Shin Ronaldo ya buga wa Portugal wasan ƙarshe?

Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya fice daga filin wasa cike da takaicin rashin nasara da Portugal ta yi a hannun Faransa a bugun fenareti bayan da ƙasashen biyu suka tashi babu ci a gasar Euro 2024 da ake bugawa a Jamus.
Masu bibiyar ƙwallon ƙafa da dama na ganin wataƙila wasan ya zama na ƙarshe da Ronaldo, mai shekara 39 ya buga wa ƙasar tasa.
To sai dai kocin Portugal Roberto Martinez ya ce ''har yanzu Ronaldo bai yanke hukunci ko zai ci gaba da taka wa ƙasar leda ko akasin haka ba.
Tsohon tauraron na Real Madrid da Manchester United ya buga duka wasanni biyar da Portugal ta yi a gasar ta bana.
A wasan zagayen 'yan 16 ne Ronaldo ya sharɓi kuka bayan da ya kasa cin bugun fenareti da ƙasarsa ta samu a ƙarin lokaci a wasansu da Sloveniya, kodayake daga baya Portugal ta yi nasara a bugun fenareti.
Wannan ne ya sa magoya bayan ƙwallon ƙafa ke yi masa kallon mutum mai kishin ƙasarsa a fannin tamaula.
Baya ga Ronaldo akwai Pepe - wanda ya kafa tarihin zama mutum mafi yawan shekaru, 41 - da ya buga gasar Euro.
'Yan wasan biyu - waɗanda suka taka leda tare a Real Madrid - sun rungume juna bayan tashi daga wasan, yayin da Pepe ke sharɓar kuka Ronaldo na rarrashinsa.


