Neymar zai ci gaba da taka leda a Santos

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku dukkan abubuwan dake wakana a fannin wasanni a faɗin duniya daga Asabar 21 zuwa Juma'a 28 ga watan Yunin 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Abdulrazzaq Kumo

  1. Gundogan

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran golan Chelsea ɗan kasar Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 30, zai kammala komawa Arsenal a kan cinikin fam miliyan 5 a wannan makon. (Sky Sports)

    Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao ɗan ƙasar Sifaniya Nico Williams, mai shekara 22, wanda ke da farashin fam miliyan 50 a kwantiraginsa, ya shaidawa ƙungiyar cewa yana da sha'awar komawa Barcelona. (Athletic)

    Burnley na shirin gabatar da tayin fam miliyan 12 kan ɗan wasan Lazio ɗan kasar Faransa Loum Tchaouna, mai shekara 21. (Football Italia)

  2. Chelsea ta sake komawa cinikin Gittens

    Gittens

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta sake tuntuɓar Borussia Dortmund kan a sayar mata da Jamie Gittens.

    Tun farko ƙungiyar dake buga Bundesliga ta yi watsi da tayin da Chelsea ta yi wa matashin mai shekara 20 kan £42m ranar 10 ga watan Yuni.

    Gittens, mai buga wa tawagar Ingila ta matasa ƴan kasa da shekara 21 tamaula, ya yi minti 13 a Club World Cup a Dortmund karkashin koci, Niko Kovac.

    Matashin wanda bai dade da sa hannu kan yarjejeniyar kaka bakwai da Dortmund ba na sha'awar komawa Stamford Bridge da taka leda.

    Bayern Munich ma na son sayen matashin ɗan ƙwallon.

  3. raducanu

    Asalin hoton, Getty Images

    Emma Raducanu ta kai zagaye na biyu a Eastbourne - ta kara fadada damar taka rawar gani a Wimbledon Open.

    Raducanu ta doke Ann Li da cin 6-7 (5-7) 6-3 6-1.

    Raducanu, wadda ta sharɓi kuka bayan nasara a karawar - za ta fuskanci Maya Joint a zagayen gaba, domin tantance, wadda za ta kai kwata fainal.

  4. RB Leipzig ta nada Ole Werner a matakin sabon kociyanta kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar 2027, kamar yadda kungiyar dake buga Bundesliga ta sanar a jiya Talata.

    Hakan ya kawo karshen neman kociyan da zai maye gurbin Marco Rose da ta fara tun daga watan Maris.

    Leipzig ta kare a mataki na bakwai a Bundesligar da ta wuce, kenan ba za ta buga gasar zakarun Turai ba, kuma karon farko tun bayan 2016.

    Werner mai shekara 37, bai amince ya tsawaita kwantiraginsa a Werder Bremen ba, domin ya koma leipzig.

  5. Sancho

    Asalin hoton, Getty Images

    Fenerbahce na zawarcin ɗan wasan gaban Manchester United Jadon Sancho, mai shekara 25, wanda farashinsa ya kai Fam miliyan 25. (Talksport)

    Sunderland ta tuntuɓi Sassuolo game da yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Faransa Armand Lauriente mai shekara 26. (ESPN)

    Everton da Manchester United na zawarcin ɗan wasan Leicester ɗan Najeriya Wilfred Ndidi, mai shekara 28, wanda zai iya barin ƙungiyar a kan farashin fam miliyan 9. (Talksport)

    Har yanzu Leeds ba ta samu tayi kan golan Faransa mai shekara 25 Illan Meslier ba duk da rahotannin da ke cewa yana shirin zuwa gwada lafiyarsa a Fenerbahce. (Sky Sports)

  6. Arsenal za ta kammala sayen Arrizabalaga a makon nan

    Arizabalaga

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal za ta kammala cinikin sayen golan Chelsea, Kepa Arrizabalaga a makon nan.

    Mai shekara 30 yana kunshin kwantiragin £5m, bayan da ya tsawaita sa hannu a yarjejeniyar kaka ɗaya a bara, sannan ya je ya buga wasannin aro a Bournemouth.

    Tsohon mai tsaron ragar tawagar Sifaniya, zai koma Arsenal domin kalubalantar gurbin da David Raya ku bugawa a Gunners.

    Arsenal na bukatar mai tsaron raga, bayan da ba ta amince ta ɗauki Neto ba, wanda ya buga mata wasannin aro daga Bournemouth.

