 daga farkon shekarar 2024 zuwa tsakiyar watan Yunin shekara, yayin da aka zargin kimanin mutum 1,141 ne suka kamu a ƙananan hukumomi 96 da ke faɗin ƙasar.
Tuni jihar Legas da ke kudancin ƙasar ta bayyana ɓarkewar cutar a cikinta.