  7. Waɗanda suka kai zagaye na biyu a Club World Cup

    Lionel Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    • Palmeiras da Botafogo (ranar Asabar a Philadelphia)
    • Benfica da Chelsea (ranar Asabar a Charlotte)
    • Paris St-Germain da Inter Miami (ranar Lahadi a Atlanta)
    • Flamengo da Bayern Munich (ranar Lahadi a Miami)
  8. Sakamakon wasannin damben gargajiya a jihar Kano, Najeriya ranar Talata

    Sakamakon damben gargajiya da aka dambata a jiya a gidan wasa dake Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

    • An tashi canjaras tsakanin Guramada Ɗan kasa da Aljanin Ramadan
    • Shi kuwa Sha'aban ya buge Shagon Zy
    • Dogon Dogon Mai Takwasara ya yi nasara a kan Shagon Kosilaye
    • Alasan shagon Bahagon yan sanda ya barar da Dogon Reza Bunza
  9. Al-Nassr ta kori kociyanta, Pioli

    Al-Nassr

    Asalin hoton, Getty Images

    Al-Nassr ta sallami kociyanta, Stefano Pioli kasa da shekara ɗaya da ya karɓi aikin horar da ƙungiyar.

    Ɗan kasar Italiya, ya karbi aikin horar da ƙungiyar da Cristiano Ronaldo da sauran taurarin ƴan wasa a cikin Satumbar 2024.

    Ya maye gurbin Luis Castro, saboda kasa samun sakamakon wasannin da ƙungiyar ke bukata.

    Pioli ya ja ragamar Al-Nassr zuwa mataki na uku a teburin babbar gasar tamaula ta Saudiiya da tazarar maki 13 tsakani da Al-Ittihad, wadda ta lashe kofin kakar da ta wuce.

  10. Wasannin Fifa Club World Cup

    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    FIFA Club World Cup rukuni na huɗu

    • Esperance de Tunis da Chelsea a filin wasa na Lincoln Financial
    • Los Angeles FC da Flamengo a filin wasa na Camping World

    FIFA Club World Cup rukuni na shida

    • Borussia Dortmund da Ulsan HD a filin wasa na TQL
    • Mamelodi Sundowns da Fluminense a filin wasa na Hard Rock
  11. An kara dakatar da Jackson wasa biyu, saboda jan kati a Club World Cup

    Jackson

    Asalin hoton, Getty Images

    An kara dakatar da ɗan ƙwallon Chelsea, Nicolas Jackson wasa biyu, sakamkon jan katin da aka yi masa a karawar da Flamengo ta doke su 3-1 a fafatawa ta biyu a cikin rukuni a Club World Cup.

    An bai wa Jackson jan kati a minti na huɗu da shigarsa karawar a zagaye na biyu, bayan ketar da ya yi wa Lucas Ayrton.

    Nan da nan aka yi masa hukuncin dakatarwa wasa daya da Chelsea za ta yi da ES Tunis.

    Sai dai kwamitin ladabtarwa na Fifa ya sake bibiyar ketar da Jackson ya yi, ya yanke hukuncin cewar da mugun nufi ya yi, saboda haka aka kara dakatar da shi wasa biyu.

    Kenan ba zai buga wasa biyu ba da zarar ta kai zagayen kungiya 16 da za ta ci gaba da karawar.

  12. Watakila Garnacho ya bar Man United

    Garnacho

    Asalin hoton, Getty Images

    Watakila Alejandro Garnacho ya bar Manchester Untied zuwa wata kungiyar kafin a fara kakar da za mu shiga.

  13. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan gaban Paris St-Germain ɗan ƙasar Faransa Bradley Barcola, mai shekara 22, wanda Bayern Munich da Liverpool ke nema. (L'Equipe)

    Tottenham za ta nemi ɗaukar ɗan wasan Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 26, bayan da ta yi rashin nasara a zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo sakamakon tayin sama da fam miliyan 60 da Manchester United ta gabatar a kan ɗan wasan mai shekara 25. (Talksport)

    Ɗan wasan bayan Liverpool ɗan ƙasar Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa, ya ki amincewa da sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta gabatar. (Guardian)

    Newcastle na tattaunawa da Burnley kan cinikin golan Ingila James Trafford mai shekara 22. (Fabrizio Romano)

  14. Tawagar mata ta Sifaniya ta fara atisaye domin Euro 2025

    Spain

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar kwallon kafa ta mata ta Sifaniya mai rike da kofin duniya, ta fara shirye-shiryen shiga gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan kammala hutun da ta yi.

    Ta fara atisaye ranar Talata tare da yan wasa 23 da suka amsa goron gayyata, domin buga Euro 2025.

    Kasar Switzerland ce za ta karbi bakuncin wasannin bana da za ta gudanar a filaye takwas tun daga ranar 2 ga watan gobe.

    Ingila ce ke rike da kofin nahiyar Turai a gasar mata da ta lashe a 2022, bayan doke Jamus a wasan karshe a Wembley.

    Tawagar Sifaniya za ta buga wasan sada zumunta nan da kwana huɗu masu zuwa da Japan daga nan ta ziyarci Switzerland, inda za ta kara a cikin rukuni mai zafi da ya hada da Belgium da Italy da kuma Portugal.

  15. Chelsea za ta yi wasa mai mahimmaci a Club World Cup

    Enzo Maresca

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea za ta buga wasa mai mahimmaci a FIFA Club World Cup, inda za ta fafata da kungiyar Tunisian, ES Tunis a wasan karshe a cikin rukuni da za su fafata a Philadelphia.

    Chelsea na bukatar maki daya domin ta kai zagaye na biyu a wasannin da ake a Amurka.

    Kyaftin din Chelsea, Reece James ba shi da lafiya da kyar idan zai buga karawar, yayin da Nicolas Jackson ke hutun dakatarwa. saboda jan katin da aka yi masa.

  16. An kara dakatar da Rico Lewis wasa biyu, saboda jan kati a Club World Cup

    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    An kara hukuncin dakatar da mai tsaron bayan Manchester City, Rico Lewis wasa biyu, sakamakon jan katin da aka yi masa a Club World Cup a wasan Wydad Casablanca.

    City ta daukaka kara, amma ba ta yi nasara ba, kenan ba zai buga wasan da za ta yi da Juventus ranar Alhamis ba a karawar karshe ta cikin rukuni na bakwai da wasa daya a zagayen yan 16.

  17. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Juventus ta shirya miƙa dan wasan gaban Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 25, da kuma ɗan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 27, a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan Ingila Jadon Sancho mai shekara 25 daga Manchester United. (Gazzetta dello Sport)

    Barcelona na daf da kammala cinikin ɗaukar matashin ɗan wasan gaban FC Copenhagen ɗan ƙasar Sweden Roony Bardghji, mai shekara 19 a kan farashin fam miliyan biyu. (Sky Sports)

    Har yanzu Monaco ba ta cimma yarjejeniya da tsohon ɗan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 32 ba, duk da rahotannin da wasu ke yaɗawa cewa an cimma matsaya. (Sky Sports)

  18. Brentford tana neman kociyan da zai maye gurbin Thomas Frank

    Andrew

    Asalin hoton, Getty Images

    Keith Andrews yana sawun gaba da za a damkawa aikin kociyan Brentford.

    Har yanzu kungiyar na neman wanda zai maye gurbin Thomas Frank, wanda ya karbi aikin horar da Tottenham.

    Andrew ya koma Brentford a bara, yayi aikin matamiki a Sheffield United da MK Dons da Jamhuriyar Ireland.

    Sauran dake takarar aikin kociyan Brentford har da Kieran McKenna na Ipswich da tsohon kociyan Ajax, Francesco Farioli.

    Tottenham ta maye gurbin Ange Postecoglu, bayan da ta kasa taka rawar gani a gasar Premier League da wuce, amma ta lashe Europa League

  19. Waɗanne ƴan wasa Man United za ta rasa a lokacin Afcon?

    Onana

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United za ta rasa ƴan wasa uku da za su je buga gasar cin kofin Afirka, Afcon idan Bryan Mbeumo ya koma Old Trafford da taka leda za su zama huɗu kenan.

    Ana sa ran fara Afcon daga 21 ga watan Disamba, sannan a karkare 18 ga watan Janairun 2026.

    Kawo yanzu Andre Onana zai wakilci Kamaru da mai tsare baya, Noussair Mazraoui daga Morocco da kuma Amad Diallo na Ivory Coast.

    Ga jerin wasannin Premier League da ba za su buga ba:

    20ga watan Disamba

    Aston Villa wasan waje

    27 ga watan Disamba

    Newcastle United wasan gida

    30 ga watan Disamba

    Wolves wasan gida

    3 ga watan Janairu

    Leeds wasan waje

    7 ga watan Janairu

    Burnley wasan waje

    17 ga watan Janairu

    Man City wasan gida

  20. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan baya na ƙasar Hungary Milos Kerkez, mai shekara 21, zai kammala gwajin lafiyarsa ranar Talata kafin ya koma Liverpool daga Bournemouth. (Athletic)

    Real Madrid za ta buƙaci sama da fam miliyan 77 kan ɗan wasan Brazil Rodrygo, mai shekara 24, wanda ake alakanta shi da komawa gasar Premier League ta Ingila. (Cadena Ser)

    Nottingham Forest ta cimma yarjejeniya ta kusan fam miliyan 19 da Juventus kan ɗan wasan gaban Amurka Timothy Weah mai shekara 25 da kuma ɗan ƙasar Belgium Samuel Mbangula, mai shekara 21. (ESPN)

    Hamshaƙin ɗan kasuwan nan John Textor, wanda yanzu haka ya sayar da hannun jarinsa na kashi 43% a Crystal Palace kan kuɗi fam miliyan 190, yana tunanin siyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sheffield Wednesday. (The Star)